Connect with us

LABARAI

Buhari Ya Yi Sabbin Nada-nade 23

Published

on


Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya amince da nada manyan jami’an hukumomi a ma’aikatar lafiya ta tarayya, Sadarwa da kuma al’adu, Ilimi, Hasken lantarki, ayyuka da gidaje, da kuma Kwamishinonin zabe na hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, (INEC).

Sakataren gwamnatin tarayya, SGF, Mista Boss Gida Mustapha, ne ya bayar da sanarwar a cikin wata takarda wacce daraktan sadarwa na Ofishin sa, Lawrence Ojabo, ya sanyawa hannu a madadin sa.

Wadanda aka nada din a ma’aikatar lafiaya sune, Dakta Abdulkareem Jika Yusuf, Medical Director, na, Federal Neuropsychiatric Hospital Kaduna, (bisa wa’adin shekaru hudu daga 8 ga  Afrilu 2018); Dakta Abubakar Musa, Medical Director, Federal Medical Centre, Nguru, Jihar Yobe (wanda za a iya sabunta mukamin na shi a duk bayan shekaru hudu daga 3 ga  watan Yuli 2017), da Dakta Abdullahi Ibrahim, Medical Director, Federal Medical Centre, Azare, Jihar Bauci (wanda za a iya sabunta mukamin na shi a duk bayan shekaru hudu daga 2 ga  watan Afrilu 2018).

Sauran sun hada da, Dakta Nasir Ibrahim Umar, Medical Director, National Obstetric Fistula Centre, Bauci Jihar Bauci (wanda za a iya sabunta mukamin na shi a duk bayan shekaru hudu daga 4 ga  watan Afrilu 2018), Dakta Iliasu Adeagbo Ahmed, Medical Director, Federal Medical Centre, Owo, Jihar Ondo (wanda za a iya sabunta mukamin na shi a duk bayan shekaru hudu daga 8 ga  watan Afrilu 2018), da Dakta Aliyu Muhammad El-Ladan, Medical Director, National Obstetric Fistula Centre Katsina, Jihar Katsina (wanda za a iya sabunta mukamin na shi a duk bayan shekaru hudu daga 8 ga  watan Afrilu 2018).

A ma’aikatar Sadarwa ta tarayya da al’adu, Dakta Stella Morounmubo Oyedepo, shugabar National Theatre, Lagos, (wanda za a iya sabunta mukamin na ta a duk bayan shekaru hudu daga 8 ga  watan Afrilu 2018), a bisa tanajin dokar kwadago, musamman sashen na 7 da na 8 na, National Theatre da National Troupe na Nijeriya dokar 1991.

“Da wannan nade-naden, Shugaban kasa, ya raba shugabancin, National Theatre daga National Troupe, ta Nijeriya,” in ji takardar sanarwar.

A ma’aikatar Ilimi, an nada Dakta Baba Dabid Danjuma, a matsayin shugaban Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Idah Jihar Kogi, (wanda za a iya sabunta mukamin na shi a duk bayan shekaru hudu daga 27 ga  watan Disamba 2017), Dakta Usman M. Kallamu, Shugaban Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Damaturu Jihar Yobe, (wanda za a iya sabunta mukamin na shi a duk bayan shekaru hudu daga 8 ga  watan Afrilu 2018), Dakta Jimah Momodu Sanusi, Shugaban Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Auchi, Jihar Edo, (wanda za a iya sabunta mukamin na shi a duk bayan shekaru hudu daga 23 ga  watan Fabrairu 2018), Dakta Dayo Hephzibah Oladebeye, Shugaban Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Ado Ekiti, Jihar Ekiti, (wanda za a iya sabunta mukamin na shi a duk bayan shekaru hudu daga 23 ga  watan Fabrairu 2018), da kuma,  Arch Sanusi Gumau, Shugaban Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Bauci, Jihar Bauci, (wanda za a iya sabunta mukamin na shi a duk bayan shekaru hudu daga 23 ga  watan Fabrairu).

Hakanan kuma, an nada, Tomunomi M. Abbey, Shugaban Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Danyan Mai da Iskar Gas da ke Bonny, Jihar Ribas, (wanda za a iya sabunta mukamin na shi a duk bayan shekaru hudu daga 23 ga  watan Fabrairu), Omokungbe Obafemi Omoseni, Shugaban Kwalejin Fasaha ta Yaba, Jihar Legas, (wanda za a iya sabunta mukamin na shi a duk bayan shekaru hudu daga 30 ga  watan Janairu 2018) da, Faruk Rashid Haruna, Shugaban Kwalejin Ilimi ta Kontagora, Jihar Neja, (wanda za a iya sabunta mukamin na shi a duk bayan shekaru hudu daga 27 ga  watan Maris 2018).

A sashen Hasken lantarki, Ayyuka da gidaje, an nada, Usman Gur Mohammed, a matsayin babban darakta, kamfanin sadarwa na kasa, TCN, (wanda za a iya sabunta mukamin na shi a duk bayan shekaru hudu daga 1 ga  watan Fabrairu 2018)

A hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, (INEC), an nada, Emmanuel Aled Hart, Kwamishinan zaben hukumar,  (REC), (wanda za a iya sabunta mukamin na shi a duk bayan shekaru biyar daga 17 ga  watan Afrilu 2018), Mohammed Magaji Ibrahim, Kwamishinan zabe, (wanda za a iya sabunta mukamin na shi a duk bayan shekaru biyar daga 17 ga  watan Afrilu 2018), Cyril Omorogbe, Kwamishinan zabe, (wanda za a iya sabunta mukamin na shi a duk bayan shekaru biyar daga 17 ga  watan Afrilu 2018), Uthman Abdulrahman Ajidaba, (wanda za a iya sabunta mukamin na shi a duk bayan shekaru biyar daga 17 ga  watan Afrilu 2018), Segun Agbaje, Kwamishinan zabe, (wanda za a iya sabunta mukamin na shi a duk bayan shekaru biyar daga 17 ga  watan Afrilu 2018), Baba Abba Yusuf, Kwamishinan zabe, (wanda za a iya sabunta mukamin na shi a duk bayan shekaru biyar daga 17 ga  watan Afrilu 2018) da Yahaya Bello, Kwamishinan zabe,  (wanda za a iya sabunta mukamin na shi a duk bayan shekaru biyar daga 17 ga  watan Afrilu 2018).

Sanarwar ta ce, Shugaban hukumar zaben ne zai rantsar da Kwamishinonin zaben a shalkwatar hukumar ranar Talata, 17 ga watan Afrilu 2018.


Advertisement
Click to comment

labarai