Connect with us

LABARAI

Magudin Jarrabawa Ne Ke Kassara Harkar Bincike Da Karatu A Dakunan Karatun Nijeriya -Bichi

Published

on


An bayyana cewa Babban Kalubalen da ke fuskantar Dakunan Karatu a Kasar nan shi ne, karancin ziyaratar dakunan karatun dan Karatu da sauran bincike, Wanda kuma magudin Jarrabawa ko satar amsa a lokacin Jarrabawa shi ne ya kawo wannan matsala kuma babban kalubale a wannan harka ta gabatar da dakunan karatu a wannan lokaci. Wannan bayanin ya fito ne daga bakin Malam Ibrahim Ahmed Bici kwararre a wannan harka ta dakunan karatu wanda kuma shi ne farkon wanda ya shugabanci dakin karatu na cibiyar Nazari da bincike ta Dimukuradiyya da ke Gidan Mubayya wacce ke karkashin Jami’ar Bayero ta Kano. Kuma shugaban Hukumar Dakin Karatu na Murtala Muhammad da ke Kano a halin yanzu a lokacin wata zantawa da wakilin mu a Ofishinsa da ke Murtala Muhammad ‘Library’.

Haka kuma Bici ya ce, ba wata gudunmawa da za ka ba dakin karatu kamar a ce ana ziyartar shi ana karatu da bincike a cikinsa, wanda idan ka yi haka to ka ba da babbar gudunmawa wajen farfado da kima da darajar dakin karatu, a cewar Bici. Haka kuma ya kara da cewa idan ana bin ka’ida irin ta da wajen cewa ba za ka ci ko wacce irin Jarrabawa ba sai ka yi karatu kamar yadda ake yi a da can baya, ta hanyar cewa ko kai dan waye ko waye komai matsayinsa ba zai ci jarabawa ba sai ya san abin haka kuma ba za a dauke ka aiki ba ko dan waye ko daga ina ka fito sai ka san abin, to wannan shi ne ya sa harkar karatu da bincike ta fi yawa a dakunan karatun mu na can baya. Ya ce amma yanzu abin takaici, saboda da magudin jarrabawa da ake yi da kuma karancin tarbiya da rashin sanin ya kamata, shi ne ya sa magudin jarrabawa ya yi yawa, ya sa za ka ga wanda bai san abu ba sai a ce ya ci jarrabawa, haka kuma wanda bai san aiki ba sai a dauke shi. To wadannan duk wasu matsaloli ne da suka kawo karancin masu zuwa dakunan karatu, mu dai a nan Kano haka kuma abin yake a sauaran wurare, dan haka sai an gyara ta hanyar dawo da dabi’ar karatu.

Dangane da maganar harkar Dakin karatu na Murtala Muahmmad da ke Kano kuwa ya ce, a yanzu haka akwai tarin Littattafai masu yawa, a fannoni daban-daban na matakan karatu daban-daban na Karatu, tun daga kan na masu karatu a Jami’o’i Kwalejoji, matakan Sakandare da Firamare har ma da sashin kanan Yara da ba su shiga Makaranta ba, da ma sashin na Yaran da ke Nozari, wato Makarantun Rainon Yara wanda kuma duk wurare ne da aka kayata su, ta yadda masu karatu a kowanne mataki za su yi sha’awar zuwa. Ga kuma sashin Dakin Karatu na zamani wanda ake amfani da Na’urorin zamani, wanda aka fi sani da E. Library, dan haka yana da kyau kowa ya ba da gudun mawarsa wajen ziyartar dakunan karatu domin karatu da bincike wanda dan haka aka samar da irin wadannan wurare a ko’ina suke.

Haka kuma kowa ya sani cewa Gwamnatin Kano karkashin Dakta Abdullahi Umar Ganduje ta yi kokari wajen inganta dakunan karatu kuma tana yin kokari a yanzu, wanda yanzu haka ana kokarin kawata dakin karatun na Kano fiye da yadda yake a yanzu ta yadda su ma na Nakasassu masu bukata ta musamman za a saukaka musu wajen zuwa yin karatun fiye da yadda abin yake, kuma akwai tsare-tsare da shirye-shirye na fadakar da al’umma ta yadda iyaye za su rika kawo ’Ya’yansu a lokacin hutu domin karatu daidai da yadda bukatarsu take, dama sauran dalibai na Makarantu, wanda kuma ake da burin sabanta abin ta yadda zai zama abin sha’awa ga masu zuwan fiye da yadda yake a yanzu, wanda kuma wannan shi ne burinsu wanda kuma suke samun goyan bayan Gwamnagtin Kano.

Malam Ibrahim Ahmad Bici, wanda aka haife shi a Garin Bici, a shekarar 1960 kuma ya kama aiki a 1992 bayan ya kammala Digirin sa a wannan Fanni da ya karanta a Jami’ar Bayero. Ya ce, harkar E. Library ba ya da wata matsala kuma ya ma fi sauki da inganci duk da rashin wadatacciyar wutar lartarki. Ya ce, hakan ba za ya kawo cikas a dakunan karatu na zamani ba, illa dai iyaka al’umma ta ba da gudun mawarta wajen ziyartar dakunan karatu.

Shirin Kiwon Lafiyar Mata Da Yara Na Kungiyar Fahimta Da  Bilgate Ya Kankama A Bauchi

Shirin inganta lafiyar mata da kananan yara na kungiyar FAHIMTA  da gidauniyar Bill-gate wanda ya fara aiki a Jihohin  Kano  da Kaduna da Legas da Neja da Bauchi wanda ke samun tallafin gwamnatin tarayya da gidauniyar Bill-gate ya samu kankama a Jihar Bauchi inda aka fara ziyartar yankunan karkara domin duba irin halin da lafiyar mata da kananan yara ke ciki da kuma yadda za tallafa musu wajen samun ingancin kiwon lafiya.

Shugabar shirin a Jihar Bauchi Hajiya Maryam Garba ita ne ta bayyana haka cikin hirar ta da manema labarai a Bauchi inda ta bayyana cewa aiki ne na shekara biyar da DRP wato (Debebelopment Research Programmed) mai samun tallafin gidauniyar  bill -gate  domin lura da yadda ake  yin alluran rigakafin lura da lafiyar mata da yara da suka shafi zazzabin nimoniya da sauran cututtuka domin ganin an samu ingantaccen kiwon lafiya a jihohin.

Maryam Garba ta bayyana cewa a matsayin ta na jagorar wannan aiki a Jihar Bauchi,  don haka suke bukatar gwamnatin Jihar Bauchi ta taimaka a bangaren aikin kiwon lafiya saboda Jihar Bauchi ta yi fice wajen tallafawa harkokin kiwon lafiya kuma ta zo ta farko kan wannan aiki don haka take son a tabbatar wannan tafiya ta dore ya kasance an samar da doka daga majalisa kan kiwon lafiya  a hukumance don kar a je a dawo ko da ace gwamnati mai ci ta tafi ya zamanto an samu dorewar aikin  kan yadda aka tsaya, ba tare da idan wata gwamnati ta zo nan gaba ta nemi fito da sabon tsari  ba, ya kasance duk wanda zai  zo ya gina a kan yadda aka tsaya.

Don haka Hajiya Maryam Garba ta ja hankalin mutanen Jihar Bauchi da kar su yi wasa da kiwon lafiya da rigakafin mata da kananan yara su je asibiti da zarar sun ji wani sauyi a lafiyar su, haka kuma mata masu juna biyu su rika halartan asibiti a kan lokaci don yin awun ciki da zarar an kai watannin fara awu. Ta gargadi  masu wasa da yin alluran rigakafi  musamman wadanda basa son karbar alluran Polio sai an tsaya da jami’an tsaro su  bar wannan al’ada su fito da yaran su don karbar alluran rigakafi na kowadanne cututtuka. Don haka ta bukaci su tsaya kai tsaye a yi aikin da ya dace wajen ci gaban jama’ar Jihar Bauchi ta yadda mutane za su  kare lafiyar su da ta iyalan su.

Saboda haka Maryam Garba ta bayyana cewa yanzu wannan shiri ya fara shiga yankunan karkara don tsara yadda za a lura da lafiya ba tare da samun cikas ba, don haka ya kamata mutane su bayar da goyon bayan da ya dace wa gwamnati don a samu ingancin kiwon lafiya. Kuma ya kamata al’adar jinkiri game da lura da lafiya da mazauna yankunan karkara ke yi a tabbatar an daina ta hanyar sanar da gwamnati bullar duk wata cuta da ba a gane kan tab a cikin lokaci don hukumomin lafiya su dauki mataki nan take.


Advertisement
Click to comment

labarai