Connect with us

LABARAI

Masu Cin Gajiyar Shirin N-Power A Gombe Sun Mayarwa Sanata Goje Martani

Published

on


A makon jiya ne Sanata mai wakiltar Gombe ta tsakiya a majalisar Dattawan Najeriya Sanata Muhammad Danjuma Goje, ya yi barin zance na cewa jihar Gombe ba ta amfana da shirin nan na N-Power da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bullo da shi.

Jama’ar da suke cin gajiyar wannan shiri na N-Power da kuma shirin nan na ciyar da Yaran Firamare abinci da suke amfana da shirin a Gombe sun taro a dakin taro na cibiyar ilimi na ETF dake Gombe inda suka yi Allah wadai da kalaman Sanata Danjuma Goje, na cewa a soke wanann shirin tunda al’ummar Gombe ba sa amfana da shirin.

Wata mata mai suna Abegail Damfani daga yankin karamar hukumar Akko inda Sanatan ya fito ta bayyana cewa basu ji dadin wannan kalamai na sanata Goje ba domin su wannan shiri na N-Power yana taimaka musu saboda da basa aikin komai yanzu sun sami aikin da yake taimaka musu wajen biyan wasu kananan bukatun su da kuma biyan kudin makarantar ‘ya’yan su.

Abigail Damfani, tace kokarin da Matasan suke yi wajen koyar da Yara a Makaranta yasa har ana kwatanta makarantun gwamnati dana kudi a jihar saboda yanayin koyarwar ya canja.

Tace da ba dan an samu ingancin koyarwa na N-Power ba da harkar ilimi ya kara lalacewa a jihar kuma idan harkar ta lalace ba yadda za’ayi a samu ci gaban da yanzu ake gani.

Tayi amfani da wannan damar wajen godewa shugaban kasa Muhammadu Buhari na bullo da shirin na N-Power domin shirin ya taimakawa mutane.

Wata Mata daga yankin Yamaltu Deba Malama Lami Adamu, tace duk watan duniya suna amfana da tallafin naira dubu biyar biyar da ake basu daga shirin conditional grant wanda shi ma yana karkashin shirin N-Power ne.

Malama Lami Adamu, tace ba gaskiya bane wani mutum yazo yace ba’a biyan su kuma duk girman sa bai fadi gaskiya ba domin sukan suna amfana amma idan wani yazo ne dan ya hana wannan shirin ya gudana to Allah ya musu maganin sa.

Shi ma Abubakar Peto Dukku, daga Yankin Dukku cewa ya yi shi ma yana amfana da wannan shirin kuma dari bisa dari suna bayan shugaban kasa Baba Buhari na irin wannan shirin da ya bullo dashi mutane suke amfana.

Abubakar Peto Dukku, ya kuma ce duk wanda yake fade-fade kan a tsayar da wannan shirin saboda a cewar sa jihar da yake wakilta ba ta amfana ba gaskiya bane.

A jihar Gombe sama da mutane dubu biyu da dari biyu da bakwai ne suke cikin gajiyar wannan shiri na koyarwa na N-Power sannan kuma yanzu akwai fiye da dubu uku da suke cin gajiyar shirin ciyar da Yaran Firamare a jihar.


Advertisement
Click to comment

labarai