Connect with us

LABARAI

Zaben Fid Da Gwani: Ana Zargin Kakakin Majalisar Nasarawa Da Sace Akwati

Published

on


A shekaran jiya ne aka gudanar da zaben fitar da gwani na jam’iyyar APC saboda fuskantar zaben Kananan hukumomi da zai gudana a 26/5/2018 a Jihar Nasarawa. Zaben da ko kadan bai yi wa wasu ’ya’yan jam’iyyar ta APC dadi ba. An dai fara gabatar da zaben fid da gwani na Kansiloli ne, a ranar Asabar 7/4/2018 duk da cewa, ba ta sauya zane ba, abin da ya gudana a zaben Kansilolin shi ne ya gudana a zaben Shugabannin Kananan hukumomin.

Tun kafin a kai ga zuwa filin zaben aka rika bukatar wasu da su janye su bar wa wasu, saboda maslaha ta Jam’iyya. Inda wasu ke amincewa wasu kuma kan kauce wa wanan tayin, su ce a hadu a zaben fid da gwani.

Zaben fid da Gwani na Kananan hukumomi ya janyo tada jijiyar wuya hade da nuna yatsa har ma ta kai da zubar da jini.

A Karamar hukumar Nasarawan Eggon, an yi cacar baki tsakanin wani dan takara Hon. Muhammad Idiris da Mataimakin Kakakin Majalisar Dokoki na Jihar Nasarawa Hon. Godiya Akwaishiki. Lokacin da Hukumar zaben suka kammala kintsawa kafin fara zaben inda aka bukaci da a yi waje. Sai daya daga cikin ’yan takarar Hon. Muhammad Idiris ya ce lalai babu wanda za a bari cikin dakin zaben idan ba Malamin zabe ba, nan da nan kamar ya zuba wa Mukadashin Kakakin Majalisar wuta a jiki.  Nan take ya yi kansa da zafafan kalamai, inda yake cewa, ni ne na hudu a Jihar Nasarawa kuma ina cikin masu fada a ji cikin wanan jihar. Haka zalika ni mai kada zabe ne kuma ni ne mai kula da kuri’ar dan takara Hon. Kasimu Ali. Dan me za ka ce ni ma na fita? Da kyar aka shawo kansa.

Shi dai Mukaddashin Kakakin Majalisa Hon. Godiya Akwashiki yana kokarin dora Hon. Kasimu Ali ne kan wanan kujerar saboda da shi ma a tunaninsa zai yi masa aiki wajen bukatunsa na neman kujerar Gwamanan jihar.

A can Karamar hukumar Toto, inda nan ne mazaber Kakakin Majalisa Dokoki na Jihar Nasarawa Hon. Ibrahim Balarabe Abdullahi. Nan ne abin ya fi muni da ban mamaki, domin Wasan zubar da jini aka yi. Duk da cewa kafin zaben an yi ta kokarin sulhuta su domin a bar wa mutum daya, abin ya ci tura. Hakan ta sanya aka hadu a fagen daga. Ana tsaka da kidayar zaben ne sai wuri ya kaure da karar harbe-harben Bindiga, daga Jami’an tsaro. Nan take kowa kafarsa ta kwace shi. Wadanda al’amarin ya faru a gaban idonsu sun bayyana wanan aikin da Kakakin Majalisa Hon. Ibrahim Balarabe Abdullahi ya aikata ya zubar da mutuncinsa a idonsu.

Shi dai Kakakin Majalisar ana zarginsa ne da ingizo Jami’an tsaronsa da ke rufa masa baya zuwa wajen zaben domin yamutsa wajen da nufin kawo rudani a zaben fid da gwanin. Shedun gani da ido sun sheda cewa, a lokacinda ake tsaka da kada  kri’a ga ’yan takarar hudu, lokacin dan takarar da Kakakin Majalisa ya tsayar kuma yake Mara masa baya Audu Nuhu  tare da Yahaya Ahmad Baba suke kan gaba daga, bisani Zakari ya janye kuma ya bukaci magoya bayansa da su kada wa Yahaya Ahmad Baba kuri’unsu. Wanan damar ce ta sanya aka kara yi wa dan takarar da Kakakin Majalisar ke so tazara nesa ba kusa ba.

A lokacin da ake kidaya alkaluma sun bayyana tazarar da Yahaya Ahmad Baba ya yi wa abokan hamayyarsa. Kawai sai aka ga Jami’an tsaron da ke tafiya tare da Kakakin Majalisa sun bayyana a harabar wurin zabe da motocin gidan Kakakin Majalisar da yake aikin ofis da su. Isowarsu ke da wuya suka fara harbin kan mai Uwa da wabi.  Wanda abin ya faru a gabansu Malam Idiris Musa. Ya ce; zuwan Jami’an tsaron suka hargitsa wurin saboda sun samu tabbacin dan takarar da Kakakin Majalisa Hon.Ibrahim Balarabe Abdullahi ya tsai da ba zai ci zabe ba .

Shi ma Sakataren shirye-shirye na Jam’iyyar APC Abubakar Daura wanda yana cikin masu gudanar da zaben, ya ce; sakamakon harbe-harben da Jami’an tsaro suka yi ya yi sanadiyar raunata mutum biyu, inda yanzu haka suna Asibiti suna karbar magani daya na Gwagwalada daya na Toto.

Daya daga cikin wanda harin ya rutsa da shi Abdurashid Yahaya, ya ce; lokacin da Jami’an tsaron suka kutsa kai cikin dakin da kayan zaben suke sun yi ta kokarin su fitar da ni saboda su kwashe kayan zaben, na ki fita sai kawai na ji harbi, lokacin da na fadi sai suka rika kwashen akwaitin zaben suka tafi da shi.

Tun kafin zaben al’umman Karamar hukumar Toto sun yi tattaki dauke da kwalaye tun daga Toto zuwa Lafiya, inda suka gudanar da kokensu gaban uwar Jam’iyyar APC saboda kama-karya da Kakakin Majalisa Hon.Ibrahim Balarabe Abdullahi ke kokarin yi masu na zaben dole, inda ya kawo dan takara ya nada ya ce, shi ne za a zaba, saboda shi ne Gwamna da uwar Jam’iyyar APC ta Jihar Nasarawa ke bukata kuma jam’iyya ta amince da shi a matsayin dan takararta. Sai dai a lokacin uwar Jam’iyyar ta nisanta kanta da wannan zargin, inda Sakataren Jam’iyyar ta APC ya ce, wannan zargi ne kuma babu ruwan Jam’iyya, saboda jam’iyya tana tare da kowane dan takara ba ta da wani wanda ta ware ta ce shi ne dan takararta. Sai dai a tashi bangaren Kakakin Majalisar ya musanta zargin cewa, da hannunsa cikin sace akwati inda ya tura wa wani dan jarida a sakon kar-ta kwana ta wayar Salula.


Advertisement
Click to comment

labarai