Connect with us

KIMIYYA

Ana Zargin Satar Bayanai Fiye da 250,000 Kullum Daga Google

Published

on


Shafin Google sun ce a kullum suna iya kokarinsu don ganin sun ba wa bayanai da mutane suke shigar wa intanet tsaro na musamman, ana zargin a kullum masu Kutse suna samun nasarar satar bayanan masu amfani da intanet, anfi satar sunayen shiga da lambobin bude su.

A wani bincike da aka gudanar a tsakanin shekarar 2016 zuwa 2017, an gano hanyoyin da dama da masu Kutsen suke amfani da su wajen satar bayanan mutane masu muhimmanci, shafin Google sun wallafa sakamakon binciken da hadin gwiwar jami’ar Kalifoniya ta Amurka, inda binciken ya nuna yadda aka samar da hanyar da za a iya gano bayanan da aka sata.

Masu binciken sun yi kokarin gano duk hanyoyin da masu Kutse suke bi wajen satar bayanan mutane, wanda ana ganin yawan hanyoyi da dabarun sunkai 25,000, sun samu wadannan hanyoyi da dabaru ne da ta hanyar tsananta bincike ba tare da an gano manufar yin hakan ba.

Google sunce shaidawa masu amfanin da shafinsu, zasu gudanar da binciken na tsawon lokaci domin gano hanyoyi da dabarun da masu Kutse suke bi don satar bayanan mutane, kuma lallai sun samu nasarar gano hanyoyi masu yawan gaske da masu Kutse suke bi don satar bayanai, sun bada misali da cewa ko mutum bai da kwarewa sosai a dabarun yin Kutse to mai sauki ne ya samu bayanai na yadda zai iya yin Kutse a dandalin masu Kutse dake intanet.

Misali a kwanan nan anyi wani Kutse da ake kira da sunan “Ekuifad Hack” wato Kutsen Ekuifad,  inda masu Kutse suka samu nasarar sace bayanan mutane masu yawan gaske, ana ganin a cikin shekara daya an saci bayanai da suka biliyan 1.9, an hada sakamakon binciken gaba daya harda watan Satumba an samu adadin bayanai da aka sace sun kai biliyan 3.3.

Amma ana ganin masu aikata laifukka a intanet suna da matukar dabaru sosai, suna amfani da hanyoyi biyu da suka fi shahara domin satar bayanai, hanya ta farko itace suna yaudarar mutane sai mutum ya dauka wasu amintattu ne don haka sai ya basu bayanai da suka shafi harkokin shi na intanet, sai kuma hanya ta biyu wato suna dibar duk bayanan da mutum yake sawa a shafukkan intanet, misali lambar katin ajiyar banki da sauransu.

Binciken na Google ya iya gano adadin mutum kusan 788,000 da za a iya yaudara a saci bayanan su, mutum miliyan 12.4 kuwa za a iya dibar sirrikansu ba tare da sun sani ba, don haka wannan Kutsen yana iya afkuwa a ko wanni lokaci, a kullum ana iya yaudarar mutum sama da 234,887 ta intanet, a yayin da ake iya dibar bayanan mutum kusan 14,879.

Lambobin bude ma’ajin bayanai kadai basu wadatarwa wajen yi wa mutum Kutse, dan haka masu Kutse suke kokarin samun sauran bayanai masu muhimmanci, wasu masu Kutsen suna iya satar bayanin wajen da mutum yake, lambar waya, lambar katin ajiya da sauran bayanai masu muhimmanci na mutanen da suke kokarin shiga shafukkan intanet.

Duk da shafin Google yana iya ganowa in aka yi kokarin shiga shafin intanet a wajen da ba a saba shiga ba, misali in kamfanin yaga ana kokarin shiga shafinka a jihar Kalifoniya ta Amurka bayan an saba kai daga jihar Kadunan Nijeriya ka saba bude shafinka to Google din zasu yi kokarin ankarar da kai, saboda hakane ma Google din suke iya hasashen duk guraren da yakamata ka bude shafinka.

Google din sun kara wani mataki na tsaro musamman ga masu amfani da akwatin wasiku na Gmail, kuma wannan matakin yayi nasarar kiyaye akant kusan miliyan 67 na Gmail daga masu Kutse.

A watan da ya gabata Google din sun kara fito da wasu hanyoyi da mutane zasu yi amfani da su don kara tsare akant dinsu na Gmail, cikin mataken harda wanda kai da kanka zaka saka don lokacin da ka ga dam aka zaka iya canzawa, duk da masana da dama suna ganin yakamata Google din su sake fito da dabaru sosai na bawa mutane kariya daga masu Kutse, amma ana ganin mutane da yawa basu damu suyi amfani da matakan kariyar ba.

Ana sa ran mutane zasu rungumi wadannan matakan na tsare akant dinsu, mutane da dam sunfi son hanya mai sauki wajen tsare akant dinsu, misali kamfanin Amazon suna da matakan kariya ga masu tahamulli da shafinsu, inda duk masu tahamulli da shafinsu sai sun amsa wasu tambayoyi da suka shafe su kafin su iya bude akant dinsu, ana ta kokarin fadada hanyoyin maganin masu Kutse ga masu tahamulli da shafukkan intanet.

Kuma kamfanin Google ne a sahun gaba a wannan kokarin, saboda masu amfani da shafukkansu kusan sunfi na ko wanni shafi yawa, sannan mutane suna tara bayanansu masu matukar muhimmanci a shafin, don haka suke ganin baza su yi kasa a gwiwa ba wajen samar da hanyoyin da masu tahamulli da shafinsu zasu bi don tsare bayanansu daga ‘yan Kutse masu satar bayanai.


Advertisement
Click to comment

labarai