Connect with us

SIYASA

El-Rufai Gwamna Ne Da Ya Cancanci Yabo -Hauwa El-Yakub

Published

on


Tun da aka zabi Malam Nasir El-Rufa’I a matsayin gwamnan jihar Kaduna a shekara ta 2015, al’uuma, musamman wadanda ba makomar jihar Kaduna ne a gabansu ba suke sukan gwamnan cewar, babu wani aiki da zai aiwatar a fadin jihar, sai fa rushe-rushe da sauran abubuwa da za su durkusar da al’ummar jihar Kaduna.

HAUWA HASSAN EL-YAKUB, babbar jami’a ce ta gudanar da ayyukan siyasa na gwamna Nasir El-Rufa’I a shiyya ta daya a jihar Kaduna, ta ce dukkanin abubuwanda ake fadi kan gwamna Malam Nasir El-Rufa’I, duk batutuwa ne da a yau za a ce ba su tabbata ba, sai dai batutuwan ci.

gaba mai girma gwamnan jihar Kaduna ya sa wa gaba a daukacin kananan hukumomi jihar Kaduna 23. Ga yadda tattaunawrar da wakilinmu BALARABE ABDULLAHI ya yi da ita a Zariya:

Me za ki ce kan ayyukan hanyoyi da aka ce wai gwamnatin jihar Kaduna na aiwatarwa a fadin jihar?

Ai ayyukan da mai girma gwamnan jihar Kaduna ke yi a sassan jihar Kaduna, ya wuce a ce wai, sai dai a yi bayanin tabbas, domin ayyukan da ake yi musamman ayyukan hanyoyi a bayyane suke, kowa na gani.

Da farko duk wanda ya san garin Kaduna, kafin malam Nasir ya zama gwamna, ya san akwai matsala a farkon shiga garin Kaduna, wato Kawo. Domin aiki na farko kenan da mai girma gwamna ya yi kenan na fadada hanyar kawo zuwa shatale-talen Lugad hol, duk wanda ya san

wannan hanya, kamar yadda na ce a shekarun baya, dole ya ce a yau al’ummar jihar Kaduna sun sami gwamna da ya damu da matsalolinsu, kuma har ila yau za mu iya cewar, Malam Nasir El-Rufa’I, gwamna ne da ya cancanci a yaba ma san a ayyukan da aiwatar daga lokacin da ya zama gwamnan jihar Kaduna zuwa yau.Kuma duk dan jihar Kaduna, in zai fadi gaskiya, abubuwan da ba a samu ba a shekarun baya, kamar yin sabbin hanyoyi da gyaran wasu hanyoyin da inganta samar da rowan shad a kuma bin hanyoyin da suka dace, domin bunkasa noma a daukacin jihar Kaduna, duk wannan an yi su, ba za a yi ba ne.

Wasu ayyuka za ki ba mu misali da su da gwamnatin jihar Kaduna ta aiwatar a shekara uku da suka gabata?

A baya na ba ku misali da babbar hanyar da ta tashi daga Kawo zuwa cikin garin Kaduna, sai hanyar da ta tashi daga Kasuwar birnin Zariya ta zarce Kaura zuwa Fadamar Sarki zuwa Kofar Galadima, sai hanyar da ta tashi daga Kofar doka zuwa Kwarbai zuwa Unguwar Katuka ta zarce ta unguwar Magajiya zuwa Kofar galadima, sai kuma hanyar Kwamngila zuwa Pz , a karamar hukumar Sabon garin zariya. Wadannan wasu daga cikin hanyoyin da gwamnatin jihar Kaduna ne ta aiwatar da ayyuansu a shiyya ta daya, akwai ire-irensu a shiyya ta biyu da kuma shiyya ta uku.

In ka lura al’ummar jihar Kaduna sun dade da sanin suna yin zabe a fallen gwamnati uku, amma ba su amfana da zaben da suke yi sai a halin yanzu, da suke ganin ayyuka a bangarori da dama, kamar yadda na bayyana ma ka a baya.

Kin taba zagawa kin ga yadda ayyukan suke gudana?

Babu ko shakka ta za gas au da dama, tun da yanzu ayyukan hanyoyin da na bayyana ma ka, kamar wadda ta tashi daga Kasuwar Birnin zariya zuwa kofar Galadima, yin ingantattun kwalbatoci a ke yi da kuma gadoji, sai wadda ta tashi daga Kofar doka zuwa kofar Galadima, makonni kadan aka biya diyya ga ma su gidajen da hanyoyin za su bi ta gidajensu, duk nan

da dan lokaci, gwamnatin jihar Kaduna za ta kammala ayyukan da na ambata ma ka su.

Me za ki ce na yadda al’umma ke ba gwamnatin jihar Kaduna goyon baya da kuma hadin kai, musamman na ayyukan hanyoyi da gwamnati ta sa wa gaba?

A gaskiya, dole a yaba wa al’ummar da hanyoyin nan za su bi ta gidajensu, domin sun ba gwamnati duk goyon bayan da suka kamata, kuma sun yi haka ne, domin sun fahimci gwamna Malam Nasiru ba irin sauran gwamnoni ba ne, da zarar ya furta zai yi, da gaske ya ke yi, shi ya sa kowa ya bayar da goyon bayansa na ganin an yi wadannan hanyoyi kamar yadda mai girma gwamna ya lashi takobin yinsu.

A bangaren kiwon lafiya, wasu ayyuka gwamnatin jihar Kaduna ta yi?

Ai a wanan bangare babu abin da al’ummar jihar Kaduna za su ce gwamna da kuma gwamnai sai dai godiya, ka dubi gyaran asibitin Gyallesu a karamar hukumar Zariya da sauran wurare ma su yawan gaske da gwamnati na yi sabbin asibitoci ta kuma gyara wasu, ba mu da mu ke cikin gwamnati ba, al’ummar jihar Kaduna a kafafen watsa labarai suna yawan bayyana murnarsuga hyaran asibitoci da ake yi ma su.

A bangaren ilimi kuwa, ka je Firamare ta Rigasa a karamar hukumar Igabi da Tudun jukun da Sani Adamu da kuma Firamare ta Unguwar Kahu a birnin zariya, duk wanda ya yi tozali da ayyukan da ake yi a makarantun da na ambata, ya san da gaske mai girma gwamna ke yi, na ciyar da ilimi gaba.

Me za ki ce kan ayyukan samar da ruwa a Zariya da gwamnatin jihar Kaduna ke yi a halin yanzu?

A gaskiya, wannan shi ne babban aikin da gwamnatin jihar Kaduna ke yi a karamar hukumar zariya, wanda kuma in an kammala, wasu kananan hukumomi da suke makotaka da zariya za su amfana da ruwan da za a samar. Musamman in ka dubi bangaren Wusasa, da suke fama da rashin ruwa fiye da shekara ashirin da kuma al’ummar Unguwar Bishar a birnin zariya, yaro dan shekara 25 bai san yadda ruwa ke zuwa a famfo ba, a gaskiya dole a yaba wa mai girma gwamna da ya lashi takobin ganin sai ya kawo karshen matsalar ruwa ta zariya.

A karshe akwai sakon da ki ke da shi ga al’ummar jihar Kaduna, na yadda zaben kananan hukumomin jihar Kaduna ya kusanto, ga kuma na shekara ta 2019 na gab da bayyana?

Sakon da na ke da shi ga al’ummar jihar Kaduna shi ne, su zabi Malam Nasir El-Rufa’I, domin ayyukan da ya ke ya ci gaba yin irinsu ko ma fiye da su, bayan shekara ta 2019, domin shi babban abin da ke zuciyarsa kenan ganin al’ummar jihar Kaduna, sun amfana da zaben da suke yi, ba su zama ma su yin zabe, amma ba su ganin amfanin zaben da suke yi, kamar yadda zabubbukan baya suka kasance.

 


Advertisement
Click to comment

labarai