Connect with us

WASANNI

Yakamata Ozil Ya Taimaka Wa Arsenal Ta Lashe Manyan Kofuna –Garry Nebille

Published

on


Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United kuma mai sharhi akan wasanni a kasar ingila, Gary Nebille, ya bayyana cewa sakamakon sake sabon kwantaragi da dan wasa Mesut Ozil yayi a kungiyar Arsenal a yanzu lokaci yayi da zai taimakawa kungiyar ta lashe manyan kofuna.
Tun a farkon kakar wannan shekarar ne dai ake ta rade-radin cewa dan wasa Ozil da Aledis Sanches zasu bar kungiyar sakamakon kin amincewa da sabon kwantaragin da kungiyar tayi musu tayi, sai dai Sanches shi tuni yakoma Manchester United yayinda Ozil yaci gaba da zama a Arsenal din bayan ya amince da sabuwar yarjejeniyar da suka kulla.
Gary Nebille yace, yanzu lokaci yayi da Ozil zai nunawa duniya cewa babban dan wasane kuma kwararre ta hanyar jagorantar Arsenal ta lashe babbar gasa kamar Firimiya ko kuma gasar cin kofin Europa da kungiyar take bugawa a wannan kakar.
Ya cigaba da cewa yanzu kungiyar ta Arsenal tanada manyan yan wasan gaba wadanda zasu bawa kowacce kungiya wahala ba kawai a kasar ingila ba har a nahiyar turai saboda haka akwai bukatar kungiyar ta lashe wani kofi babba.
Ya ce ya zama dole Arsenal din ta lashe kofin Europa da yanzu takai matakin wasan kusa dana karshe sannan kuma yakamata su sake shiri domin fuskantar kakar wasa mai zuwa.
Ya kara da cewa rashin Aledis Sanches a kungiyar ba karamar matsala bace domin babba ne kuma kwararren dan wasa amma tunda har Ozil yaci gaba da zama yakamata kungiyar ta dawo cikin manyan kungiyoyi hudu na gasar firimiya sannan kuma su koma matsayin da aka san kungiyar a baya.
Kawo yanzu dai Arsenal tana mataki na 6 a gasar firimiya sai dai takai matakin wasan kusa dana karshe a gasar Europa inda zata kece raini da kungiyar Atletico Madrid ta kasar sipaniya a karshen wannan watan.


Advertisement
Click to comment

labarai