Connect with us

LABARAI

Ba Za Mu Yi Zaben Shugabannin APC A Adamawa Ba –Bindow

Published

on


Gwamnan jihar Adamawa Umaru Bindow Jibrilla, ya ce babu batun wani zaben sabbin shugabannin jam’iyyar APC a jihar, domin kuwa shi ya amince shugabannin jam’iyyar da su ci gaba “babu wani zabe kuma a Adamawa”.

Gwamnan ya bayyana haka ne lokacin da shugabannin jam’iyyar daga matakin jiha zuwa kananan hukumomin jihar suka kai mishi ziyara a gidan gwamnatin jihar.

Ya ce amincewa ci gaban shugabancin shugabannin ya biyo bayan tsayawa da hakorin da sukayi ne da kuma biyayya ga shugabancin gwamnatin APC a jihar.

Wannan dai na zuwa mako biyu bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bada shawara ga taron kwamitin zartaswar jam’iyyar na kasa (NEC) cewa kamata ya yi jam’iyyar ta gudanar da zaben sabbin shugabanni a kasar baki daya, mai makon karin wa’adin shekara guda.

To sai dai gwamna Bindow, ya ce su a jihar zasu maye gurbin shugannin da suka mutu ne kawai, ya ce daukacin shugabannin dole su ci gaba.

Ya kara da cewa yana goyon bayan karin wa’adi ga shugabannin jam’iyyar da’akayi tunda farko ya ce hakan zai taimaka wajan kaucema rigingimun jam’iyya, kuma an yiwa kowa adalci lamarin da ba zaisa wasu su kwace jam’iyyar ba.

“Dole na godewa shugabannin jam’iyyar APC daga mazabu zuwa matakin jiha, saboda irin goyon bayan da kuke nunawa gwamnatina, akan haka na amince daku ku ci gaba da shugabanci na wasu shekaru hudu.

“Haka kuma ina neman da wadanda suka mutu kawai za’a maye gurbinsu duk sauran su kasance kan matsayinsu.

“Zan daukeku mu tafi tare da shawarwarinku da biyanku bisa goyon da kuka bai wa gwamnatina da kuma matsayina na shugaban jam’iyyar a jiha, zan tabbatar na cika alkawuran da na dauka muku.

“Ni ina daya daga cikin gwamnonin da suke goyon bayan karin wa’adin, kuma nayi ne da kyakkyawan fata, domin gujewa rigingimu a jam’iyya, ba wannan kawai ba zan iya rasa damar da nake dashi a Fati daga wasu guruf da daidaiku” inji Bindow.

Gwamna Bindow Jibrilla, ya kuma bukaci shugabannin jam’iyyar a jihar da su yi watsi da batun siyasar kudi kamata ya yi a duba cancanta “ni jin ni ba zan baiwa jam’iyya da jama’ar Adamawa kunya ba” inji Bindow.

Tun da farko da yake jawabi shugaban jam’iyyar APC a jihar Ibrahim Bilal, ya godewa gwamnan bisa tsayawar da ya yiwa shugabannin jam’iyyar a wannan bayuwacin lokaci.

Shugaban jam’iyyar ya kuma tabbatarwa gwamnan da cewa suna goyon bayan sake zabensa a babban zaben 2019, ya ce zasu bashi dama shi (Bindow) zai samu tutar takara gwamna karkashin jam’iyyar a jihar Adamawa.

Ibrahim Bilal, ya kuma sanar da mutuwar shugaban rikon jam’iyyar APC a karamar hukumar Maiha, Mista John Batam, inda ya bukaci shiru na minti guda domin girmamashi.

A na ganin daukan wannan matakin da gwamnan ya yi bai rasa nasaba da tsaron kwace jam’iyyar da tsohon gwamnan jihar Murtala Nyako idan anyi zaben, saboda haka wannan ita ce damar da ta ragewa gwamna Bindow.

 


Advertisement
Click to comment

labarai