Connect with us

ADABI

Tsohuwar Taska: Littafin ‘In Da So Da Kauna’

Published

on


07038339244  [email protected]

Littafin ‘In Da So Da Kauna’ na Ado Ahmad Gidan Dabino, MON, an fara wallafa shi a shekarar 1991, wato a yanzu ya na da shekaru 27 da haihuwa kenan.

Labarin In Da So Da Kauna labari ne na soyayya a tsakanin Sumayya da Muhammad. Sumayya yarinya ce kyakkyawa `yar gidan masu hannu da shuni. An yi soyayya irin ta zamanin da, inda Sumayya ta rubuta wa Muhammad wasika a kan irin son da take yi masa, amma da farko Muhammad ya ki, saboda yana ganin sun sha bambam ta fuskar aji, ma`ana ita Sumayya ta fito daga gidan masu arziki, a yayin da shi kuma Muhammad ya fito daga gidan talakawa.

Manyan taurarin wannan labarin sun hada da: Muhammad, Sumayya, Abdulkadir, Naja`atu, Saratu, Hajiya-Mai-Idon-Cin-Naira. Farkon harkallar wannan labarin ta faro ne daga inda Sumayya ta hadu da Abdulkadir. A wurin wani biki ne, Sumayya ta hadu da Abdulkadir, saurayi dan gidan masu hannu da shuni. Abdulkadir ya fada cikin soyayyar Sumayya, amma ta ki ba shi hadin kai. A gefe guda kuma ga kakar Sumayya nan Hajiya-Mai-Idon-Cin-Naira, ta kallafa ranta a kan Abdulkadir, saboda tana ganin shi ne ya fi dacewa da ya auri Sumayya a maimakon Muhammad. Daga nan ta shiga neman magani a wurin bokaye domin ta raba Sumayya da Muhammad.

Idan da za a lissafa manyan labarun soyayya na Hausa guda goma wanda ba za a ta6a daina yayinsu ba, to lallai littafin In Da So Da Kauna zai shigo cikin jerin na daya zuwa na uku. Zan iya kwatanta littafin In Da So Da Kauna da littafin soyayya na Ingilishi mai suna Pride and Prejudice na Hausa, saboda tsananin kar6uwarsa.

Wannan littafi na In Da So Da Kauna ya yi tasiri sosai a fagen adabin Hausa, ya zaburar da wasu makaranta na wancan lokacin ta yadda har suka rikide suka koma marubutan kansu, sannan ya samu kar6uwa sosai ta hanyar yaduwa a sassan duniya daban–daban.

An fasara wannnan littafin zuwa harshen Ingilishi da sunan The Soul of my Heart.

 

Cikin littafin na IN DA SO DA KAUNA akwai baitukan soyayya da Muhammad ya yi wa Sumayya:

1- Bismil ilahi jallah ya sarki gwani roko na ke a gare ka sarkin mulki.

2- Karan basira har hazaka rabbana , domin na wake sahiba mai kirki.

3-   Allah dado tsira ga Ahmadu sayyadi, alay sahabbai tabi’ai ba burki.

4- Waka ta soyayya na ke so zana yi, a gare ki lallai don na nuna halinki.

5- Tauraruwata ya ki gani sarauniya , ni ne masoyin naki mai kaunarki.

6- Sumayya girman sonki birnin zuciya, ya zarce ma in bayyana shi da baki.

7-   Kogi na kauna na shige na dulmiye, na cusa kaina can cikin kaunarki.

8-   Ko da ana jifa da harbi zan shiga , raina yana matsayin a fansar naki.

9- Amma akwai makiya da ke yin hassada, burin su kullum kadda in aure ki.

10- Suka su ke kullum suna zargi kwarai, Allah yasa su gane aikin kirki.

11- Sun ce da ni talakan da ba shi da ko dari, kuma banda halin ma da

zan aure ki.

12- Sun manta Allah ne ya ke yin arziki , in yai nufin ya azurta mamman naki.

 

Ga duk wani ko wata mai sha`awar karanta tsofaffin littattafan Hausa, to ya kamata a nemi littafin In Da So Da Kauna a karanta.

A gaida babban yaya, Ado Ahmad Gidan Dabino, MON. Allah ya ja kwana.

 


Advertisement
Click to comment

labarai