Connect with us

TATTAUNAWA

Jan ’Yan Kasuwa A Jiki Ne Silar Nasarar Da Mu Ka Samu -Yusif Abba

Published

on


Alhaji Yusif Abba Kasm shi ne Kwanturolan Hukumar Kwastan Mai kula da Jihohin Kano da Jigawa, a tattaunawarsa da Jaridar Leadership A yau, Yusif Abba ya bayyana dalilan samu nasarar sa a cikin shekara guda da doriya da zuwansa Kano, sannan kuma ya bayyana farin cikinsa bisa yadda jami’an hukumar ke bashi goyon baya har ta kais u ga samun nasarar da Hukumar Kwastan ke alfahari da ita. Ga dai yadda tattaunawar ta Kasance.

Za muso ka  gabatarwa da Jama’a kanka da kanka?

Alhamdullahi ni sunana Yusif Abba Kasim kuma a halin yanzu ni ne Kwaturola mai kula da Jihohin Kano da Jigawa, kuma shelkwatar mu na nan Titin Bompai a Jihar Kano.

A baya wasu na kallon hukumar Kwastan a matsayin wata hukuma dake zaman barazana ga harkokin Kasuwanci, shin me ya kamata jama’a su  fahimta dangane da ayyukan wannan Hukuma?

Kamar yadda aka sani ita Hukumar Kwastan guda cikin muhimman ayyukan da aka rataya alhakinsu akan ta shi ne  habaka Kasuwanci, saboda haka Hukumar Kwastan bata wata barazana ga harkokin Kasuwanci, aikin ta shi ne habaka Kasuwanci tare da tattarawa Gwamnati Kudaden shiga na kayayyakin da aka shigo  da su, sai kuma tabbatar da cewa ba’a shigo da kayan da doka ta haramta shigo da su ko fitar da suba. Wadanan su ne ayyukan da aka dorawa wannan Hukuma.

Ranka ya da dade a yiwa jama’a gwari gwari kan ire iren kayayyakin da hukuma ta hana shigo da su ta wasu iyakokin Kasar nan?

Haka ne, kayayyakin da Gwamnatin tarayya ta hana shigo da su ba wai Hukumar Kwastan ce ta hana shigo da su ba, doka ce ta Gwamnatin Tarayya. Mu Hukumar Kwastan aikin mu shi ne tabbatar da ganin ana bin

doka da oda, Haka kuma ka ma kayayyakin da aka hana shigo da su wanda kuma lokaci zuwa lokaci gwamnati kan yi gyara akan wasu kayan da aka hana shigo da wasu, ya yinda kuma za a amince da shigo da wasu.

A halin yanzu Muhimman  wadanda za mu ce an hana shigo da su ta kan iyakokin mu na nan,  wanda kuma ta nan muka fahimci mutanen mu sun fi amfani da su wajen shigo da kaya,  wanda suka hada da Shinkafa irin ta

kasashen waje, Man Girki, Kayan Gwanjo da Motoci Takumbo da maganin Sauro irin igiyar leko da Taliyali, Makaroni irin ta waje din nan wanda aka hana shigo da su, ta wadannan muhimman iyakokin namu kamar yadda na fada  na Kano da Jigawa sai ta tashoshin jiragen ruwa.

A shekarun da suka gabata an sha jin yadda ake ta da jijiyar wuya tsakanin hukumar Kwastan da ‘yan Kasuwa, musamman kan korafin da ‘yan Kasuwa ke yi cewar ana tare su bayan sun yi sayayya acikin Kasuwanni, shin ina wannan batu ya kwana?

Abin da yake faruwa shi ne muna kokarin wayar da kan jama’a musamman ‘yan Kasuwa cewa dokar data tanadi kafa wannan Hukuma ta Kwastan ta bada damar shiga ko ina domin kama kayan, bawai ya saba doka ba ne, wannan aikin wayar da kan Jama’ar shi ne muke ganin ya shiga kan ‘yan Kasuwar, domin suna fahimtar muna  da damar shiga ko ina domin kama kayan, saboda haka ba zasu ce a daina kama a bubuwan da aka tabbatar da rashin sahihancin yadda aka shigo da su cikin kasa ba.

Fahimtar hakan da ‘yan Kasuwa suka yi ya sa sun rage wannan bakar ta’ada ta faskaurin, wanda kuma ana yin wannan kokarin ne domin a rage fasakauri, mai yiwuwa an samu raguwar al’amari hakan tasa abubuwan su kai sauki.

Zuwan ka wannan hukuma cikin shekara daya da doriya an samu fahimtar juna tsakanin ‘yan Kasuwa da jamai’an hukumar da kake shugabanta a Kano da Jigawa, ko mene sirrin wannan fahimtar juna?

Alhamdulillahi Nasarorin da aka samu akwai batun jawo su a jika da muke  tare da da nuna masu mu abokan su ne na habaka Kasuwanci, muna nuna masu yadda zasu bi doka da oda kan maganar harkokin shigo da kayayyaki, wannan ta sa muke shiga kafafen yada Labarai muna gabatar da shirye shiryen wayar da kan ‘yan Kasuwar yadda zasu ci gaba da gudanar da harkokin shiga da fitar da kayayyaki, wannan ya taimaka

kwarai da gaske.

Kwanakin baya an samu tashin tashina tsakanin jami’anka da al’ummar wani gari da ke kusa da iyakar Jigawa da Nijar wanda har takai ga lalata abubuwan hawan jami’an hukumar ta ka, shin an shawo kan wannan matsala?

Alhamdulillahi wannan matsala tuni an shawo kanta kuma hankali ya kwanta an ci gaba da gudanar da harkokin yau da kullum kamar yadda aka saba tsakanin ma’aikatanmu da jama’ar wannan gari, Kamar yadda ka sa ni ne aduk lokacin da kuke kokarin hana wata barna zaka tarar da wasu mutanen basa son hana wannan al’amarin. Saboda haka dole a wasu lokuta a dinga samun dan tashin tashina anan da can.

A lokacin an dan samu wani kuskuren harbi da ya faru wanda hakan ya yi sanadiyyar rasa ran wani mutun guda daga cikin mutanen garin, wanda shi ne ummul haba’isan faruwar wancan al’amarin. Amma alhamdulillahi hankali ya kwanta mun ziyarci iyalan mamacin da shugaban karamar hukumar mun zauna an tattauna an kuma warware matsala komai ya koma kamar yadda aka  san shi a baya.

Shin zuwa yanzu ayyukan da kuka sa gaba a iya cewa kwalliya na biyan kudin Sabulu?

Alhamdulillahi gaskiya Kwalliya ta biya kudin sabulu, ba don komai ba lokacin da na zo na tarar ana tattarawa Gwamnatin Tarayya abin da bai kai naira Biliyon guda ba a wata guda, amma zuwana  mun tara abin da ya haura Naira Biliyon guda a kowane wata, wanda a shekarar data gabata mun tattarawa Gwamnatin Tarayya abin da ya Haura Naira Biliyon 13.

Haka kuma daga farkon wannan shekara da muke ciki, kowane wata muna samun sama da Naira Biliyon 1.2. saboda haka a kashin farko na wannan shekara mun tara sama da Naira Biliyon uku da doriya.

Sannan kuma mun samu nasarar kame kayan da aka kiyasta kudin fitonsu ya kai Naira Miliyon 300, haka ma wanann shekarar da muke ciki mun samu nasarar kama kayayykin da idan da biya mu su harajin za a yi da abin da za abiya zai haura Naira Miliyon 170. Saboda haka zamu iya cewa Kwalliya ta biya kudin Sabulu.

Kamar yadda na fada maka cewar mun tattara harajin da ya haura sama da abin da Gwamnatin tarayyya ta dora  mana alhakin tattarawa, saboda har rara muka samarwa Gwamnati

Kasancewar ‘yan Kasuwar mu na da karancin wayewa ta fuskar sabon ci gaban da duniya ke kai a yanzu, shin kowacce rawa kuke takawa wajen ganin ‘yan Kasuwar sun ci gaba da amfana  da sabon tsarin da duniya ke kai?

Gaskiya ne muna da wannan tsari kuma ‘yan Kasuwar na karbar wannan tsari yadda ya kamata, kullum ana ci gaba da wayar da kan ‘yan Kasuwar kamar yadda a halin yanzu ma a zamance ake gudanar da tsarin sauke

kaya a  tashoshin jiragen ruwa dake Legas ana kawo su nan Kano, kamar irin motaci da kwantena kwantenar kayayyaki duk ana sauke su, kuma ana gudanar da harkokin ne ta yanar gizo.

Dokar hana shigo da wasu kayayyaki na cikin dokokinku da ke tayar da hankalin mai karamin karfin, shin  mene sirrin hana shigo da shinkafa ne?

Kamar yadda na fara fada gwamnati ce ke samar da doka, bayanan da muka samu shi ne Gwamnati ta hana shigo da shinkafa ta kan iyakokin kasa bata hanyar tashar jiragen ruwa ba.  Kuma dalilinta shi ne tana son

bunkasa harkar Noma domin samar da shinkafa acikin gida Najeriya, domin akan wadancan iyakoki babu isassun na’urorin da za ayi amfani da su wajen tantance ingancin kayan da ake son shigo dashi. Sabanin ta

tashoshin jiragen ruwa za a samu isassun kayan aiki a wurin.

Yi wa mai karatu dalla dalla irin Nasarrorin da ka cimma zuwan ka wannan hukuma reshen Kano da Jigawa?

Babbar nasarar da aka samu itace duba abin da da aka samu sannan kuma a duba shin abin da aka samu mun aiwatar dashi yadda ya kamata, kuma Alhamdulillahi an tabbatar da samun nasarar abin da aka dora mana aiwatarwa, gwamnatin tarayya a shekarar data gabata cewa tayi mu tara Naira Biliyon goma, kuma cikin ikon Allah da jajircewar mu muka samu nasarar tara sama da Naira biliyon 13.

Haka kuma Gwamntin tace mu tabbatar da kame duk wani kayan laifi, sai gashi muna ta samun nasarar kame kayan lafin, wanda na shaida maka cewa a shekarar data gabata kayayyakin da muka kame idan da ace kudade aka biya musu da za a samu abin da ya tasamma Naira Miliyon 300. Bayan haka kuma an bamu umarnin bunkasa harkokin cinikayya tsakanin al’umma, kamar yadda da ku ‘yan Jaridu ku ka tabbatar da cewa an dai na fuskantar cece kuce tsakanin jami’anmu da ‘yan Kasuwa. Alhamdulillahi kwalliya ta biya kudin sabulu domin mun Tarawa gwamnatin kudin shiga wanda harma sun haura abin da gwamnati ke sa ran samu, mun samu nasarar kame kayan da ake bukatar kamewa, ga kuma bunkasa harkokin kasuwanci a tsakanin al’ummar Kano da Jigawa.

Shin ko akwai wani kalubale da hukumar taku ke fuskanta a halin yanzu?

Babban Kalubalen da muke fuskanta shi ne yadda wasu ‘yan Kasuw ke rungumar harkar fasakaurin amatsayin hanyar samun kudade, wannan ta sa kullum mukan samu matsalar wasu su kan runguma harka ta fasakauri

ka’in da na’in.musamman kokarin shigo da wannan shinkafa da aka hana shigo da ita ta kan iyakoki kasar nan, amma dai muna ta kokarin hana su.

Ya ya danganta ta ke tsakaninka da abokan aikin ka wadanda kuke gudanar da wannan babban aiki tare?

Alhamdulillahi  muna da kyakkyawar dangantar aiki a tsakaninmu, ma’aikata na suna gudanar da aikinsa yadda ya kamata wajen taimaka mana samun wannan nasarar abin da aka sa mu muyi,  muna da ofisoshi a Jihar Jigawa  kamar yadda muke da su a nan Jihar Kano. Muna aiki tare domin ciyar da wanann hukuma gaba.

Mene  sakon ga al’ummar Kano da Jigawa musamman ‘yan Kasuwa?

Babban sakon da zan aikawa al’ummar Jihar Kano da Jigawa shi ne su dauke mu aminan juna, muna taimakawa Gwamnatin tarayya ne kuma Gwamnatin tarayyanan tasu ce, Don haka su guji abin da zai sabawa

dokokin kasa wadda suka sabawa haramtattun cinikayya wadda Gwamnati ta haramta. Su shigo da halastattun kaya ba wadanda aka hana shigo da su ba. Sanan kuma kowa ya yi kokarin biyan harajin kayansa yadda ya

kamata.

Su yi kokarin kaucewa harkokin fasakauri domin fasakauri na kawo cikas ga ci gaban tattalin arzikin kasa, hakan ba daidai bane kuma ba ci gaba ba ne wannan shi ne babban kiran da zanyi ga jama’a, kuma muna

godiya bisa hadin kan da jama’a ke bamu a lokacin da muke gudanar ayyukan wannan hukuma.


Advertisement
Click to comment

labarai