Connect with us

LABARAI

Hukumar FIRS Ta Kwato Naira Biliyan 29 Ta Hanyar Hadin Gwiwa Da EFCC

Published

on


Shugabannin Hukumar tattara kudaden haraji ta kasa (FIRS) tare da Hukumar hana yima kasa tu’annafi na tattalin arziki, zasu hada kai domin gano, wadanda ke son  kaucewa biyar kukaden harajin da ya kamata su bada.

Sun kara bayyana cewar hadin kan nasu na aiki, har abin ya kai ga sa wa kuwa sun, samu kudaden Naira bilyan  29.

Shi wannan hadin kan zai kasance kamar wata fitila ce wadda zasu rika haskakawa domin gano wadanda suka ki ba ita Hukumar hadin kai, duk kuwa da yake da tsarinta na yin ahuwa. Bayyana kaddarorin da aka mallaka, da kuma bayanai na kudaden da suke shigo ma mutum, saboda su kammala biyan harajin daya kamata su biya.

‘’Tuni dai ita Hukumomin FIRS da EFCC  sun yi jagoranci na biyan wasu harajin da ka ki biya, kudaden da suka kai  Naira bilyan29, daga bankuna da kuma wasu Hukumomin harkar kudade, tsakanin watannin Nuwamba 2017 da kuma Maris 2018. Wahab Gbadamosi mai magana da yawun Hukumar shi ne ya bayyana haka  a wata sanarwa.

Mr Gbadamosi ya bayyana haka ne lokacin da aka yi taro a hedikwatar Hukumar dake Abuja shi shugaban Hukumar tara kudaden haraji ta kasa, Tunde Fowler ya ce Nijeriya kamar daisauran wasu kasashe tana neman yadda zata kara samun hanyar yadda zata dauki mataki akan wadanda suka ki biyan haraji. Shi shugaban Hukumar ya je EFCC ne domin kai ziyarar ban girma.

‘’Akwai maganar rashin biyan biyan kudin haraji yadda ya dace, ko ma rashin biyan harajin,  da kuma na kudaden da suke shigo ma mutum, ko shakka babu ita Hukumar EFCC ta bada gaggarumar gudunmawa, ana kuma ganin sakamakon yin hakan, bada dadewa bane bankuna biyu suka biya nasu harajin, wannan ba zai rasa nasaba da maganganun da suka ji, muna son hadin kai da EFCC, musamman ma yanzu maganar BAIDS ta kare. Su wadanda suka ki biyan haraji zasu dandana kukarsu.’’

‘’Ina son duk wanda ya isa ya biya haraji ya kwana da sanin cewar a shirye muke mu yi amfani da duka wata dama da muke da ita, mu tabbatar da cewar duk wanda yaki biyan haraji an hukunta shi kamar yadda da doka da kunshi hukunce hukuncen’’.

Mai rikon mukamin shugaban Hukumar EFCC Ibrahim Magu a shirye yake ya taimako wajen kawo kudade da yawa, da kuwa sa wadanda suke kin bada haraji su fuskanci doka.

Maguy a bayyana cewar ‘’Mutane na saurin amsar haraji amma kuma bau son su biya, domin bin yadda doka ta ce, abin babu dadi. A kwai bukatar samar da wata tawaga duk wani harajin da mutum ya amsa, ya bada shi akan lokaci, ina taya Hukumar FIRS murna saboda canjin da aka samu na tara kudin haraji. Ko shakka babuan samu  ci gaba akan tara kudaden haraji. Zamu ci gaba da yin haka, mun yi irin hakan a da lokacin da kay i horarwa a Kaduna, zamu tabbatar da duk abin da kuke so mu yi, idan dai har akan doka abin yake’’.

Shugaban Hukumar yayi kira da ‘yan Nijeriya dasu bada hadin kai wjen yaki da karbar rashawa, ya ce kowa yana da rawar da zai taka.

‘’Kowa yana da rawar da zai taka wajen yaki cin hanci, ba kuma dole bane sai kun yi yadda Magu yake yi ba, babban abin da ya da ce a gane shi ne, a fahimta sosai harkar cin hanci ba abu bace mai kyau, ina kira ga kowa da kowa yayi yaki da cin hanci tun a gida,, a fadawa ‘ya’ya cin hanci ba abu bane mai kyau’’.


Advertisement
Click to comment

labarai