Connect with us

TATTAUNAWA

Da Mu Aka Yi Zaben 2015 Amma Ba A Ba Mu Ko Da Kuturun Bawa Ba –Sani Dan Gama

Published

on


Tun daga lokacin da aka gabatar da zaben shekara ta 2015, daidaikun al’umma da kuma wasu kungiyoyi da aka kafa su domin rufa wa wadanda suka shiga takarar baya a lokutan yakin neman amincewar al’umma su zabi ‘yan takarar jam’iyyar ‘APC’ tun daga kasa ya zuwa sama,bayan an kammala zaben mafiya yawan wadanda suka bayar da gudunmuwar a matakan jihar Kaduna da kuma tarayyar Nijeriya na ci gaba da yin kukan an ajiye su a gefe guda, kuma ko da rana daya ba a taba kirarsu a ce ma su, an gode kan gudummuwar da suka bayar ba.

ALHAJI SANI DANGAMA, shi ne shugaban kungiyar tallafa wa Buhari da el-Rufa’i, wato ‘Buhari-El-Rufa’i Special Campaign Organization’ wadda aka kira ‘BESCO’ a takaice, ya bayyana wa wakilinmu da ke Zariya BALARABE ABDULLAHI irin hawa da kuma gangarar da suka yi kafin zaben shekara ta 2015, wanda suka tuntubi kungiyoyi kafin zaben da aka ambata, amma tun da aka kammala zaben ba a cika alkawarin tallafa wa kungiyoyin da suka bayar da goyon bayansu ba a karkashin wannan kungiya ta ‘BESCO’. Ga dai yadda tattanawarsu da wakilinmu ta kasance:

Zan so ka bayyana wa mai karatu cikakken sunanka

Suna na Sani Dangama

 

Mene ne sunan wannan kungiya ta ku?

Sunan wannan kungiya shi ne Kungiyar tallafa wa Buhari da kuma El-Rufa’I a ga sun sami nasara a zaben shekara ta 2015, kuma ni ne shugaban wannan kungiya a halin yanzu, domin lokacin da mu ka kafa kungiyar, wato kafin zaben 2015, Malam Muhammad Tukur ne shugabanta,amma Allah ya yi masa rasuwa, shi ne na zama shugabanta a halin yanzu, kamar yadda na bayyana ma ka.

 

Me ku ka mayar da hankali a karkashin wannan kungiya kafin zaben shekara ta 2015?

Babban abin da mu ka saw a gaba shi ne neman kungiyoyin al’umma tare da hada kansu, su zabi Buhari da kuma El-Rufai’I ako wace kunduma na karamar hukumar Zariya, mun zauna da kungiyoyi da yawan gaske, mu ka bayyana ma su bukatarmu, tare da alkawarin in an sami nasarar cin zabe za a tallafa wa wadannan kungiyoyi, tare da tafiya tare da su a al’amura da dama.

 

To bayan samun nasarar zabe, me ya faru?

Ai tun da aka sami nasarar cin zaben, daga shugaban kasa Buhari zuwa Gwamna El-Rufa’I, babu wanda ya kira mu ko kuma aka turo ma na sakon godiya na gudunmuwae da mu ka bayar har zuwa wannan rana da mu ke tattauna da kai.

 

To daga lokacin da ku ka kammala bayar da gudunmuwar har aka sami nasarar zaben zuwa yau, ya alakarku da kungiyoyin da ku ka yi ma su alkawari?

Lallai a watannin da suka gabata, da mu ka ga an yi shekara uku ba a ce ma na komi ba, sai mu ka ko ma ga wadannan kungiyoyi, inda mu ka ba su hakuri na rashin ba su wani tallafi day a dace, kamar yadda mu ka ce ma su cewar in an ci zabe za a tallafa ma su.

Yanzu kuma da mu ka ga batun zaben kananan hukumomi ya taso a jihar Kaduna, shi ne mu ka sake komawa ga wadannan kungiyoyi, mu ka sake ba su hakuri, tare da nuna bukatar su zabi ‘yan takar jam’iyyar APC,a daukacin kananan hukumomin jihar Kaduna 23,in lokacin zaben ya yi.

Kuma mu na ci gaba da tunatar da wadanda ba su da kuri’ar zabe, lallai su mallaka, domin zaben APC kamar yadda na bayyana ma ka a bayan nan yanzu.Mun kuma dauki matakai da yawan gaske na duk wanda ba shi da katin zaben zai samu kamar yadda doka ta tsara.

 

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’I, ya san kun yi wannan aiki na tallafa ma su kafin  da kuma bayan zaben shekara ta 2015?

Lallai gwamnan jihar Kaduna ya an wannan aiki da mu ka yi, domin mun dauki kundin ayyukan da mu ka yi, wato na bayanan zagayen da mu ka yi, da na murya da kuma na hoto, mun kai ma sa hannu da hannu, wanda a wancan lokaci ne ya yi ma na alkawarin gwamnatinsa za ta tallafa wa wadannan kungiyoyi da suka bayar da gudunmuwa a lokutan zaben 2015.

 

Kun tuntubi mai ba gwamna shawara kan siyasa kan wannan aiki da ku ka yi zuwa yanzu?

Lallai ba mu tuntube shi ba, domin shi dai ya san abin da mu ka yi, kuma duk wani na kusa da gwamna ya san gudunmuwar da mu ka baya, sai mu ka bai kamata mu je wajen wanda ka bayyana ba.Kuma duk zagayen da mu ke yi, yaransu a gundumomi suna bayyana ma su dalla-dalla.

 

Tamkar an juya ma ku baya ken an, amma ga shi ku kun a kokarin shiga wajensu, an ce matar shige, bat a mutunci ga mijinta, haka ne?

To, mu duk abin da mu ke yi, mu na yi ne, domin a sami canji, an kuma samu, duk abin da zai biyo baya, mu jam’iyyar mu ke dubawa da kuma alkawurran da aka yi wa kungiyoyin da suka bayar da gudunmuwar da na bayyana ma ka.Kuma domin wani abu na cika alkawari bai zo garemu ba, na ce ma ka jam’iyyarmu ta APC mu ke kallo a duk motsin da mu ka yi.

 

Yanzu dai za a iya cewar, gwamnatin tarayya da kuma gwamnatin jihar Kaduna duk sun yi shakuletin-bangaro da ku tare da ayyukan da ku ka yi ma su, an ya za ku ci gaba da yin aiki a karkashin wannan kungiya kuwa ya zuwa zaben shekara ta 2019?

Ba zan canza batun da na bayyana ma ka ba,lallai duk abin da mu ke yi, mu na yi ne domin ci gaban jam’iyyar APC, mu na nan a kan wannan hanya da yaddar mai kowa mai komi.

 

Kamar ba a duba gudunmuwar da ku ka bayar ba, za ku ci gaba da ayyukan ken an a yana yin kun a aiki, ba sannu, ballanta na gode?

Mu fa abin da mu ka dauka lokacin dubawar ne bai yi ba, in lokacin dubawar ya yi za a duba kamar yadda aka yi alkawari a lokacin da n ace ma ka mun ba gwamna bayanin ayyukan da mu ka yi hannu da hannu.

 

Ka na ganin kungiyoyin za su yadda su kara rungumar ku kamar yadda suka rungume ku a baya?

Abin da mu ke bayyana ma su, su daina cewar wani abu bai je garesu ba, amma gwamnati ta sami nasarorin day a shafe su kai tsaye, kamar tsawo da dai sauransu da sauran tallafi da gwamnatoci ke yi da ya shafi noma da ilimi da kiwon lafiya duk nasarori ne da suka kamata a duba su, saboda haka, ba mu da wata matsala da wata kungiya baki daya. Mu ci gaban jam’iyyar APC mu ka sa wa gaba ba wasu abubuwa na daban ba.


Advertisement
Click to comment

labarai