Connect with us

ADABI

Mahammadu Gambo Mai Wakar Barayi: Tsakanin Tuba Da Adabi (3)

Published

on


08065533969  [email protected]

Tsakanin ra’i da ra’ayi

Dalilin da ya sa ake nuna wa wannan fage irin na adabin Gambo wariya bai wuce madafar nazari ba. Yawancin nazarin adabi bai wuce jigo da warwara ba, in an motsa a kara salo da zubi da tsari. Sai dai mun manta ko mun ki mu amince tuni an wuce wannan ra’i, Wanda muka yi wa shimfida, ya kuma zaune yawamcin nazarce-nazarcenmu. Shi kuma ra’in lalatattun lamurra (Kueer Theory) da suka hada da sata da luwadi da karuwanci da madigo da batsa da bore da makamantan su, da kila zai iya yi mana jagora bai da mazauni a yawancin adabin Afirka, (dubi Olaniyan & Kuason;2007). Kamar yadda masu nazari sukan yi bayani, madigo da luwadi da karuwanci da sata, bakin al’amurra ne a nahiyar Afirka.

Idan ana maganar su a cikin aikin adabi ana kallon su ne ta yadda suka shiga cikin rayuwar mutanen Afirka, ba irin yadda suka wakana a rayuwar ba, ma’ana wadannan abubuwa al’ada ce irin ta Turawa da Hausawa suka gamu da ita a wani zamani. Shi ya sa ko a ra’in lalatattun lamurra aka rasa yadda za a bullo musu, sai dai a fito da bayanin yadda Adabawan suka shirya shi. Wannan shi (Dunton(1989) da Desai da Munro(2007) suka yi a nazarce-nazarcensu. Luwadi a tsakanin sojoji da wadanda ke yin madigo a makarantun kwana na ‘yan mata wadanda zuwan boko ne ya ta’azzara su, hakan ne ko ba haka ba ne ya danganta ga irin ra’in da mai nazari ya yi amfani da shi.

Da kila wadannan masana sun ci karo da wakokin Gambo da kila sun yi wa nazarinsu bita, domin a nan ne aka fito da abin da ra’in ke bukata sosai.

Domin abin da Gambo ke cewa ke nan tun asali, shi ba waka yake yi ba, nazarin al’umma yake yi, ya buga ganga ne domin ya shaida wa al’ umma abin da yake yi, mai kyau ko maras kyau, ko ka yarda ko kada ka yarda. Ke nan da sata gaskiya ce, fadarta a waka ma gaskiya ce, nazarnta ma gaskiya ne! An ya kuwa ana tuba da fadar gaskiya? Ashe ramin gaskiya kurarre ne? Ana kuma tuba daga aikin adabi? Eeeeh aaaa’a.

Kila dai mu ce ana yin ritaya ko murabus ko ajiyewa domin magada su ci gaba daga inda aka tsaya ko kuma dai aikin adabi ya ki aikatuwa, ma’ana wakar ta kare, ko alkalamin ya bushe, ko hikimar ta buwaya, dole ta sa a bar fagen, ba don ana so ba.

To amma Gambo ya ce ya tuba, kila ma nan gaba a yi bikin kona ganguna da sauran kayan kida, ban sani ba. Shin me ya sa Gambo zai tuba, in tubar ya yi? Shin a tunaninsa wakar barayi laifi ce? shi ya sa ya tuba daga yin ta? Shin nazarin al’ummar da ya yi a baya ashe laifi ne ya dade yana yi wa Hausawa? Shin satar jiya ko ta gargajiya da ya fada a wakokinsa da kuma satar zamani da ya kitsa daga baya sun ware ne tsakanin Hausawa? Wa ya karu daga tubar Gambo? Ni dai ba zan iya sani ba, domin na dauka ba tuba ya yi ba, ga a in da yake fada:

 

Dud da ana yanke ni gobe,

Dud da ana halbe ni gobe,

Ba ni barin mugun kidan ga,

Don ba tuba nikai ba,

Sai in mutuwa tad dauki raina,

Ko in kuma Allah ya hukunta.

 

Jawabin kammalawa

Da alama Allah ne ya hukunta, Tun kafin Gambo ya mutu, ya bar waka bayan ya cika shekara 60 a doron kasa. Da yake kuma ba magaji ya bari da zai ci gaba daga inda ya tsaya ba, bari na kare wannan sharhi da irin tambayoyin da Gambo ya yi wa Nazaki da ya ce ya tuba da yin sata, kila mu gane inda gaskiya lamarin yake. Kodayake ban da murya irin ta Gambo, amma duk da haka,

 

kai, kai, a jinjina ganga!

Wai Gambo na son tambayarka,

In ka tuba da wakar sata duniyag ga,

Don ka tsira kiyama ka tuba Gambo,

Ko Don ka kama ibada kab barin ta?

Na ce in don ka tsira kiyama ka tuba Gambo,

To, gobe kiyama Indi za ka,

Ba wani sauki za ka ji ba,

Ka cika littafinka dauri,

Had bisa bainai an rubuta.

Shin Gambo ka tuba da waka ne Don gudun gaba,

To ka tuba yanzu ‘ya’yanka,

Ubansu mawakin nan na kwari,

Shi ne sunan babansu bar abada.

Gambo in ka zama babban malami, mai karatu,

Tun da ba ka zama sarkin Musulmi,

Gambo mai wakar nan ta kwari za a ce ma,

Ba walwale suna za ka yi ba.

Shin Gambo, ko ka tuba da waka ne

Don yau ba sata har barayi?

Ka sani kai fa Gambo, ka tuba, ka tube har Mahadi

Satar nan ba a barin ta

To ina amfanin tubar?

 

Wannan shi ne karshen wannan makala.

 


Advertisement
Click to comment

labarai