Connect with us

LABARAI

Masari Ya Bukaci Akantocin Kasar Nan Da Su Rika Fallasa Barayin Gwamnati

Published

on


Gwamnan jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari ya bukaci Akwantocin (Accountants) a kasar nan da suke tona asirin manyan jami’an gwamnati da su ke sama da fadi da kudaden gwamnati a fadin a ma’aikatu, hukumomin hade kuma da sashi-sashi na gwamnati domin dakile yawaitar handamar dukiyar kasa haka siddan.

Aminu Masari ya yi wannan kirar ne a Talatar nan yayin da shugaban kungiyar Akwatoci (National President, Association of Accountants of Nigeria (ANAN) na kasa Alhaji Shehu Ladan ya ziyarce shi a ofishinsa da ke Katsina.

Gwamnan ya yi bayanin cewa dukkanin wani babba da ke cikin harkar gwamnati baya iya sanya hanu a kan dukiyar jama’a ba tare da sanin Accountant ba, don haka ne ya ce Akwantoci suna da gagarumar rawar takawa wajen rage dumbular dukiyar jama’an kasa ta barauniyar hanya.

Alhaji Bello Masari ya ce gina kasa gami da samar da ci gaba ba ya taba samuwa ba tare da kowa ya bayar da tasa gudunmawa a fanninsa ba.

Tun da fari ma, shugaban kungiyar Akwantoci ta Nijeriya ANAN, Alhaji Shehu Usman Ladan ya bayyana cewar makasudin zuwar tasu jihar Katsina shine domin ci gaba da shirin habaka aiyukansu kashi na biyu na wannan shekara mai taken (MCPD).

Ya kuma bayyana cewar a yayin taron kuma za su horar da sabbin ‘ya’yan kungiyar kan sanin makamar aiki domin kyalliya take biyan kudin sabulunta.

Ya bayyana cewar matakin zai taimama musu gaya wajen inganta aiyukansu a kowani bigire a fadin kasar nan.


Advertisement
Click to comment

labarai