Connect with us

RAHOTANNI

Kwararru Na Kokarin Samar Da Ingantaccen Irin Shuka A Kasar Nan —Dakta Maji

Published

on


A kokarin da suke nyi na taimaka wa manufar wannan gwamnati na wadata kasa da abinci,tuni kwarru a fannin aikin gona suka dukufa wajen ganin an samu nasarar aiwatar da wannan kyakkyawar manufa ta gwamnati.

Dakta Maji Alhassan Iswako kwararre a fannin irin shuka daga ma’aikatar Afirkan Rice, yana kuma cikin wadanda suka gabatarda lacca a wajen taron karawa juna sani, wanda ake yi a Ciniyar binciken aikin gona da wayar da kan manoma da bayar da dabarun noma ta jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.

Taron wanda gwamnatin tarayya bisa hadin gwiwar African Debelopment Bank suka dauki dawainiyar gudanar da shim asana sun baje ilim yadda za samar da hanyoyin da za dinda samun ingantaccen iri shuga domin amfani mai kyau kuma mai yawa wanda zai sa manomi ya ci ribar sana’ar ta sa sosai.

Mahalarta taron sun fito ne daga jihohi guda bakwai wato, jihar Imo da Anambura da Enugu da Kebbi da Sakkwato da Kano da Neja da kuma Jigawa, wanda wadannan jihohin ke kan gaba wajen samar da sarrafa iri, shi ya sa ma a ke kiran wadannan jihohi da Crop Processing Zone.

Baya ga maganar bunkasa iri akwai kuma maganar samar da kayan more rayuwa ga al’ummar wannan kasa kamar, gyara yanayin noma,ko hanyoyi ko samar da ruwan shad a na noman rani ko gina ko gyara makarantun al’umma, kanmar firamare ko a ginawa manoma rumbunan da za dinda adana amfanin gonarsu da kuma taimakawa wajen harkar lafiya, ta hanayar samar da kananan asibitoci da gyara su.

Dakta Maji ya ci gaba da cewa, “a ma’aikatanmu ta African Rice, aikinmu shi ne na shinkafa, wannan training da muke yi shi ne batun gyara irin shinkafa, saboda muna ganin cewa manomi ya shiga gona ba iri ingantacce, to matsala ne,

Sannan akwai abu muhimmi da ke damun manomanmu na kasa, ba su da ingantaccen iri da za su shuka a gonakinsu, ya za mu yi mu gyara yanayin daga wurare da yawa wadanda suke da fada a ji daga aikin noma? Kamar su jami’o’i da cibiyoyin binciken aikin noma kamar su ADPsda makamantan su.

Haka kuma ma’aikatar kula da iri ta kasa  National Seed Council dukkansu ya kamata a ce an farfado da su, an inganta iliminsu game da irin shinkafa shi ya sa muna kasa-kasa mutane daga wuraren nan. Wannan shirin da muke yi yanzu mun gabatar da gayyatar mutane kamar hamsin daga wadannan gurare, wasu sun zo daga jami’o’i wasu sun zo daga ADPs wasu sun zo daga National Seed Concil wasu sun zo daga Seed Companies don kawai mu hada kai mu san yadda za mu inganta iri a kasar nan, shi .

Kuma fatan wannan nya zama kamar phase one ne, amma a phase two za a ce a bar wannan states da muke yanzu ko ko a’a mu inganta abin da muke yi a wannan states, a’a wasu states ne? Yanzun ba za mu iya fadi ba. Gasikiya abin da zai faru.

Dakta ya ce bisa hasashe za mu iyawadata kasar nan da abinci, amma ba mu kai matsayin ba. Duk abubuwa da gwamnati ke yi takan taimaka, akwai taimako ana yin gaba, amma kadan akwai wani muhimmin abu da ba su yi ba kuma sai sun inganta sun yi wannan abun, duk wuraren nan kasashen da ke kawo mana shinkafa a nan kasar ba sa neman su dogara da ruwan sama, sai da noman rani wannan gaskiya gwamnatin nan da na gaba da na baya ba su fahimci wannan ba, kuma ya kamata su fahimta.

Bari in gaya maka misali kamar Chana kamar Thailand wadanda suke kawo mana shinkafa ba sa dogara da ruwan sama, madatun ruwa suke amfani da su.

Haka Pakistan  Indonesia wuraren nan ba wanda ke dogara ga noman shinkafa a dogara ga ruwan sama, kuma wuraren nan yanzu suna bada karfi ga rijiya, ruwan rijiya a gona, ruwan rijiya ai ba ruwa ba ne, kudi manoma suke kashewa kuma zai maida amfanin da tsada ka gane ko? Gwamnati ya kamata su tashi tsaye a ga cewa ko wane waje da a iya noma shinkafa a samar masu ruwa.

Ai akwai hanyoyi da yawa, muna da irin ribers da yawa, wasu kanana wasu manya ko ba haka ba? Irin karamin dam za a iya yi, irin abin da ake kira head dikes za a iya yi, babban famfo wanda zai ba da ruwa arha ko ma manoman ne za su ba da kudi a sai mai zai fi masu arha yana rike famfo nasu, ka gane ko? An gyara yanayin noman an yi masu channels a samu babban famfo wanda za a sa, su wannan Companies ai famfo suke amfani da shi kuma suna cin riba kuma famfo suke amfani da shi ko ba haka ba ne, a ce a samu wani famfo wanda zai iya tallafa manoma kamar dubu a wani lokaci ko ma dari biyar, source na ruwan su daga waje guda inji guda ne, ai wannan zai iya yi na taba ganin wannan a gurare da yawa in ka je Nijer, Chad suna da wanu riber ana kiran shi Riber Tsari, kana tafe a bank na riber din za ka ga pumps din nan sun yi targeting communities ana ba su ruwa, su manoman famfo ya zama nasu su za su kiyaye da shi, ba yan sun girba za a karba za a karbi amfanin gona  daga kowa na kula da injin da mai, an yadda za a iya samun ruwa.

A karshe Dakta ya shawarci da su mayar da hankali ga noman rani in suna so a samu shinkafa a kasar nan. Ga manoma kuwa, Ga manoma su koyi noman zamani, su maida noma ciniki.

Jabiru Aliyu daga NAERLS na daga cikin wadanda suka halarci taron karawa junanin wanda kuma ya nuna amfanuwar da ya yi wanda ya ce zai taimaka masa da sauran al’ummar habaka noman shinkafa.

Haka kuma Muhammad Idi daga  National Agricultural Seeds ya ce wannan taro kamar ma su aka shiryawa domin suke ada alhakin tabbatar da ingantaccen iri ya shiga hannun manoma.

 


Advertisement
Click to comment

labarai