Connect with us

KASUWANCI

Jami’an Kwastan Sun Kwace Tabar Wiwi Ta Naira Milyan 74

Published

on


Jami’an hukumar Kwastam shiyyar Legas, sun kwace buhuna 98 da kuma kunshi 570 na tabar Wiwi wacce ta kai mikidarin Naira milyan 74 a ranar Laraba.

Hukumar ta Kwastam ta ce, an shigo da tsinanniyar tabar ta Wiwi ce daga kasashen Togo da Ghana, ta kuma ce ta kama wanda ake tsammanin shi ne ya shigo da tabar.

“Mun kama direban babbar motar da ta dauko tabar, amma an ba shi beli na musamman,” in ji Kwanturolan shiyyar, Uba Mohammed.

Hukumar ta Kwastam ta ce, tuni har ta hannanta muguwar tabar ga hukumar hana sha da fataucin muggan kwayoyi ta, NDLEA,  domin daukan mataki na gaba.

“Wannan taba ce mai hadari, wacce ba ta dace da kowa ba, don haka a madadin hukumar Kwastam, ga shi na hannanta maku wannan tabar domin ku kwace ta ku kuma hukunta wadanda suke da hannu kan shigo da ita,” in ji Uba.

Da yake amsar tabar a madadin hukumar ta, NDLEA, wani Jami’in hukumar na shiyyar Legas, Lawal Opeloyeru, ya nu na hukumar na su a shirye take da ta hada hannu da hukumar ta Kwastam.

“Mun yi magana da ‘yan’uwanmu da ke Ghana, da su tabbatar sun hana aikata wannan mummunan aikin, amma ba abin da suka yi kan hakan, amma dai muna sa ran cin nasara kan hakan, domin mun yi magana da ‘yan sandan kasa da kasa kan matsalar.

“Da zaran mun sami izinin Kotu, za mu lalata kwayoyin a bainar jama’a a nan Legas,” in ji Mista Opeloyeru.

Hukumar ta Kwastam ta ce, ta kwace manyan motoci 10 na buhunan shinkafa masu nauyin kilogram 50, da kudinsu ya kai Naira milyan 74 a tsakankanin ranar 1 zuwa 10 ga watan Afrilu.

Sauran kayayyakin da hukumar ta kwace sun hada da motoci kala daban-daban, dilolin kayan gwanjo masu yawa, daskararrun yankakkun kaji masu yawa, da kuma man girki da aka kiyasta a kan Naira bilyan 1.4.

 


Advertisement
Click to comment

labarai