Connect with us

RAHOTANNI

Iska Mai Karfi Ta Yi Ajalin Mutum Guda A Keffi

Published

on


Biyo bayan iska mai karfi sakamakon ruwan sama da aka samu a garin Keffi a Talatar makon jiya, hakan ya yi sanadiyyar rasuwar mutum guda tare da jikkata wasu bayan da iskar ta tumbuke wata katuwar bishiyar dorawa har jijiya inda bishiyar ta fadi a kan wani masallaci da ke karkashinta alhali da jama’a cikin masallacin suna fake ruwa.

Wannan al’amari mai cike da tashin hankali ya faru ne a yammacin wannan rana da misalin magrib a mararrabar Unguwar Karai da ke Unguwar Lambu Keffi, Jihar Nasarawa, inda Rabo Alhaji Shuaibu da aka fi sani da suna Baba Rabo ya rasa ransa.

Wadanda lamarin ya faru a kan idanunsu sun bada shaidar cewa, Baba Rabo tare da wasu mautane suna cikin wannan masallaci ne suna fake ruwa, ruwan da ya zo dauke da iska mai karfi. Ana haka ne sai aka ji fadiwar wannan bishiya ta dorawa a kan masallacin inda ta raba masallacin biyu tare da ragargaza shi.

Bayanai sun tabbatar da cewa bayan aukuwar ibtila’in, nan da nan jama’a suka hadu domin ceto wadanda lamarin ya rutsa da su a cikin masallacin. Daga bisani an samu fitar da mutanen cikin masallacin inda aka taras da Baba Rabo rai ya yi halinsa, sauran mutanen kuwa sun samu raunuka daban-daban.

Marigayi Baba Rabo mazaunin Unguwar Karai ne, magidanci ne har da ‘ya’ya, kuma ma’aikaci a jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi. Tuni dai aka yi jana’izarsa washegari Laraba kamar yadda addinin Islama ya tsara.


Advertisement
Click to comment

labarai