Connect with us

RAHOTANNI

An Fara Garkuwa Da Kananan Yara  A Giwa

Published

on


A ranar juma’ar da ta gabata ne wasu mutane wadanda ba a San ko su waye ba suka sungumi wani yaro mai suna Aminu Yakubu dan shekara 7 a wata unguwa Madara a cikin garin Giwa ta jihar Kaduna.

Alhaji Yakubu shi ne uban yaron wanda ya ce, “ Wallahi ba zan iya cewa komai ba sai dai addu’ar Allah ya bayyana min wannan yaron” amma wani bawan Allah abokin uban yaron da aka sace, wanda ya ce a sakaya sunansa amma shi ma cewa ya yi “Tabbas a ranar Juma’a ne da misalin karfe 4 zuwa 5ny, Aminu ya fito yana wasa a kofar gidansu da ke unguwar ta Madara.

Kafin magariba sai iyayen Aminu suka lura bai shigo gida ba, sai aka fara nemansa tare da sanarwa ga duk inda ake sa ran ganinsa, amma babu labarinsa har zuwa wannan lokaci da muke wannan magana babu wani labari amma yanzu babu abin da muke yi illa rokon Allah ya bayyana mana wannan yaron”.

Ya zuwa yanzu bincike ya muna cewa, masu garkuwa ne suka shigo garin na Giwa inda suka sami sa’ar yin garkuwa da shi Aminu da wani yaro amma wancen yaron da suka tambaye shi cewa ina babanka? Sai  ya ce musu “ Ai babana ya rasu” sai suka ce to mamanka fa? Sai ya ce “Ita ma ta mutu “ hakan ya sa suka sake shi amma sukaki  Aminu.

Majiyarmu ta shaida mana cewa, masu garkuwar har sun kira wayar yayan  Aminu tare da shaida masa cewa, sun yi garkuwa ne da Aminu har sai an ba su wasu miliyoyin kudi za su sako shi.

Wakilinmu tuntubi jami’an ‘yan sanda na garin Giwan don jin ko wane mataki  suka dauka a kan lamarin.

DPO mai kula da wannan karamar hukumar bai samu damar cewa komai ba saboda alokacin suna tattaunawa kan maganar tsaro karamar hukumar.

Su ma kungiyar tsaro na Cibil Defence sun ki yarda su ce uffan, saboda al’amarin na gaban magabatansu.

Dakta Yahaya Ibrahim shi ne kantomar karamar hukumar ta Giwa wanda ya bayyana  cewa, “A gaskiya ban ji dadin faruwar wannan lamari ba amma tuni na rubuta rahoto a kan lamarin na tura ga amma ina kira ga jama’ar karamar hukumata da su tashi tsaye wajan addu’a a kan wannan bala’i da ya shigo cikin kasa baki daya kuma za mu dauki duk matakan da suka dace wanda ba sai mun yada ba.

Saboda haka ina kira ga jama’a da su kula da yara tare da lura da duk wani bakon ido da ba a gane masa ba.


Advertisement
Click to comment

labarai