Connect with us

RA'AYINMU

Sunayen Berayen Gwamnati: Share Fagen Siyasar 2019

Published

on


A kwanakin baya ne babbar jam’iyyar adawa a Nijeriya, PDP, ta bugi kirji ta kalubalanci jam’iyyar mai mulkin kasar, APC, da cewa, idan ta isa ta fitar da jerin sunayen berayen da su ka sace kudaden gwamnati, musamman a zamanin da ita PDP din ke rike da madafun ikon kasar. Ita kuwa APC ba ta yi kasa a gwiwa ba, sai ta biye wa PDP din, ta fitar da jerin sunayen wasu ’yan siyasa da a ke tuhuma da laifukan sace-sacen kudaden gwamnati a lokacin da a ka damka mu su amanar ’yan kasa.

Tabbas jerin sunayen, wadanda ministan yada labarai Mista Lai Mohammed ya fitar a lokuta mabambanta, sunaye ne na ’yan siyasar da ke fuskantar kalubalen tuhuma a gaban kotuna daban-daban ko hukumomin yaki da cin hanci da rashawa na kasar, ICPC da EFCC ko kuma hukumar kula da da’ar ma’aikata ta Nijeriya. A wannan kam bau karya, babu sharri, to amma fa yawancinsu har kawo yanzu gwamnatin ta APC ba ta iya yin nasarar kama su da laifi a gaban kotu ba, ballantana a hukunta su.

Bugu da kari, babban abin lura shi ne babu ’yan APC ko kwaya daya, wadanda a baya su ke gwamnatin PDP, amma su ka yi tsallen badake su ka dawo APC din ba, bayan da su ka raba hanya da tsohuwar gwamnatin ta APC. Abin nufi a nan shi ne, maimakon gwamnatin APC ta fitar fa jerin sunayen duk wadanda a ke zargi da sace dukiyar al’ummar kasa a lokacin na PDP ba tare da warewa ko la’akari da wadanda su ka fice daga PDP din su ka dawo APC ba, a’a, sai gwamnatin ta fitar da zallar wadanda har yanzu su ke cikin PDP kadai; sauran kuwa da alama sun sha kenan, domin ba sa cikin wadanda za a yiwa terere.

Daga dukkan alamu, hakika wannan salon ba komai ba ne face tabbatuwar sharar fage ga siyasar 2019, lokacin da za a gudanar da manyan zabukan kasar.

Ita kanta PDP ta yi tsaurin kai da yawa da ita fitowa ta murje idanunta a gaban ’yan Nijeriya har ta kalubalanci APC a kan ta idan ta isa ta fitar jerin sunayen wadanda ta ke zargi da kasancewa manyan beraye a lokacin baya.

Kada manta, dukkan barnar da ta faru a gwamnatin baya, ta faru ne fa a karkashin gwamnatin PDP, wacce ita ce mulki kasar tun daga lokacin da Nijeriya ta dawo mulkin farar hula, bayan da soja ya mika mulki ya koma bakin aikin da kundin tsarin mulki ya tanadar ma sa na tsaron kasa.

Shekaru 16 PDP ta yi ta na rike da madafun iko tun daga 1999 har zuwa 2015, inda ta yi faduwar bakar tasa a babban zaben shekarar, wanda wannan shi ne faduwar zabe irinsa na farko a tarihin siyasar kasar, domin a lokacin ne shugaban kasa mai ci ya fadi a zabi yayin da ya ke yunkurin yin tazarce a karo na biyu.

To, amma a zahirin gaskiya za a iya cewa, talakan Nijeriya ba fitar da jerin sunaye ya ke bukata ba; abinda ya fi bukata shi ne a hukunta wadanda su ka aikata laifukan a cikin shekaru ukun nan da APC ta amshe ragamar mulkin kasar, sannan kuma a dakatar da irin wannan ha’incin ya tsaya cak!

Sai dai kuma wani abin takaici shi ne, ko a cikin gwamnatin ta APC an samu irin wannan matsalar, inda a ke zargin wasu manyan jami’an gwamnatin da aikata irin wannan mummunar dabi’a, amma kuma APC din sai ta yi murkisisi ta ki saka sunayensu a jerin sunayen berayen na na lalitar gwamnatin.

To, karara hakan na nufin cewa, an shiga fagen wasan siyasar 2019 kenan, inda za a cigaba da musayar yawun da ya wuce haka a nan gaba. Ba zai zama abin mamaki ba, idan PDP ita ma ta fitar da nata jerin sunayen, wanda babu tantama za ta kwaye bayan ’yan APC ne, domin ta dauki fansa kan kwance ma ta zani a kasuwa da APC ke shirin aikatawa a yanzu da sunan fitar da jerin sunayen wadanda a ke zargi da aikata hali ko samartakar bera a gwamnatin Nijeriya.

Wannan zai iya bude kofar da ita kuma APC za ta iya mayar da martani ta hanyar sauya wani salon na siyasa, la’alla ma za ta iya yin barazanar kamawa da garkame wasu ’yan siyasar ta PDP, don rufe bakunansu, kamar yadda ita ma PDP din ta yi aikata hakan a baya, inda ya rika yin amfani da musamman EFCC wajen yunkurin hana wasu ’yan adawa takara, la’alla ko da sunans ne dai ya baci ko kuma ta hana su sakat har zuwa lokacin gudanar da manyan zabukan, wanda a sannan kuma lokaci ya kure mu su na dawowa su gyara kimarsu a idanun masu kada kuri’a.

To, ko ma dai mene ne zai faru, a fili ta ke cewa, an gama share fagen siyasar 2019. Shi dan tsako mai rabon ganin badi, ko a na muzuru ko a na shaho, sai ya gani!!!

 


Advertisement
Click to comment

labarai