Connect with us

WASANNI

Real Madrid Da Bayern Munchen Da Kuma Liberpool Da Roma A Gasar Zakrun Turai

Published

on


Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid za ta kara da kungiyar Bayern Munich a gasar cin kofin zakarun Turai yayin da Liberpool za ta kara da Roma wadda tayi waje da Barcelona a gasar.

A jiya ne hukumar kula da kwallon kafar nahiyar turai ta raba kungiyoyin hudu da suka rage a gasar bayan kungiyoyin sun samu nasara a wasannin da suka buga na kusa dana kusa dana karshe.

Za a yi wasannin a ranakun 24/25 na watan  nan na Afrilu, sai zagaye na biyu a ranakun 1/2 ga watan Mayu mai zuwa kuma a watanne za’a buga wasan karshe.

Za a buga wasan karshe na gasar zakarun Turai a birnin Kieb, na Ukraine, ranar 26 ga watan Mayu.

Real Madrid ta fitar da Jubentus a wasan dab da na kusa da na karshe, yayin da Roma ta fitar da Barcelona.

Ita kuwa Liberpool ta doke Manchester City, sai Bayern da ta yi waje da Sebilla ta kasar sipaniya a wasanni biyun da suka fafata

A bara ma Real Madrid, wacce ke rike da kanbun, ta fitar da Bayern a kan hanyarta ta lashe gasar sai dai Bayern Munchen na kokarin lashe gasar a karon farko tun shekara ta 2013.

Bayern ce za ta fara karbar bakuncin wasan farko, yayin da Roma za ta ziyarci Liberpool a wasan farko.


Advertisement
Click to comment

labarai