Connect with us

MAKALAR YAU

Muhimmancin Hakuri A Rayuwa

Published

on


[email protected] 08065683849

Hakuri wani abu ne wanda ake bukatar  mutum  ya sa tawali’u, dauriya juriya, da rashin damuwa a ransa, musamman ma idan yana bukatar mallakar wani abu a rayuwarsa, ya jira sai yadda hali ya yi, wato shi duk yadda  Allah ya yi, babu wata damuwa. Ba wai sai ya ce shi dole sai ya samu wani abin da ya sa a gabansa ba, wanda shi kuma a wannan lokacin yake son sai ya kai ga mallakar, ko kuma ta halin kaka duk ya tashi ya damu kansa har ma ya damu na wasu. Bayan kuma Allah madaukakin sarki ya yi mana horon da mu rika yin hakuri a kan al’amuran rayuwa, saboda duk yadda ake cikin tsanani , sauki fan a nan zuwa, saboda sai an yi hakuri kafin a samu cim ma buri, ai an hada da hakuri kafin a samu nasara a dukkanin abubuwan da aka sa gaba, gaggawa dai kowa ya san aikin Shaidan ce, saboda duk wani abin da aka yi shi cikin gaggawa, ba kasafai ake cim ma wani buri mai amfani da gamsarwa  ba, daga karshe kuma ana yin da-na-sani ne wadda keya ce kowa ya sani, a kuma baya take.

Ba kowa ba ne yake iya zama shugaba, duk yadda aka yi sai wani ya sa hakuri tukunna, idan kuma haka mutum ya daukar ma ransa, zai dade yana shan wahalar rayuwa  ta duniya, domin bai san yadda Allah ya tsara ma shi a rayuwa ba. Hakuri baya baci kamar yadda marigayi Alhaji Adamu Danmaraya Jos ya bayyana cikin wata wakarsa, wadda yake cewa ‘’Hakuri  ba ya baci hakuri abin Manzon Allah, in  mutum ya cuce ka, in mutum ya zage ka, sai ka bar shi da ya Allah, tun da Allah  shi yay yi shi, kuma Allah  shi yay yi ka, sai ka bar shi da ya Allah, sakayya na gun Allah.

Sau da yawa a rayuwa abubuwa da dama suna faruwa, idan ma mutum ya dubi yadda Allah ya halicci  ‘yan yatsun hannun shi, ai wannan ma ya isa ya kasance wani babban misali, kuma wani wa’azi ne wanda mutane ya dace ace, tuni sun fahimci hakan, to amma ina ai ba duka  ne suke tunanin hakan ba. Idan yana son ya mayar  da duk yatsun hannun su kasance dogaye, ko kuma gajajjera ai da yayi hakan ba tare da yin shawara da wani ba. Ya kuma fi mu sanin halin kowa, shi yasa yake ba kowa duk abin da ya ga ya fi dacewa da shi. Duk abin da mutum ya ga Allah subhanahu wata’ala ya ba shi, shi ya ga ya fi dacewa da shi, duk wata maganar  ma da zai yi , ta ko abin bai burge shi ba, wannan kuma ba za ta yi ma sa wani amfani ba. Ai dama shi tagumin mutum dama baya wuce habar shi.

Halin da ake ciki yanzu rashin hakuri shi ne ya mamaya yawancin wasu al’amura na rayuwar wasu, saboda su ba su san a ba su hakuri ba, ko kuma su ga lalle ya kamata su yi hakurin, idan muka dubi misali idan jarabawa ce aka yi a makaranta, kowa akwai abin da Allah yake ba shi, ba kuma dole ba ne, ya yi dai dai da na wani ba. Koda kuwa  ita amsar jarabawar ce aka rubuta akan Allo, wani ba zai iya juya ba, koda kuwa an ma ace ma shi ya juya din, a ce ma amsar ce aka rubuta. Wani zai samu digiri mai daraja ta daya, wani ta biyu wadda take sama, sai kuma wadda take kasa-kasa, akwai digiri mai daraja ta uku, sai kuma na karshe ana kiran shi  (Pass) amma abin ba wani yabo bare fallasa dangane da shi sakamakon, haka ne da dace da shi, sai kuma na karshen shi gaba dayan ma bai tare da wata nasara, sai dai rashinta. To haka abin yake a rayuwa bama sai kawai a makaranta ba, rayuwa ta yau da kullun tana bukatar yin hakuri, tsakanin mata da miji akwai bukatar a rika yin hakuri, idan aka ce babu shi, to za a dade ana kasancewa cikin matsala har akai ga yin zaman manja da doya, idan ma ba sa’a aka yi ba to shi auren ba zai yi wani nisa ba, sai an samu rabuwa.

Idan muka  kalli shi al’amarin shugabanci muka kuma kale shi ta ko wadanne bangarori na rayuwa , za mu iya gane cewa matsaloli na tasowa, a duk lokacin da wata maganar da ta shafi zabe ta taso, ba fa kowa ba ne yake kasancewa shugaba ba, watakila ma shi mutum bai da masaniyar, sai yayi shugabancin ba, koda kuwa na shugaban masu share kasuwa ne, idan dai  ba a son shi fa, to bafa a son nasa ke nan , duk yadda, zai yi sai dai yasa hakuri, idan kuma yaki to sai ya  hadu da  ikon Allah, wanda sai ya girgiza shi watarana , duk kuwa yadda yake ganin shi al’amarin. Amma ka wai hakanan, sai kaga wasu suna ta kai gwauro su kai mari muddin dai, wata maganar shugabanci ta taso,  wani shi yana iya yin har ma abin da bai dace ba, yana iya yi, saboda dai kawai a rika kiran shi da sunan shugaba, koda kuwa na masu sharar kasuwa ne, abin  Allah ya dade da tarfa wa garin shugabanci ruwa. Sai kaga ana ta tada kura, wasu ma har su kai ga kauce hanya suke yi, basu ko tunawa da shi wannan bawan Allah wato hakuri, idan ka ga ma wanda ke yin shi sai a rika ce mai, idan bai yi sa’a ba, har ma sai duniyar ta kai ga kware mai bai san halin da ake ciki ba, ko kuma ya kasance kamar ya rako wasu duniyar ne, su suna tatsar nono, shi kuma ya rike masu kahon. Hakuri shi ne wanda idan aka yi juriyar yin shi watarana sai dai kawai mutane su rika maganar Allah sarki dubi wane don Allah sai kace ba shi bane wane dan gidan wane, da shekarun baya ba, ya shiga cikin kwata ko kuma ya fada manja ya  kuma bare ma shi, amma kuma da ya yi hakuri, yau ga shi, ya zama wanda kowa yake son yin hulda da shi. Amma shi kuwa dan’uwan dayan wanda ya biye ta wasu, yana ganin shi bai sanwata maganar hakuri ba, shi ma din bai wuce watarana a wuce da shi yayi wani abin fadin saboda, ya sa rashin hakuri a zuciyar shi, sai yayi yadda wane da wancan suka yi, yaya za ayi ace kamar shi har su wane ake maganarsu, amma shi ba ma wanda ke maganar shi, da haka ne wasu suna iya ganin abin kamar da wasa yake yi wato ita maganar daya furta, to ashe shi bada wasan yake yi ba, sai ya kai ga aikata abin da, ko abubuwan da ba shi kadai zai shafa ba wato shi kanshi sai kashin kajin,  ya kai ga shafin shi ,sai mutane da yawa, ba don komai ba, sai saboda yayi watsi da hakuri  ne, ya rungumi shi rashin hakurin.

Duk idan rashin hakuri ya hadu da karya saboda ai dama gidansu daya ne, suna kuma haduwa sosai, saboda kamar nau’in turaruka ne, akwan wadanda za a hada, kamshin abin ba a cewa komai, akwai kuma wadanda za a hada sai kawai aga mutane  suna ta toshe hancinsu saboda wari. Akwai kuma wadda take  taka masu baya wato son zuciya, wadda ita ta kasance ne tamkar daddawa, gishiri , maggi  kai har ma da Onga wajen tallabo hankalin wanda dama shi  ‘’Mai neman kuka ne, sai kuma ga shi  har an kai ga jifar shi da kashin Awaki’’. Idan har aka samu shi irin wannan hadin to shikenan sai kowa ya samu wuri ya zauna, domin sanin lalle bada dadewa ba ne, sai an samu labarai da dumi-duminsu.

 


Advertisement
Click to comment

labarai