Connect with us

WASANNI

Dama Ina Son Fuskantar Arsene Wenger -SIMEONE

Published

on


Mai koyar da yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid, Diego Simeone, dan kasar Argentina  ya bayyana cewa ya dade yana fatan ganin ya fuskanci mai koyarwa Arsene Wenger domin gwada basirarsa akan sa a kowacce irin gasa.

Someone ya bayyana hakane a wata hira da yayi da gidan talabijin dake kasar sipaniya inda yace Wenger babban mai koyarwa ne wanda ya dade yana koyarwa kuma yana da basira da hangen nesa da kuma iya koyar da kwallo.

Yaci gaba da cewa yayi farin ciki da aka hada Arsenal da kungiyarsa a gasar Europa domin yasamu damar buga wasa da mai koyarwa kamar Wenger wanda ya dade yana koyarwa kuma ya koyar da manyan manyan shahararrun yan kwallo a duniya.

Ya kara da cewa Wenger yasamu gagarumar nasara a Arsenal tun daga lokacin daya fara aikin koyar da kungiyar saboda haka babu wani mai koyarwa da bazai jinjinawa Mista Wenger ba idan aka duba irin bajintar dayayi a baya.

Arsenal da Atletico Madrid dai zasu kece raini a gasar Europa a matakin kusa dana karshe a karshen wannan watan inda za’a fara buga wasan farko a filin wasa na Fly Emirates kafin daga baya kuma aje kasar Sipaniya domin buga wasa na biyu.

 


Advertisement
Click to comment

labarai