Connect with us

KIWON LAFIYA

Gwamnatin Kaduna Ta Gyara Cibiyoyin Kiwon Lafiya Matakin Farko

Published

on


Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da cewar ta gyara da kuma daukaka martabar cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko guda saba’in da bakwai daga cikin dari biyu da hamsin da biyar dake daukacin jihar a cikin shekara uku da suka shige.

Bayanin hakan yana kunshe ne a cikin kundin dake dauke da nasarori da inda aka samu nakasu da kungiyar sanya ido akan kiwon lafiyar jihar (KADMAN) ta tattara ta kuma gabatarwa da kwamishinan kiwon lafiya na jihar Paul Dogo a lokacin bude zagaye na farkon shekara na kwana daya da maaikatar ta kiwon lafiya ta shirya a Kaduna.

A cewar kudin, daga cikin cibiyoyin kiwon lafiyar guda dari biyu da hamsin da biyar da gwamnatin ta yi niyyar gyarawa da kuma daukaka matsayin su, guda saba’in da biyar ne kacal ta samu damar gyaran su.

Kundin ya nuna cewar gyara da kuma daukaka martabar cibiyoyin kiwon lafiya guda 86 suna a yankin arewacin jihar ne, inda guda talatin da uku ne kawai aka kammala su daga cikin  tamanin da shida.

An kuma bayar da kwangilar gyaran cibiyoyin na kiwon lafiya na matakin farko dake karamar hukumar Kudan, amma guda biyar kawai aka kammala sai kuma a karamar hukumar Kubau, inda aka bayar da kwangilar gyaran cibiyoyin kiwon lafiya guda sha daya, amma biyar kawai aka kammala.

A karamar hukumar Zaria kuwa an bayar da kwangilar gyaran cibiyoyin kiwon lafiya guda sha uku amma shida kawai aka kammala, sai kuma karamar hukumar Lere inda aka bayar da kwangilar gyaran cibiyoyin kiwon lafiya guda sha daya, amma biyu kawai aka kammala.

Har ila yau, a karamar hukumar Sabon Gari,an kammala kwangilar guda uku daga cikin cikin goma, inda a karamar hukumar Birnin Gwari aka kammla kwangilar guda uku daga cikin sha daya.

Bugu da kari kundin ya nuna cewar, kwangila gyara cibiyoyin kiwon lafiya guda tamanin da daya da aka bayar a shiyyar Kaduna ta tsakiya, guda ashirin da hudu ne kawai aka kammala.

Kundin yaci gaba da cewa, a yankin kudancin Kaduna an bayar da kwangilar gyaran cibiyoyin kiwon lafiya ashirin aka bayar, inda kuma a karamar hukumar  Kaura aka bayar da kwangilar guda goma, amma ko daya ba’ a yi ba haka a karamar hukumar Zangon Kataf an bayar da kwangilar gyaran cibiyoyin kiwon lafiya guda sha daya, amma ba’a kammala ko daya ba.

A jawabin sa a wurin taron, kwamishinan kiwon lafiyar jihar Dakta Paul Dogo, musamman akan rashin aiwatar da kwangilar ta Kaura da Zangon Kataf ya danganta hakan akan sakacin ‘yan kwangilar da aka baiwa aikin.

Acewar sa, “ nida kai na naje wurin na duba, inda naga ‘yan kwangilar sun yi watsi da aikin kuma gwamnati ta damu kwarai akan hakan”.

Dakta Paul ya bayar da tabbacin cewar, nan bada jimawa ba za a ci gaba da sauran ayyukan da ba’a kmalla su ba.

Da aka tambaye shi akan karacin ma’aikatan kiwon lafiya a jihar Kwamishinan ya tabbatar da hakan, ida yace gwamnatin zata dauki sababbin ma’aikatan kiwon lafiya na musamman da za a tura su kanana asibiti dake jihar don magance hakan .


Advertisement
Click to comment

labarai