Connect with us

LABARAI

Abdulsamad Zai Gina Asibiti Mai Gadajen Kwanciya 220 A Kano

Published

on


  • Ya Yaba Wa Gwamna Ganduje Da Sarki Sanusi

Hamshakin dan kasuwar nan na Afrika kuma haifaffen Kano, wato shugaban kamfani BUA da 9mobile, Alhaji Abdulsamadu Isiyaka Rabi`u, wanda ya yi fice wajen tallafawa tattalin arzikin Nijeriya da kuma al`umma bakidaya, yanzu haka zai gina wani katafaren asibiti wanda ya kunshi dadajen kwanciya 220 a Kano, wanda kuma a ka kiyasta zai lakwame kudi zambar Naira biliyan 7.5, inda fadin asibitin ya kai mita 15,000, kamar dai yadda rahotanni su ka tabbatar.

Haka kuma a wani labarin daban, Alhaji Abdulsamadu ya yabawa gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, da masarautar Kano a karkashin jagorancin Mai Martaba Malam Muhammadu Sunusi II a kan kokarinsu na inganta harkar auratayya da kuma zamantakewar al’ummar Kano da ma Arewa bakidaya.

Ya fadi haka ne a cikin wata hira da ’yan jarida a dakin taro da ke titin Luggard Road a Kano kwanakin baya.

Haka kuma ya shawarci al`umma a kan su zama masu ba da hadin kai a kan duk wani abu da shugabanni da masana su ka zo da shi, wanda zai inganta rayuwarsu bakidaya.

 


Advertisement
Click to comment

labarai