Connect with us

LABARAI

An Tabbatar da Ingancin Darussa 21 a Jami’ar ATBU

Published

on


Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) dake Bauchi sun samu tabbacin ci gaba da gudanar da darussa (kwas) guda 21. Wannan tabbacin ingancin gudanar da wadannan darussan ya samu ne daga hukumar kula da ingancin Jami’o’i ta Nijeriya wato NUC.

Wannan sanarwar ta bayyana ne ta hannun Jami’in hulda da Jama’a ta Jami’ar wato Andee Iheme a ranar Alhamis din da ta gabata a Bauchi.

Iheme ya bayyana cewa; sun samu tabbacin ingancin wadannan darussan ne a wata takarda da aka aiko musu daga ofishin hukumar kula da ingancin Jami’o’i na kasa dake Abuja.

Ya tabbatar da cewa; dukkan darussa 9 da ake gudanarwa a tsangayar kere-kere, an tabbatar da ingancinsu sai dai darasi guda daya wanda yake bukatar a kara inganta shi kafin a amince da shi.

Ya ce; darussan sune; “Noma (agriculture), bio-resources, kimiyyar sinadarai, kimiyyar harkokin tsare-tsaren muhalli, Komfuta, Lantarki, Kanikanci, Kimiyyar Sinadaran Man fetur, Kimiyyar motoci.”

Ya kara da cewa; darasin da yake bukatar a kara inganta shi kafin a tabbatar da su, su ne darasin kimiyyar karafa wato (Mechatronics) da kuma kimiyyar tsare-tsare wato (System Engineering).

Sai dai ya tabbatar da cewa; dukkanin darasin dake tsangayar Ilimi, an tabbatar da ingancinsu sai dai guda daya tak wanda yake bukatar a kara inganta shi.

Ya ce; haka abin yake a tsangayar noma, dukkanin darussan an tabbatar da ingancinsu. haka ma tsangayar kimiyya da fasaha, cikin darussa hudu da aka gabatarwa da hukumar, darussa biyu wato lissafi da Komfuta suka samu tabbacin an inganta su. a tsangayar kimiyyar muhalli kuwa, suma dukkanin darussan an tabbatar da ingancinsu.

Ta sanarwar “darussan sune‘Kuantity Surbeying,’ Tsare-tsaren Biranai (URP).” haka labarin yake a tsangayar gudanarwa. Inda aka tabbatar da ingancin darussan aikin banki da sha’anin ku]i.

Iheme, ya tabbatar da cewa; Mataimakin Shugaban Jami’ar wato Saminu Ibrahim ya tabbatar da cewa za su yi dukkanin mai yiwuwa wajen ganin sauran darussan da ba su samu tabbataccen inganci ba, sun samu wannan ingancin daga Hukumar ta NUC.

Sannan ya tabbatarwa da Malamai da daliban dake Jami’ar cewa; dukkan wani shirye-shirye an ri ga an gama shi wajen ganin duk inda NUC ta bijiro da shi wanda ya hana a inganta sauran darussan, za a bi domin ganin an gyara har su samu suma tabbacin inganci. Saminu Ibrahim ya bayyana Jami’ar ATBU a matsayin muhalli na neman ingantaccen Ilimi, ya ce; ba zai bari wannan kallon da ake yiwa Jami’ar ya zama an daina ba musamman a karkashin jagorancinsa.


Advertisement
Click to comment

labarai