Connect with us

WASANNI

De Bruyn Da Salah Da Harry Kane na Kokawar Lashe Gwarzon Gasar Firimiya

Published

on


Hukumar kwallon kafar kasar ingila ta fitar da jadawalin sunayen yan wasan da zasu kara domin lashe kyautar gwarzon dan wasan firimiya na bana wato dan wasan dayafi kowanne dan wasa kokari.
Dan wasa Kebin De Bruyn yana cikin yan wasa uku da aka zaba a kungiyar Manchester City bayan dan wasa Lorey Sane da kuma Dabid Silba sai kuma Harry Kane na kungiyar kwallon kafa ta Tottenham dan kasar ingila wanda shine dan wasa na biyu acikin yan wasan da sukafi zura kwallaye a raga.
Muhammad Salah, wanda yafi kowanne dan wasa zura kwallo a raga yana ciki sai kuma mai tsaron ragar kungiyar kwallon kafa ta Manchester United wato Dabid De Gea wanda ya buga wasanni 16 batare da an zura masa kwallo a raga ba.
De Bruyn dai ya zura kwallaye 7 a raga sannan kuma ya taimaka anci kwallaye 12 sai Muhammad Salah wanda kawo yanzu ya zura kwallaye 29 kawo yanzu sannan kuma ya taimaka aka zura kwallaye tara.
Harry Kane, wanda ya lashe kyautar dan wasan dayafi zura kwallaye a raga shekaru biyu a jere da suka gabata shima yana ciki inda kawo yanzu yanada kwallaye 25 sannan kuma ya taimaka an zura kwallaye biyu.
Lorey Sane kuma ya zura kwallaye 9 ne kawo yanzu sannan kuma ya taimaka an zura kwallaye 12 sai kuma takwaransa na Manchester City, Dabid Silba, wanda yaci kwallaye 8 sannan kuma ya taimaka akaci kwallo 11.


Advertisement
Click to comment

labarai