Connect with us

SIYASA

Matasan APC A Yobe Sun Jaddada Goyon Baya Ga Adamu Chillariye

Published

on


Matasan jam’iyyar APC a jihar Yobe sun jaddada goyon bayan su ga shugabancin Alhaji Adamu Chillariye- shugaban jam’iyyar APC, na riko a jihar Yobe.

Sun bayyana cewa lokaci yayi wanda ya kamata su fito fili domin bayyana matsayar su ga al’ummar jihar dama kasa baki daya dangane da gudumawar da ya bayar wajen ciyar da APC a gaba.

Bugu da kari kuma, sun yi kira ga gwamnatin jihar da cewa wannan shi ne ra’ayin mafi yawan matasan jihar Yobe. Sun kuma bukaci da a tabbatar wa Alhaji Adamu Chillariyen shugabancin jam’iyyar bisa ga cancanta da kwarewar da yake da ita wajen hada kan yan jam’iyyar daga kowanne bangaren al’ummar jihar.

Babban sakataren gmayyar kungiyar matasan jam’iyyar APC a Zone-B (APC Youth Banguard), Kwamared Arma-Ya’u Sulyman ne ya shaida hakan, a cikin zantawar sa da wakilin mu a jihar Yobe. Wanda ya kara da nuna cewar, a halin da ake ciki yanzu, kan yayan APC a hade yake wuri guda, ta dalilin dattakon shugaban jam’iyyar.

Ya ce, jam’iyyar APC a Yobe itace jam’iyyar mafi rinjaye, tun tana APP (1999), har ta koma ANPP (2003/07); wanda kuma daga bisani a 2015 ta rikide zuwa APC- inda ta samu babbar nasara a babban zabe tare da Kafa gwamnatin tsakiya da a jihar Yobe. Kuma tun daga wancan lokacin, jam’iyyar PDP ce ke rike da matsayin jam’iyyar adawa a jihar, wadda kuma take da karfi a kudancin jihar.

Sakataren ya ce, kuma babban dalilin da yasa a can baya PDP tayi karfi a kudancin Yobe shi ne, yanki ne wanda kabilanci ke taka rawa a fagen siyasa, wanda ya kunshi kananan hukumomi 4- Potiskum, Nangere, Fika da Fune. Lamarin da ya jawo duk wanda ya samu dama a jam’iyya mai ci jihar; daga cikin wadannan kabilun, sai ya fifita kabilar sa. Yayin da su kuma sauran al’ummun da aka nuna musu wariya wajen cin moriya da samun alfarman Gwamnatin jihar, sai su koma jam’iyyar adawa koda ba ason ransu ba.

Ya ce, amma daga baya, a lokacin da dan kudancin jihar Yobe ya kasance shugaban jam’iyyar APC na jiha, wanda ya fahimci matsalar da ke kawo cikas, sai ya dauki matakin gyara a cikin jam’iyyar. Kuma shi kanshi Gwamna Alhaji Ibrahim Gaidam, ya san da wannan matsalar, kuma ya damka wannan amana ta sake hada kan yan jam’iyyar APC ka Alhaji Adamu Chillariye. Matakin da ya bashi damar bube kofa ga sauran kabilun domin su shigo gwamnati a dama dasu.

“Kuma sanin kowa ne kan cewa, zuwan Alhaji Adamu Chillariye a matsayin shugaban jam’iyyar APC ne yayi kokrin baiwa kowwace kabila a jihar Yobe gurbin taka muhimmiyar rawa wajen cimma muradu tare da raba mukaman jam’iyyar daidai-wadaida, ba tare da nuna mambanci ba a APC, kuma hakan ne yasa sauran kabilun da suke adawa da gwamnatin jihar suka sauya sheka daga Jam’iyyar adawa ta PDP zuwa jam’iyyar APC mai mulki.”

“Dadin-dadawa kuma, Adamu Chillariye yayi kokari wajen kawo hadin kai a tsakanin kowa da kowa a jihar Yobe, al’amarin da ya samo asali dangane da yadda yake gudanar da shugabancin jam’iyyar APC cikin yanci tare da jan kowanne bangare a jiki, domin a gudu tare a tsira tare”. Inji Arma-Ya’u.

A hannu guda kuma ya ce, saboda hakan yanzu jam’iyyar APC Yobe ta samu rinjaye wanda bata taba samun irin sa ba a tarihin siyasar jihar, a baya jam’iyya mai mulki tana da karfin fada a ji kawai a gabashi da arewacin jihar, amma yanzu ta baza tafin ta kudancin jihar, wanda ya dade a karkashin ikon jam’iyyar adawa ta PDP, kuma wannan nasara tana da nasaba da kyakkyawan jagorancin Adamu Chillariye. Wanda yanzu babu wata jam’iyyar mai wani katabus idan ba APC ba, an zama abu daya, babu wariya babu kabilanci.

Ya ce, wata shaida a kan hakan ita ce a satin da ya gabata shugaban jam’iyyar APC, Alhaji Adamu ya karbi magoya bayan PDP kimanin 7000 a kudancin jihar. Kafin haka, a kwanan baya APC ta karbi wani ayari daga jam’iyyar PDP; irin wannan karbar yayan jam’iyyar adawa ya faru sama aji 10 a wannan shiyya ta ‘B’, kuma yanzu haka akwai shirin karban sama da magoya bayan PDP kimanin 10,000, ai banza ba ta kai zomo kasuwa.

“kuma wadannan nasarori da Alhaji Adamu Chillariye yake samu suna zuwa ne ta dalilin cikakken goyon bayan da yake samu daga gwamnan jihar Yobe, Alhaji Ibrahim Gaidam, domin burin da Gwamna yake dashi shi ne yana so ne a dama da kowanne yanki da kowacce kabila a sha’anin tafiyar siyasa da mulkin Yobe. Gaidam baya so abar wata wani bangare ko wata kabila a baya, kuma shi ne ya sanya kullum yake yaba wa da kokarin Adamu Chillariye akan irin hallaci da dattako wajen hada kan al’ummu daban-daban a wannan jiha tamu ta Yobe”. Ya nanata.

Ya ce, kuma babban dalilin mu na ci gaba da goyon bayan shugabancin Alhaji Adamu Chillariye, shi ne shi ma gwamnan jihar Yobe yana alfahari da shi saboda kasancewar sa mutum mai rikon amana, gaskiya, da zuciya daya ( bashi da rufa-rufa akan Gaskiya), kuma ba mutum ne mai shirya karya ko girman kai ba, sannan ba a taba tuhumar sa da fachaka da kudin jam’iyya ko wata munakisa ba. Ya ce, shugabancin jam’iyyar APC a karkashin Adamu Chillariye, jam’iyyar APC ta tara kudin da zata iya tunkarar zaben 2019 a jihar Yobe ba tare da gwamnatin jihar ko wani dan takara ya agaza mata sisin kwabo ba.

“Kuma kwazo da himmar Adamu Chillariye, shi ne yasa mu matasa a kudancin jihar Yobe muka ga ya dace ya zarce, saboda zarcewar shi yana da matukar mahimmanci, saboda kasancewar shi ne ake da tabbacin zai rike amanar yan jam’iyyar APC baki daya tare da ta Gwamna Ibrahim Gaidam, kuma a wannan gabar, inda zaben 2019 ke karatowa, muna tsoron a kawo mutumin da ba a san kwarewar shi ba- wanda kila ya hada kai da yan siyasa Abuja, su kai al’ummar jihar Yobe su baro”.


Advertisement
Click to comment

labarai