Connect with us

RAHOTANNI

Yadda Bata-Gari Ke Cin Karensu Ba Babbaka A Kasuwanin Yobe

Published

on


Masu cin kasuwanin mako-mako a jihar Yobe, suna fuskantar barazana daga wasu bata-gari, ta yadda suka kirkiro sabbin hanyoyin yi wa jama’a damfara tare da amshe abin hannunsu.

Mazambatan kan yi amfani da salo kala-kala wajen ha’intar mutumin da tsautsayi ya fada kansa. Yayin da wani lokacin, sukan dana tarkon damfarar jama’a ta hanyar fake wa da karamar sana’a ko kirkirar sana’ar cajin wayar tafi-da-gidanka, inda ta hakan sai su tara kayan jama’a ko su sayi kayanka, da sunan je ka dawo, daga bisani sai ka neme su kasa ko sama.

A lokaci guda kuma, bata-garin kan yi amfani da kananan yara -ka za ta tare suke, su sayi kayanka sai su bar maka yaron, shi ke nan zancen ya sauya. Inda a wani jikon su fake da wasa da maciji- bayan sun hada baki, sai su ba mutum tsoro, wanda da zarar ya firgita sai su tsame shi.

Wani binciken musamman da wakilinmu a jihar Yobe ya gudanar a kasuwanin mako da ke Babban-Gida, ta karamar hukumar Tarmowa, da Garin-Alkali a Bursari da Jajimaji a Karasuwa, sai kuma Gaidam, da takwarorinsu. Inda ya lura da yadda masu cin kasuwanin ke ci gaba da korafin yadda wadannan bata-gari ke cin karensu babu babbaka.

LEADERSHIP A YAU ASABAR ta zanta da daya daga cikin masu cin wadannan kasuwanni, a kowanne mako- Sama’ila Alhaji Sa’idu Gashuwa, ya shaidar da cewa, “ A gaskiya, halin da ake ciki yanzu wasu mazambata sun addabi kasuwaninmu na mako-mako a nan jihar Yobe, saboda kuma yadda suka bullo da sabbin hanyoyi kala-kala wadanda suke amfani da su wajen damfarar jama’a, su kwace musu dukiya.”

“Wani sa’in sai ka ga mutum sanye da babbar rigar alfarma, kai ka ce wani hamshakin mai kudi ne ko wani babban ma’aikacin gwamnati ne, ashe dan damfara ne; kiri-da-muzu ya zare maka idanu ya kwace maka kudi. Irin hakan ya sha faruwa ga abokanmu masu sana’ar dabbobi a nan kasuwar Babban-Gida, da takwarorinta. Sannan kowanne lokaci  canja salo tare da bin hanyoyi kala-kala suke yi wajen kwace wa jama’a kudi. Saboda haka muke kira ga jama’a su rinka yin kaffa-kaffa da mazambata”.

“Ko a makon da ya wuce, akwai wani abokin sana’armu- dan Shuwa, daga jihar Borno, wanda kowanne mako yake zuwa sayen dabbobi a wannan Kasuwar, ya zo da kudi kusan Naira miliyan daya (1,000,000), kawai sai wani mutum ya ja shi gefe, inda ya zare masa ido tare da nuna masa cewa, jami’in tsaro ne, yayin da ya ce ya kawo kudin da suke a hannunsa. Bai yi gardama ba ya mika masa kudin kuma a haka ya tafi abin sa. Kuma irin hakan na faruwa bila adadin, a Kasuwar”. In ji dan Kasuwar.

Bugu da kari kuma, wakilinmu ya gano yadda wani dan damfara yake amfani da kasa dankali wajen ha’intar jama’a a kasuwar Jajimaji a jihar Yobe. A irin wannan nau’in zamba, inda bata-garin ke sayo buhun dankali tare da karkasa shi a bakin rumfa wanda hakan zai jawo hankalin ‘yan’uwansa ‘yan kasuwa wajen amincewa da shi. A cikin wannan halin ya karbi kayan jama’a da dama, ciki har da turamen atamfa, kayan koli da makamantan su, da nufin idan yamma ta yi su dawo su karbi kudadensu.

Yamma tana yi, masu bashi suka yi cincirindo a bakin rumfar mai dankali, shiru ba batu ba labarinsa. A haka mai buhun danklin ya tattara abin da ya rage, sauran kuma suka dauki na damo.

Har wa yau dai, a kasuwar dai, shi ma wani takadari mazambaci ya tattara wayoyin tafi-da-gidan ka- wadanda jama’a suka ba shi caji, kan ka ce ‘biyar’ ya yi gaba da su, wata kila sai gobe kiyama.

Yadda ya tsara al’amarin, shi ne ya nemo wani kwara-kwaran injin bayar da hasken wutar lantarki, ya samu mahadar jama’a  a kasuwar, ya kafe janaratan tare da kayan cajin waya; ya sa kida. Kan ka ce me, jama’a sai kawo wayoyin su suke- manya da kanana. Can, bayan da ya ga babu ido mai yawa a kansa, a haka ya cusa wayoyin jama’a a buhu ya kauce.

A haka injin janarato ya yi ta bada wuta da hayaki, daya bayan daya jama’a suka yi ta taruwa, ana jiran mai cajin, har kusan magariba babu amo ba labari.

A lokacin da na leka kasuwar Gaidam, can kuma wata irin sata ce ake yi wa jama’a ta kiri-da-muzu tare da hadi da renin wayau. Inda gungun ‘yan sane suka bullo da sabuwar hanyar kwace kudin jama’a, a cikin baki alaikum.

Yadda suke yi a kasuwar Gaidam, da zarar ‘yan sha-ukun sun kula akwai kudi a jikinka, to sai abin da Allah ya yi, za su datse ka a wata kwana, su yi maka sane (tsame kudin aljihunka) ta hanyar ba ka tsoro da macijin da suke wasa da shi, a lokacin da ka firgita, kafin ka dawo hayyacinka sun gama maka aiki. Kuma ka neme su sama ko kasa- har da mai wasa da macijin, ka rasa.

Wakilinmu ya zanta da jama’a da daman gaske a kasuwar ta Gaidam, sun bayyana cewa, baya ga sane damfara tare da wala-wala, wani sa’in kuma har da damfara ta hanyar sojan-gona; idan mazambatan suka ga kudi a gunka, kuma da zarar sun ganka ‘haka-haka’ sai su ce maka su jami’an tsaro ne, su tuhume ka da kasancewa dan Boko Haram, nan take jikin mutum ya dauki tsima. A haka za su amshe ‘yan kudin da ke jikinka.

Bisa ga wannan ne ‘yan kasuwar hadi da sauran jama’a suka yi kira na bai-daya ga gwamnatin jihar Yobe tare da jami’an da nauyin kare jama’a da dukiyoyin su ya hau kan su da cewa su kawo dauki domin shawo kan wannan matsala, wadda idan aka bar abin ya ci gaba zai ta karuwa ne.

Saboda haka ya zama wajibi ga dukkan jami’an da ke da alhakin dakile wannan babbar annoba da su tashi tsaye wajen ganin sun kawo karshenta.

Ga su kuma al’umma ya kamata su kiyaye, sannan duka wani wanda suka gab a su amince masa ba kar su yarda su kulla wata hulda da shi, sannan da zarar wani ya fara yi maka barazana maza ka tona asirinsa. Kada a bari a dinga yin fargar jaji.


Advertisement
Click to comment

labarai