Connect with us

LABARAI

Ana Samun Gagarumar Nasara A Rigakafin Shan Inna A Fagge –Abdullahi

Published

on


Al’ummar karamar hukumar Fagge suna bada cikakken hadin kai da goyon baya domin samun nasarar riga-kafin cutar shan inna. Shugaban karamar hukumar Alhaji Ibrahim Muhammad Abdullahi da akafi sani da Shehi ya bayyana haka da yake zanawa da jaridar LEADERSHIP A Yau.

Shehi ya ce karamar hukumar karkashin jagorancinsa ta dauki matakai da suka kamata wajen ganin al’ummar yankin sun bada hadin kansu wajen yakar cutar da take kassara rayuwar kananan yara.

Ya ce dukkan masu ruwa da tsaki a harkakokin al’umma na karamar hukumar tun daga kan ma’aikata,hakimin Fagge da masu unguwanni da malamai na addimi duk suna kokarin wayar dakan al’umma kan alfanun yin riga-kafin dan hana yaduwar cutar kuma ana samun nasarar hakan.

Alhaji Ibrahim Muhammad ya ce irin wannan hadin kai da ake  samune yasa dogon lokaci ba’a  sami alamar bullar cutar a fagge ba sakamakon irin yanda iyaye ke bada goyon baya akan riga-kafin.

Shugaban karamar hukumar yayi kira ga iyaye suyi watsi a duk wata jita-jita da wasu ke yadawa na cewa riga-kafin nada wata mummunar manufa ta boye, karya ce kawai ake yadawa kuma su al’ummarsu sunada wayewa na sanin duk wani abu dazai cutar dasu, su kuma a matsayinsu na shugabanni ba za su bari a kawo wani abu da suka san zai cutarda da jama’a ba.

Shehi ya ce karamar hukumar za ta ci gba da bai wa harkar bunkasa  lafiya kulawa ta musamman da kula da tsaftar muhalli wanda shima riga-kafine ga cutuka masu yaduwa.

 


Advertisement
Click to comment

labarai