Connect with us

LABARAI

2019: ’Yan Nijeriya Mazauna Amurka Da Ke Neman Kujerar Buhari

Published

on


Idan ‘yan Nijeriyan nan uku dake zaune a kasar Amuka suka samu abin da suke so to lallai sunayensu zai kasance a katin jefa kuri’ar zaben shekarar 2019, haka kuma zai zama karo na farko a tarihi da al’ummar Nijeriya dake zaune a ketare suka nuna shawa’arsu suka kuma shiga harkar siyasar kasar nan gadan-gadan.

A watan daya gabata ne Mista Gabriel Adegboye da Mista Samuel Mbonu da kuma Mista Omoyele Sowore suka kaddamar da yakin neman zaben darewa kujerar shugabancin kasar nan a can kasar da suke zaune ta Amurka. Amma duk sun kaddamar da yakin neman zaben nasu ne daga can kasar Amurka a cikin ‘yan Nijeriya mazauna can, hakan bai sa kungiyar ‘yan Nijeriya mazauna kasashen waje ta “Nigerians in the Diaspora (NIDO)” su rugume su ba, kungiya da shugabannin ta su na nisanta kansu daga wadanan ‘yan takaran.

A watan Fabrairu Mista Mbonu, mazunin garin Washington DC ya yi bukin sanar da bukatar sa na shiga gwagwamayar takarar shugabancin kasar nan a taron da aka yi a dakin taro na “Airforce One Boardroom” dakin taro ne dake cikin “Ronald Reagan Presidential Library” a garin California.

Majiyar mu bai yi mana cikakken bayanin yadda bikin nuna shaw’awar nasa ya gudana ba amma wani shafin labarai na intanet mai suna Elombah ya wallafa wasu mukala a watan Maris a kan yakin neman zaben Mista Mbonu da kuma irin tanadin da ya yi wa kasar nan in har ya samu cimma burinsa na zama shugaban Nijeriya.

Haka kuma, kamar sun hada baki, Mista Sowore, mawallafin shafin watsa labarai na Sahara Reporters, da Mista Adegboye, wani Fasto sun kaddamar da yakin neman zama shugaban Nijeriya a rana daya wato ranar 10 ga watan Maris a jihohin Amurka guda biyu da Maryland da Tedas. Mista Sowore ya kaddamar da taron yakin neman zaben nasa ne a wani gidan cin abinci na wani dan Nijeriya a birnin Bowie ta jihar Maryland yayin da bayani ya nuna cewa Mista Adegboye ya kaddamar da nasa taron yakin neman zaben ne a gidansa dake Pflugerbille ta jihar Tedas.

“Bamu san komai a kansu ba” inji Patience Key, shubaban daraktocin kungiyoyin NIDO da USA. “A hukumance kungiyar mu ta NIDO bata da wani masaniya a kan wadannna ‘yan takara da yakin neman zaben da suke yi”

An kirkiro da kungiyar NIDO ce a shekarar 2000, hadakar kwararrun ‘yan Nijeriya ce da kungiyoyin kwadago da sauran kungiyoyi dake zaune a kasashen waje da nufin samar da hanya mafi sauki da ‘yan Nijeriya dake zaune a kasashen wajen zasu yi mu’amala da gwamnatin da take mulki a Abuja. Tuni kungiyar ta rikida daga yin ragistan kananan kungiyoyi zuwa yi wa daidaikun mutane ta kuma fadada mazauninta daga garin Atlanta da Georgia da Canada da Europe zuwa Amurka ta Yamma da tsakiyar Amurka.

“A kan ‘yan Nijeriya dake zaune a kasashen duniya, muna tattatara bayan kwarewarsu don ganin yadda za a samu hadin kai ta taimakon kasar mu Nijeriya. Kungiyar mu bata siyasa ba ce, mu ba ‘yan siyasa bane, bamu kuma jingina da wata kungiyar siyasa ba” inji Misis Key wadda kuma ita ce shugaban kungiyar NIDO na jihar Maryland ta kasar Amurka.

Sylbester Mode, shugaban kungiyar a jihar Birginia, na da ra’ayin nesanta kungiyar daga ‘yan kasar dake da muradin siyasa mazauna kasar Amurka dama sauran kasashen duniya.

“Basa tare da kungiyar mu ta NIDO reshen Amurka, saboda kawai suna zaune a nan kuma suna takara bai mayar dasu cikinmu ba” inji shi.

Mista Mode, wanda yana zaune a yankin Washington DC ta kasar Amurka tun shekarar 1980, ya ce, a shekarun baya ‘yan Nijeriya masu ra’ayin siyasa sun sha yin amfani da kugiyar wajen cimma burinsu, ya tabbatar da cewar a wannan lokacin ba zasu yarda a yi amfani dasu ba wajen cimma burin siyasa.

“Da zaran sun isa Abuja, sai su shiga neman na kansu, su manta da kungiyar mu ta NIDO.”

Mista Mode ya kara da cewar, an yi wa kungiyar NIDO ragista ce, a matsayin wata kungiyar da ba zata tsunduma fagen harkokin siyasa ba kamar dai yadda dokokin kasa Amurka ya tanada.

“Mu ba ‘yan siyasa bane, sashi na 501 (c) 3 na tsarin mulkinmu ya nuna cewa mu wata kungiya ce mai zaman kanta ne wadda ba mai neman riba ba, hakan na nufin ba zamu iya shiga fagen siyasa ba” inji shi.

Daga dukkan alamu, wadannna ‘yan takarar basu zo a hukumance sun nemi goyon bayan mu ba duk da cewa, wasu daga cikinsu su gaiyaci daidaikun mutane a cikin kungiyar zuwa tarukkan yakin neman zabensu, kungiyarmu ta NIDO ta kuma gargadi manbobin ta a kan hada ra’ayoyinsu tare da ra’ayin kungiyarmu ta NIDO.

“Babban kuskure ne in wani dan kungiya ya halarci wani taron siyasa a matsayinsa na dan kungiyar NIDO”, inji Misis Key, ta kuma kara da cewar ta samu takardar gayyata zuwa taron yakin neman zaben Mista Mbonu dana Mista Sowore.

“Na san Sowore, na yi magana da shi na kuma gan shi lokacin da ya je yakin neman zabe a jihar Maryland amma na je taron ne a matsayin kashin kai na ba ina wakiltar wani bane”

Shaharraren mai wallafa jaridar nan ta intanet mai suna Sahara Reporters, Mista Omoyele Sowore a kwai alamun cewar, fitowar Missta Sowore da Mbonu da kuma Adeboye a matsayin masu takarar kujerar shugabancin kasar nan ya kada zukatan yan Nijeriya mazauna kasar Amurka fiye da yadda a ke tunani. A shekarun bayan, in lokacin zabe ya yi sai dai ‘yan Nijeriya dake zaune a kasar Amurka su karbi bakoncin ‘yan takaran kujeran shuganci daga gida Nijeriya musamman bayan an kamala zaben fid da gwani na jam’iyyu.

A watan daya gabata ‘yan takaran nan guda uku sun yi zagayen yakin neman zabe fiye da yadda ‘yan siyasa daga gida Nijeriya ke yi in shigo sai abin takaicin sakon da suka yi kokari shigo da bai kai ga inda ya kamata ba a tsakanin ‘yan Nijeriya mazauna kasar Amurka.

A sakon daya watsa dai-dai da fara yakin neman zaben nasa, Mista Adegboye, ya ce, Shi malamin addinin Krista ne kuma Allah ne ya kaddara fitowarsa ya jagoranci Nijeriya domin fito da ita daga rikice rikicen zubar da jini dana siyasa da matsalar tattalin arziki, An haife shi ne a ranar 9 ga watan Agusta 1965, dan asalin garin Ogbomoso, ta jihar Oyo, duk da cewar bai yi cikakken bayanin yadda zai cimma wannan manufa nashi ba amma ana saran in har ya kai ci zai tabuka wani abu. Ya kuma ce , bai shiga wani kungiyar siyasa ba a halin yanzu, sanan zai nufi gida Nijeriya ranar 10 ga watan Maris domin ci gaba da yakin neman zabensa.

A wani sakon daya tura ta kafar Youtube, Mista Mbonu ya bayyana cewar, shi ba kamar sauran ‘yan siyasan Nijeriya bane zai kawo cikaken ci gaba a kasar duk da cewa bai yi bayanin hanyoyin da zai cimma wannan burin ba. Ya shirya taro da ‘yan Nijeriya a garin Charlotte na jihar North Carolina ranar 9 ga watan Mayu domin ya tattauna sakamakon ziyararsa zuwa gida Nijeriya, ya mayar da hankali ne a kan abubuwa guda uku a yakin neman zabensa wadanda suka hada da samar da wutan lantarki da tsaftatacen ruwan sha da kuma tsaro.

Shi ko Mista Sowore, yakin neman zabensa yana samun tagomashi ne saboda matsayinsa na mawallafi, yana samun kabuwa a wajen ‘yan Nijeriya mazauna Amurka, amma duk da haka yawan mutanen dake bayansa bai kai abin azo a gani ba in aka kwatanta da yawan ‘yan Nijeriya dake kasashen waje.

Ya samu karbuwa kwarai da gaske a zagayen da ya yin a jihohin Maryland da Pennsylbania da kuma Michigan a watan Maris, amma irin yadda aka karbi bukatar neman gudummawar daya nema ba a bin a zo a gani bane shi ma. Ba a samu cimma Dala Miliyan 2 da aka nema na tallafin yakin neman zabensa, amma tun da a kwai sauran kwanaki kusan 300 kafin a gudanar da zaben yana iya kaiwa ga ci.


Advertisement
Click to comment

labarai