Connect with us

LABARAI

Kafa Na’urorin CCTV A Tashoshin Jiragen Saman Legas Da Abuja Aikin Ya Kai Kashi 90 – FAAN

Published

on


Aikin da ke gudana na kafa na’urorin hangen nesa na CCTV, a wasu wurare na musamman a tashar saukan Jiragen sama ta Murtala Muhammad (MMIA), da Legas, da kuma ta Nnamdi Azikwe (NAIA), da ke Abuja, aikin ya kai mikidarin kashi 85 zuwa 90 na kammaluwa, hukumar kula da tashoshin saukan Jiragen saman ce, (FAAN), ta shaida hakan.

Babban manajan hukumar ta FAAN, Uwargida Henrietta Yakubu, ta ce, wannan shi ne zai zamo karo na farko da aka gudanar da wani babban aiki na tsaro a tashoshin saukan Jiragen saman, sakamakon matsalar tsaron da aka rika samu a baya.

A wata tattaunawa da ta yi da manema labarai, ta ce, hukumar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da inganta tsaron masu amfani da tashoshin Jiragen a dukkanin kasarnan.

Ta ce, bayan an sanya su a kashi na farko, hukumar ta FAAN, za ta kuma isa tashoshin Jiragen saman na, Kano, Fatakwal da kuma Enugu a kashi na biyu.

Ta kara da cewa, hukumar ta horar da jami’an tsaron ta yanda za su yi amfani da na’urorin, ta bayar da tabbacin inganta tsaro a dukkanin tashoshin sauka da tashin Jiragen na kasarnan, ta hanyar yin amfani da sabbin na’urorin

Kan taron ACI da ke tafe, Yakubu, ta ce, Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ne zai bude taron, ta ce taron na yankin yammacin Afrika, zai kasance wata dama ce da masu zuba jari na gida da waje, za su samu a sashen na Jiragen sama.


Advertisement
Click to comment

labarai