Connect with us

LABARAI

An Gabatar Da Maulidin Manzon Allah (S.A.W) Da Na Sayyada Fatima A Kano

Published

on


Daya daga cikin fitattun mabiya Darikar Tijjaniyya, Alhaji Ali Nuhu Wali wanda mahaifin sa ne ke yi wa Shehu Ibrahim Inyass fassarar larabci zuwa Hausa tun zamanin da Shehu Ibrahim Inyass ya hadu da Sarkin Kano, Alhaji da kuma zuwan Shehu Nijeriya a karon farko.

A karshen makon da ya gabata ne Alhaji Ali Nuhu Wali ya shirya Maulidin Manzon Allah da Yar Ma’aikin Allah da kuma Maulidin Shehu Ibrahim Inyass da gabatar da walimar saukar Dalibai guda biyu wanda Allah ya azurta da sauke karatun Littafin Allah Mai tsarki a unguwar Rijiyar Zaki cikin Garin Kano.

Ya ce matsayin Manzon Allah (S.A.W) da kuma matsayi ‘yarsa ya sa duk shekara masoya wadannan bayin Allah masu daraja suke shirya wannan Maulidi don jaddada farin ciki da murna a daidai wannan lokaci domin dai duk wanda ya fahimci matsayin Manzon Allah da matsayin ‘yarsa Sayyada Fatima to wajibi ne a nuna soyayya da kauna, da kuma bayin Allah da suka karantar da matsayinsu kamar su Shehu Tijjani (R.A) da Shehu Ibrahim Inyass da ma sauran bayin Allah magabata masu hidima a tafarkin addini na gaskiya.

Haka kuma bukin Mauludan uku a hade na bana ya hada da saukar karatu na dalibai biyu; Muhammadul Amin Ali Nuhu da Fatima Ali Nuhu wanda suka azurta da sauke karatun alkur’ani mai girma.

Malamai da dama ne suka gabatar da jawabi akan darajoji da nagartar Manzon Allah (S) da kuma daukaka da girman Sayyada Fatima, sai kuma irin gudun mawar da Shehu Ibrahim Inyass ya bayar ga Addinin Musulunci.

 


Advertisement
Click to comment

labarai