Connect with us

KIWON LAFIYA

Amfanin Dan Itacen ‘Pear’ Ga Lafiyar Mutum

Published

on


Dan itacen ‘Pear’ yana taimakawa wajen yakar cutar daji da taimakawa hanin ido da bayar da kariya wajen kamuwa da ciwon(osteoporosis) da sauran cututtuka.

Kayan lambu kamar kyauta ce ga dan adam harda itacen ‘Pear’ domin kuwa ya sha bam-bam da sauran kayan marmari.

Dandanon sa baida iyaka kuma dauke yake da kayana kara kiwon lafiya ga dan adam.

Kamar yadda Chris Gunnar ya bayyana shi, yana dauke da sanadaran dake karawa zuciya lafiya, misali sanadarin (fatty acids), yanada kashi 77 bisa dari na sanadaran(calories) da suke fita daga cikin kitse, inda hakan, inda yake sanyawa daya daga cikin sa kayan lambu mai kasancewa.

Sai dai, yana da mahimmanci a san da cewa, dan itacen ‘Pear’ bawai kawai yana dauke da sanadarin(fat) bane domin mafi yawanci yawan sanadarin (fat) yana dauke da sanadarin(oleic acid) ne.

A daya bangaren kuma, sanadarin(oleic acid), shima yana dauke da alfanun karin kiwon lafiya, wadanda suka hadada, rage karfin ciwon hawan jini da rage kiba da bayar da kariya ga kwayoyin halittar jikin mutum daga yin dameji da bayar da kariya ga ciwon Sijari na(type 2) da kuma bayar da kariya ga kwakwalwar mutum.

Ga Amfani Shida Da Dan Itacen ‘Pear Ke yiwa Lafiyar Mutum

  1. Yana daidaita hawan jini.

Kamuwa da hadarin bugun zuciya da shanye war barin jiki da ciwukan koda, suna aukuwa ne sakamakaon dagawar hawan jini saboda karancin sanadarin(potassium).

Amma ana san cewar Ayaba tana dauke da isasshen sanadarin(potassium) haka bincike ya nuna cewar, sanadarin (potassium) dake cikin dan itacen ‘pear’, yafi yawa idan ana maganar saukar hawan jini.

  1. Ana yin amfani dashi wajen magance jin zafin gabbai.

Kuma wannan jin zafin zai iya zama muni saboda cin abinci kamar Alkama ko da Dawa da shan Sikari da sauran su.

Har ila yau, dan itacen ‘pear’, yana daya daga cikin da a kimiyance aka sani yana samar da sauki.

Yana dauke da isassun sanadarai na (fats) da(phytosterols) da (antiodidants) dana  Bitamin E da  Bitamin C da kuma (carotenoids) wadanda suke bayar da dauki ga alamomin ciwon babbai.

  1. Yana bayar da kariya daga kamuwa da cutar daji.

Bincike ya nuna cewar, yawan cin sanadarin (folate) dake a cikin abinci, zai iya bayar da kariya daga jin ciwon ciki da cutar daji ta mahaifa.

Sai dai, abubuwan da suke kashin bayan samar da wannan ragin a yanzu ba’a san su na amma masu bincike sunyi amannar cewar, sanadarin (folate) yana bayar da kariya a yayin gwajin jini da ake kira a turance(DNA) da kuma wanda ake kira(RNA) a lokacin rarraba kwayoyin

halittar dake cikin jini.

Sun kuma bayar da shawara cewar, dan itacen na ‘pear’ zai iya taka rawa wajen magance cutar daji haka a wasu binciken da aka gudanar sanadarin (phytochemicals) da aka fitar daga cikin dan itacen ‘pear’ zai iya taimakawa wajen  kare mutuwar kwayoyin halitta.

Bugu da kari, cin abinci mai gina jiki  ya nuna cewar yana rage yin damejin sanadarin (chromosomal) sakamakon shan magunguna.

  1. Bayar da kariya ga ido.

A cewar binciken da aka gudanar a baya, wasu daga cikin sanadarai  (antiodidants) kamar na (lutein) dana (zeadanthin), ana bukatar su wajen inganta ido.

Dan itacen ‘pear’ musamman haifar da  mai wuyar sha’ani kamar na sanadaran(antiodidants) da ake samu daga sauran hanyoyin abinci, wanda yake dauke dasu da yawa.

Sanadarai sune kan gaba wajen kawar da hadurran ciwuka musamman a tsakanin mata.

  1. Yana taimakawa wajen kare fitar numfashi marar dadi.

Domin kamar yadda aka sani ba wai rashin kiwon lafiyar baki ne lallai yake janyo numfashi marar dadi ba, amma harda rashin cikin mutum ya yi daidai yadda ya kamata.

Saboda haka, idan kana fuskantar wannan yanayin, yana da kyau ka dinga amfani da dan itacen ‘pear’ don ya gyara maka bakin ka da kuma hanjin cikin ka.

Har ila yau, yana taimakawa wajen kawar da numfashin baki marar dadi.

  1. Cin abinci mai gina jiki ga mata masu juna biyu.

Yin amfani da dan itacen ‘pear’, yana taimakawa kiwon lafiyar su.

Yana dauke da dimbin sanadarin(folic acid) yana kuma taimakawa jaririn dake cikin ciki da samar da kiwon lafiya ga kwakwalwa halittar jikin mutum da kuma taimakawa jini.

Bugu da kari, yana taimakawa wajen saukar da sanadarin(cholesterol) zuwa kasa ga mata masu juna biyu da rage hadarin kamuwa da jin kasala.

A karshe, yana da kyau a sani cewar, alfanun da dan itacen ‘pear’ yake dashi wajen kiwon lafiya a takaice basu da iyaka.

Taikamawar da yake yi wajen yakar ciwon daji da baiwa fatar jiki kariya, yana kuma taimakawa wajen rage kiba da daidaita ciwon Sikari an kuma gano cewar, mutanen da suke cin cin dan itacen ‘pear’ da yawa, suna kasancewa a cikin koshin lafiya.

 


Advertisement
Click to comment

labarai