Connect with us

LABARAI

Jihar Kano Ta Yi Bankwana Da Cutar Polio – Dakta Muhammad

Published

on


Jihar Kano na bikin murnar cika watanni 45 ba tare samun rahoton bullar cutar polio ba a kananan Hukumomin Jihar 44, Babban Sakatare a Hukumar kula da lafiya a matakin farko na Jihar Kano Dakta  Muhammad  Nasir  Muhammad ne ya bayyana haka a lokacin Kaddamar da shirin allurar rigakafin cutar ta Polio na watan Aprilun shekarar 2018 a karamar Hukumar Wudil dake Jihar Kano.

Dakta  Muhammad  Nasir  Muhammad yace wannan nasara ta samu ne bisa jajircewar  masu ruwa da tsaki a cikin harkokin yaki da wannan mummunar cuta mai kassara kananan yara, saboda haka sai bayyana gamsuwarsa bisa aikin hadin guiwar da ake gudanarwa, musamman Gwamnmatin Jihar Kano, kungiyar ci gaba a duniya da kuma Masarautar Kano bisa samun wannan gagarumar Nasara wadda ya yi fatan dorewar ta.

Dakata Nasir Muhammad ya bukaci mata masu rainon ciki da su tabbatar da ziyartar cibiyoyin lafiya domin karbar alluran rigakafi tare da adana katunan alluran nasu. Hakazalika Dakta Muhammad ya hori  al’umma dasu yi kokarin kiwon lafiyarsu ga cutuka masu yaduwa  ta hanyar tabbatar tsaftar muhalli da abinci tare da kwanciya a wuraren da ke da wadatacciyar iska domin kaucewa kamuwa da cutar Sankarau. Yace haka zai tabbata ne idan aka tabbatar da tsafta yara  tare bude tagogi domin watayawar iska.

Mai Martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II na bayar da kyakkyawar kulawa wajen yaki da cutar ta Polio, inda sarkin ya bayar da umarnin ga dukkan Hakimai, Dagatai da masu unguwanni domin tabbatar da cewa ana kai yara wajen allurar rigakafin cutar Polio a kowane lokaci. Domin tabbatar da samun nasarar yaki da cutar ta Polio Sarkin Kano Malam Muhammad Sanusi II ya bayar da umarnin gabatar da rahoto daga dukkan hakiman Kano kan nasarar allurar polio  da kuma kididdgar yaran da aka Haifa da wadanda akayi brinsu domin samun tabbacin yadda za’a ci gaba tunkarar abubuwa.


Advertisement
Click to comment

labarai