Connect with us

LABARAI

Mun Kwace Bindigogi 83 Alburusai 702 A Hannun Jama’a A Bauci -’Yan Sanda

Published

on


Rundunar ‘yan sandan jihar Bauci, ta bayyana cewa, ta kwato bindigogi har guda tamanin da uku daga hannun jama’a wadanda suke rike da bindigogi a jihar ba bisa ka’ida ba. Haka kuma, rundunar ta bayyana cewa sama da alburushi dari bakwai da biyu ne suka kwato a hannun jama’a tun bayan da shugaban ‘yan sanda ya bayar da umurnin kowanei dan Nijeriya da ke rike da makami ba bisa ka’ida ba ya dawo da shi domin kiyaye fushin ‘yan sanda.

DSP Kamar Datti Abubakar Kakakin Rundunar ‘yan sandan jihar Bauci shi ne, ya shaida hakan wa manema labaru a jiya, yake cewa hakan na cikin matakin rundunarsu na kawarwa da kuma dakile bazuwar makamai ba bisa ka’ida ba a hannun jama’ar jihar. Ta bakinsa, “Idan ba ku mance ba, ko za ku tuna, a ranar 21/02/2018 ne shugaban ‘yan sandan Nijeriya Ibrahim K. Idris NPM, mni, ya bayar da wa’adin kwanaki (21) wanda yanzu haka aka kara kwanakin zuwa 30 ga watan Afrilun 2018 da cewar dukkanin wani ko wasu gungun jama’a da suke dauke ko suke rike da makamai, bindigogi ba bisa ka’ida ba su gaggauta kai wa rundunar ‘yan sanda mafi kusa da su,” Ya kara da cewa, Shugaban rundunar ‘yan sanda ya baiwa sashi-sashi da bangarori na ‘yan sanda da su tabbatar da amso makamai daga hannun jama’a kafin wannan ranar, har ma ya ce, IG din ya kafa sashi na musamman kan wannan fannin.

Datti ya bayyana cewa, a bisa haka ne, shugaban rundunar ‘yan sandan jihar wato CP Sanusi Lemu, ya kaddamar da sashin musamman da ya daura wa alhakin wanan gagarumar aikin. Ya ce, kawo yanzu sun samu nasarori, “Kawo yanzu, mun samu nasarar kwato bindigogi (83) da suke hannun jama’a wadanda dukkaninsu jama’a ke rike da su ba bisa ka’ida ba, sannan kuma mun samu nasarar kwato alburusai har guda dari bakwai da biyu (702) daga hannun jama’a kama daga wadanda muke zargin suna amfani da su wajen aikata munanan ayyuku da kum daidaikun jama’a,” In ji DSP.

DSP Kamar Datti, ya yi bayanin irin makaman da suka kama da cewar, Bindiga kirar AK47 guda 30, AK49 guda daya, ‘fabricated guns’ guda ashirin, ‘Single Barrel guns’ guda biyar, ‘Double guns’ guda biyu, ‘Pumps Action guns’ guda hudu, K2 guda daya, ‘Pistols’ guda ashirin, da kuma alburusai guda (702) masu rai, sai kuma ‘cartridges’ (70).


Advertisement
Click to comment

labarai