Connect with us

RAHOTANNI

Kungiyar KADA Ta Yi Sabbin Shugabanni

Published

on


A Lahadin da ta gabata ne aka rantsar da sabbin zababbun shugabannin kungiyar Karofi Debelopment Association da aka fi sani da KADA a takaice da ke Unguwar Karofi Keffi, Jihar Nasarawa, domin ci gaba da jan ragamar harkokin kungiyar.

Tun farko sa’ilin da yake jawabi a wajen taron, shugaban kwamitin zaben da aka gudanar Malam Adamu Salihu, ya bayyana cewa, kwamitin ya bi dukkan matakan da suka dace wajen gudanar da aikin da aka dora masa wanda a karshe mutum goma sha takwas daga jerin ‘yan takaran da suka nemi mukamai daban-daban ne suka yi nasara.

Da yake jawabin ban-kwana ga jama’a, shugaban kungiyar mai barin gado Malam Yahaya Labaran, ya shaida wa taron cewa an kafa kungiyar KADA ne sama da shekaru talatin da suka gabata da zummar hadin kai da cigaban yankin Karofi Keffi. Ya ci gaba da cewa, tun bayan kafuwar kungiyar zuwa yau sun samu nasarori da daman gaske wadanda jama’a suka amfana, ciki har da yin hanyar samun taransfoma na lantarki guda biyu don amfanin jam’ar Karofi da kewaye, samar da rumfar bugu ta zamani, gyara hanyoyi da samar da magudanan ruwa da dai sauransu masu yawan gaske.

Alhaji Shamsuddin Abubakar (Fakacin Keff) ne ya kasance babban bako a wajen taron. Da yake tofa albarkacin bakinsa yayin taron, ya nuna cewa abin alfahari ne da Allah ya albarkaci kasar nan da ‘yan kasa masu kishi. Tare da cewa shugabanci abu ne mai muhimmancin gaske a tsakanin  al’umma, don haka ya ce duk wanda Allah ya bai wa shugabanci sai ya rike amana yadda ya kamata.

Daga nan, Alhaji Shamauddin ya jaddada bukatar da ke akwai jama’a su kasance masu biyayya ga shugabanni gami da dokokin kasa. Sannan ya karasa da yi wa sabbin shugabannin KADA da aka rantsar fatan alheri, tare da yin kira ga sauran unguwannin garin Keffi da su yi koyi da KADA don cigaban al’umma.

Da yake jawabi a madadin sabbin shugabannin KADA, sabon shugaban kungiyar  Malam Nasara Abdullahi, ya nuna godiyarsu ga jama’ar Karofi da wannan dama da suka ba su na jagorancin al’amuransu. Tare da bayyana tsarin aikinsa a matsayin shugaban kungiya mai ci da ya hada yaki da sha da saida miyagun kwayoyi a yankin Karofi. Kazalika, ya yi kira ga ‘yan unguwa da su ba su cikakken hadin kan da suke bukata domin ba su damar iya sauke nauyin da ya rataya a kansu. Kana ya yi fatan mahalarta taron Allah ya maida kowa gidansa lafiya.

Tuni dai sabbin shugabannin suka sha rantsuwar saba layar kama aiki ta hannun Barista Hassan Usman. Sabbin shugabannin kungiyar dai sun hada da Nasara Abdullahi a matsayin shugaban kungiya, Yahaya Mika’ila a matsayin mataimakin shugaba na 1, sai Barista Nuhu Yusuf Yashi babban sakatare da Bala Muhammad Ango a matsayin ma’aji da dai sauransu.

Taron dai ya samu halartar jama’a da dama daga sassan Keffi, ciki har da jiga-jigan ‘yan siyasa da dai sauransu. Yayin da taron ya watse lami lafiya.

 


Advertisement
Click to comment

labarai