Connect with us

KIMIYYA

Babbar Ariyar Rediyo Da Talbijan Na Da Matukar Illa

Published

on


Hukumar da ke kula da kafofin sadarwar ta Nijeriya (National Communication Commission) ce ta fadi haka, a yayin da take nazarin wani rahoton bincike akan ariyoyin kamfanonin waya da na gidajen rediyo da talbijan,  akwai wani tariri mai karfi da ariyoyin suke fitar wa.

rahoton ya kunshi bayyana na masana akan illolin wannan taririn ga ‘yan adam, don haka hukumar tace dole ta zauna ta yi nazarin wannan rahoton domin gano hanyoyin da za’a bi wajen magance wannan matsalar kafin ta zama matsalar da ba za ta magantu baa nan gaba.

NCC a shafin ta na intanet ta ce, ‘Gidajen talbijan da rediyo masu zaman kansu sune a sahun gaba wajen fitar da wannan tiririn, sannan tiririn da suke fitar wa yana da matukar yawa sosai, Allah ma ya sa na’urar da ta ke fitar da taririn ta na can kololuwar ariyar ne da Allah kadai ya san irin illar da za ta yi wa al’umma, duk da haka mutane sun fi shakar tiririn ariyar gidajen rediyo da talbijan fiye da yadda suke shakar na kamfanonin wayar hannu amma dai duk karfin tiririn daya ne sai dai yawan su ne ya bambamta.’

Wasu masu bincike ‘yan kasar Astireliya sunce suna zargin wannan tiririn shi ne ke haifar da cutar sankarar jini ga yara masu kananan shekaru, duk da wasu masanan ‘yan kasar Ingila suna shakkar hakan, a na su binciken sun ce lallai tiririn bas hi da wata alaka da cutar sankarar jini ga kananan yara duk da sun san ya na da muguwar illa.

Dadewa ana shakar wannan tiririn shine babban abun da ake jin tsoro, saboda tabbas in aka dade ana shakar taririn to zai haifar da matsaloli na lafiya masu wuyar sha’ani, don haka dole a nemu hanya mai sauki da za’a yi maganin wannan matsala ta tiriri.

Sun kara da cewa, ‘Duk bincike ya tabbatar da cewa waoyin hannu suna da matsaloli sosai, amma ba matsalar tiriri bace babba daga cikin matsalolin, tafiya a mota ana waya ya ma fi taririn hatsari, domin ya na afkar da munanan hadura, ana ganin ya nunka na wanda shan giya ya ke haifar wa, wato wanda tuki cikin maye yake haifar wa.

 


Advertisement
Click to comment

labarai