Connect with us

RAHOTON MUSAMMAN

Yadda Mata Ke Kauracewa Haihuwar Asibiti A Kauyukan Abuja

Published

on


Wannan wani rahoto ne na musamman dangane da yadda mata a wasu yankunan Abuja suke kauracewa halartar asibitoci domin haihuwa, sai dai su nemi agajin unguwar zoma. Kafar sadarwa ta PREMIUM TIMES ce ta gudanar da binciken wanda wakilinmu UMAR A. HUNKUYI ya fassara domin amfanin masu karatunmu.

Asabe Joshua, tana zaune ne a kauyen Igu, da ke can wajen garin Abuja, babban birnin kasarnan. Kauyen yana da tazarar Kilomita 15 ne kacal tsakanin sa da garin Bwari, shalkwatar Karamar Hukumar Bwari. Garin na Igu, tamkar ire-iren karkara ne da ke sassan nahiyar Afrikan mu.

Akwai dan karamin asibitin shan magani a kauyen, amma dai mai kaman da babu ne.Asabe Joshua, tana zaune ne a kauyen Igu, da ke can wajen garin Abuja, babban birnin kasarnan. Kauyen yana da tazarar Kilomita 15 ne kacal tsakanin sa da garin Bwari, shalkwatar Karamar Hukumar Bwari. Garin na Igu, tamkar ire-iren karkara ne da ke sassan nahiyar Afrikan mu.

“Mama, Anguwar zoman mu ce ta karbi haihuwar ‘ya’yana dukansu, in ji Uwargida matan Joshua, wacce take da ‘ya’ya biyu, kamar yadda ta shaidawa wakilinmu.

“Gaskiya ta fi Nas-Nas din asibitin namu ma kwarewa wajen karban haihuwa, sannan kuma a duk lokacin da aka bukace ta tana nan.”

Wakilinmu, ya yi jimirin yin wannan mawuyaciyar tafiyan a kan babur, a kokarin sa na ganin sai ya isa wannan kauyen na Igu. A kan wannan hanyar ta kura da kwazazzabe, da ta hada wannan sashen da birnin na Abuja, tsakanin kauyen da Abujan, akwai wasu kauyakun kamar na, Baragoni, Zuna, Gaba da Danko, duk a kan hanyar.

Hakanan dan babur din da na dauki hayarsa ya yi ta tsalle da ni gami da ratse-ratse a wannan murdaddiyar hanyar domin kaucewa fadawa ramuka. Mazauna yankin masu bin hanyar a kullum, hakanan ala tilas suka dangana suke bin wannan hanyar duk da wahalarta da rashin dadinta kullum a bisa Kekuna da Baburan su. Wannan hanya mai yawan kura, hakanan take sama da shekaru 10, a kowace damina kuma kara tabarbarewa take yi.

Daure take da wani tsohon zani a kirjin ta, bisa wata rigar shimi wacce ga dukkanin alamu da can fara ce, ‘yar kimanin shekaru 23, Uwargida Matar Joshua, ta zayyano wa wakilin namu yadda ma’aikatan jinya da ke wannan dan karamin asibitin na su, suka tilasta mata komawa wajen Mama, watau anguwar zoman gargajin da ke nan kauyan na su.

“Kafin na haifi dana na farko, na kan je asibitin a duk ranakun awo. A lokuta da yawa, idan ni da sauran masu cikin sun je Asibitin awon cikin na su, kamar yadda aka tsara, sai ka ga, ko dai a ce su ma’aikatan Nas-nas din ba sa nan a bakin aikin na su, ko kuma ko da suna nan din, sai su ce mana mu koma sai gobe mu sake dawowa.

“Ko a lokacin da na fara Nakuda, da misalin karfe 5 na yamma, sai mijina da kuma wani makwabcinmu suka je asibitin domin su kira ma’aikatan jinyan. Wacce suka samu a bakin aikin sai ta gaya masu cewa, su koma ga ta nan zuwa yanzun nan.

“Bayan kimanin mintuna 30 ba ta zo ba, sai mijin nawa ya sake komawa domin ya sake yi mata magana, ko da ya isa asibitin sai ya taras da ba kowa ta ma fita ta kulle asibitin gabadaya. Hakan ya tilasta makwabciya ta zuwa ta kira Mama, Anguwar zoman gargajiyan kauyan namu, wacce a cewar makwabciyar nawa, duk Mama din ce ta karbi haihuwar ‘ya’yanta 4 da ta haifa. Bayan na haife lafiya, sai na kawo Naira dubu guda na baiwa Mama din, wacce ta karba cike da murna da farin ciki,” duk a cewar Matar Joshua.

Anguwar zoman gargajiya, ita ce wacce ta kan taimakawa mata a lokacin haihuwa. Yawanci su kan koyi aikin ne ta hanyar saba yin aikin da wasu anguwar zoman da ta gabace su. Ma fi yawan lokuta za ka taras tsaffi ne, wadanda suke da kwarewa a kan aikin, sukan kuma dauki aikin da suke yi din ne a matsayin taimako kawai.

Me Ya Tilas Ta Wa Mutane Komawa Wajen Anguwar Zoman Na Gargajiya

Yawancin mata a wasu sassan na kasarnan,musamman a karkara da kauyaku, sun fi amincewa ne da su haihu a gida a hannun Anguwar zoman ta gargajiya, a maimakon zuwa asibitocin su haihu. Sau da yawa abin da suke kokawa da su su ne, nisan tafiyan da za su yi zuwa asibitocin, ko kuma kudaden da za a caje su a asibitocin. Wasu kuma matan sukan koka da cewa, ma’aikatan jinyan na asibiotocin sukan wulakanta su, don haka sukan gwammacewa yanda anguwar zoman ta gargajiya da ke tare da su kan tararrabe su cikin jin kai da tausayi.

Yawancin kananan asibitocin ma ba su da cikakkun kayan aikin da za su kula da matan masu haihuwa a lokutan nakuda da kuma ma bayan haihuwan na su, wannan ya sanya mata da yawa ba sa ganin wani alfanun zuwa iren wadannan  asibitocin.

Binta Nuhu, ita ce, anguwar zoman ta gargajiya, wacce mazauna kauyan na Igu, ke wa lakabi da Mama, wacce Matar Joshua ta yi ta maimaita ambaton ta a baya can. Wakilin namu ya sadu da ita, a bakin hanya tana zaune kusa da wajen da diyarta ke sayar da mayukan injin Babura. Bayan da wakilin namu ya gabatar mata da kansa ne, cikin jin dadi da farin ciki, sai ta janyo wata kujerar roba da ke kusa da ita ta mika masa domin ya zauna a gefen ta.

Binta Nuhu, ta ce, shekarun ta 55 ne, ta kuma shafe sama da shekaru 25 tana yin wannan aikin na anguwar zoman gargajiya. Ta kuma haihu, domin ‘ya’yanta shida, kuma tana alfaharin duk sun manyanta, suna ma da nasu ‘ya’yayen.

Da harshen Hausa ne take iya magana, Mama, ta shaidawa wakilin namu irin kwarewar da ta samu da kuma irin kalubalen da take fuskanta a matsayin ta na anguwar zoman gargajiya a wannan kauyen na Igu.

“Na sami horon watanni bakwai a cibiyar lafiya ta Kafi Koro, da ke Jihar Neja. A can din ne na koyi yadda ake karban haihuwan jarirai. Na karbi haihuwan sama da Jarirai 400, a yanzun haka da yawa daga cikin su duk sun yi aure, su ma suna da na su ‘ya’yan,” in ji Binta Nuhu, tana labarta mana kwarewar ta da kuma jin dadin ta kan aikin da take yi.

“Na kan karbi Naira dubu guda ne a kan kowace haihuwa. Amma kasantuwar yadda komai ya yi tsada a kasarnan yanzun na kan karbi Naira dubu biyu ne, a wasu lokutan kuma Naira dubu daya da dari biyar. Ko tagwaye ko haihuwan daya duk kudin daya ne.

“Baya ga aikin gona, wannan shi ne sana’a ta, da na dogara da ita. A baya na kan sayar da kwayoyin asibiti, amma tun a bara na daina saboda mutane sais u karba amma ba sa biya.

“Na kan ma yi allura, na bayar da maganin zazzabin Maleriya da na Tyfod. Idan marar lafiya ya zo gare ni, da na kalli fuskan su, na san abin da ke damun su, sai na karbi kudi a hannun su na je kantin sayar da magungunan na sayo magani, kila da kuma allurar da ta dace,” in ji Mama.

“Amma idan na lura abin ya fi karfi na, sai na tura su asibiti. Sai dai mafi yawan lokutan ma’aikatan asibitin ba a samun su, don haka sai mun nemo hayan masu Keke ko babur domin su kai marar lafiyan babban asibitin Bwari.

“Wata mace ba ta taba mutuwa a karkashin kulawa ta ba, domin na kan yi abin da ya dace cikin hanzari. Da zaran na lura matan ba ta samun sauki, sai na hanzarta kiran ‘yan’uwanta domin su yi gaggawan kai ta babban asibiti,” in ji Mama.

Mama, din ce ta karbi haihuwar Hannatu Sunday, na ‘ya’yanta duka biyu. Tana magana da jabun turanci na, ‘fidgin,’ ta shaida ma wakilin namu cewa, ita fa ta dogara ne ga aikin Mama din, domin ma’aikatan jinyan da ke asibitin na su ba sa kulawa da marasa lafiya da kyau, sannan kuma ga kudin da suke tsuga wa mutane.”

“Hatta a lokacin da muke zuwa awon cikin, sai su yi ta zagin mu, ba sa tausasa mana. Sannan ka na haihuwa a hannun su, sai ka biya Naira dubu biyar, a maimakon 1,500, da za ka baiwa Mama.

Matar Sunday ta ce,  yaro guda ne kadai daga cikin ‘ya’yanta uku ta haifa a asibitin na Igu.

“Wata ‘yar Cocin mu ce ta hada ni da Mama. dan da na haifa na biyu da na uku, duk Mama ce ta karbi haihuwan na su. Har gida za ta biyo ka ta amshi haihuwan ba sai ka je gidanta ba.

“Ban taba kuma samun wata matsala ba, a bayan na haihu din. ni da abin da na haifa, duk za ka taras muna cikin koshin lafiya. Bayan mun haihu ne mu kan kai Jariran asibiti domin a auna su, a kuma yi ma su allura. Wannan ne kadai abin da asibitin ke iya yi mana,” a cewar ta.

Jikokinmu ma da yawa duk Mama din ce ta karbi haihuwar na su.

Joyce Zaka, ita ce diyar Mama ta uku. Mama din ce kuma ta karbi haihuwar ‘ya’yanta hudu duka, kamar yadda ta shaidawa wakilin namu.

“Asibitin ba ya aikin komai, ba kuma mota a cikin sa da za ta iya kai mu cikin gari. Wani abin jin dadi kuma shi ne, har gida Mama ta kan zo domin ta karbi haihuwan. Kiranta kawai za a yi, sai ka ga ta zo da sauri. Ni uwata ce, don haka ba na biya, amma ta kan amshi tsakanin Naira 1,500 zuwa 2,000 ne a hannun sauran matan.

“Bayan an haihu, sai mu kai Jaririn asibitin domin a auna shi. Mu kan kuma kai Jariran a yi ma su allura idan lokaci ya yi,” in ji matar Zaka.

Ziyarar da wakilin namu ya kai karamin asibitin na Igu, ya ganin ma idonsa dalilin da matan kauyen suka gwammace haihuwa a wajen anguwar zoman gargajiyan maimakon su je asibitin.

Asibitin a bude ya ke, amma ba kowa a lokacin da wakilin namu ya isa. Bayan kimanin mintuna 30 ne sai ga wata mata mai kimanin shekaru 30 mai suna, Eunice Gagare, ta shigo asibitin.

Eunice Gagare, Nas ce a asibitin. Ta ce, ta je kai sako ne a wani kauyen da ke kusa da nan din.

Ta ce, yawancin mazauna kauyan na Igu, sun fi gwammacewa su ta fi manyan asibitocin da ke cikin gari.

“Matan su kan zo awon ciki a nan, amma in lokacin haihuwan na su ta zo, ba ma ganin su. Sai dai mu ji labarin cewa sun haihu kawai, ko kuma mu gansu da Jariran su. A wasu lokutan, in sun sami matsala wajen haihuwan a hannun anguwar zoman na su ta gargajiya, su kan zo nan, amma da shike ba mu da kayan aikin da za mu kula da matsalar na su, sai mu tura su asibitin Bwari kawai,” in ji ta.

Amma me ya sa ake kulle asibitin, bayan kuwa an yi shi ne don a kula da marasa lafiya, Eunice Gagare, ta ce, “ Ba lantarki a wannan garin. Don haka muke kullewa da misalin karfe 5 na yamma a kullum, don ko mun zauna zuwa dare, ba hasken lantarkin da za mu iya yin aiki da shi.

“Da Tocilolinmu kawai muke aiki a wasu lokutan, idan sun yi mana kiran gaggawa. Amma a yanzun haka, tocilolin namu da kuma wayoyin mu da muke haskawa duk sun mutu, sai mun sami wanda zai je cikin gari, sai mu ba shi ya je ya yi wo mana cajin su, washegari ya dawo mana da su.”

Yanda Lamarin Yake A Igu, Haka Yake A Shere Koro

Daga wannan kauyen na Igu ne, wakilin namu ya ziyarci kauyen Shere Koro, nan kusa da Igu din ne yake, a can din ma, da yawa daga cikin mazauna kauyan sun shaida masa cewa sun fi aminta da aikin anguwar zoman ta gargajiya, a bisa asbitin, domin aikin na ta ya fi arha ya kuma fi kyau.

Ebelyn Mba, uwa ce mai ‘ya’ya biyu, ta ce, Naira 500 kacal anguwar zoman da ta karban mata haihuwan ‘ya’yanta, ta caje ta.

“Ga ta da tausayi da haba-haba da mutane. Ta kan dauke mu tamkar ‘ya’yan da ta haifa ne, kudin ma ko ba ka da su, sai ta ce, duk lokacin da ka samu sai ka biya ta. Amma in ko ka je asibiti, tilas ne ka biya 5,000, nan take kafin ma su taba ka. Kudin sun yi tsada sosai, yawancin mu ba mu da wannan kudaden,” in ji ta.

Wata mazauniyar kauyan, Hannah Lazarus, ta ce, nisan asibitin da ke Shere Koro din ba matsala ne ba. “Amma duk da haka, mutane sun fi ganewa zuwa wajen anguwar zoman ta gargajiya, domin a wasu lokutan ma kyauta take karban haihuwan na su.

“Idan ka ce mata ba ka da kudi, sai ta ce maka ai ba komai ka bar shi kawai. Don haka a wasu lokutan, sai in mun haihu ne sai mu kai mata kayan abinci domin godiya kawai,” in ji ta.

Sai dai, Babbar malaman asibitin, Christiana Kagbu, cewa ta yi, ba sa samun hadin kai daga matayen ne, don haka ba sa yaba taimakon da suke yi ma su.

“A lokutan awo, mukan shaida masu, da zaran lokacin haihuwa ya zo su hanzarta zuwa asibitin, amma ba sa zuwa. Sun gwammmace wa anguwar zoman gargajiya, amma da zaran sun sami matsala a wajen ta, sai ka ga sun kawo su nan. Hakan yana ba mu wahala sosai, domin ba su san abin da anguwar zoman gargajiyan ta taba ko ta yanke masu ba,” in ji Kagbu.

“Duk matsalar da ba ma iya mata, sai mu tura su babban asbitin cikin gari wanda yana da nisa daga nan. Ba mu da motan daukan marasa lafiya, sai dai majinyacin ya nemi mutanan da ke da mota su kai su asibitin,” in ji ta.

Anguwar zoman ta Shere Koro, ba ta gari a lokacin da wakilin namu ya ziyarci garin.

Gwamnati Tana Daidaita Aikin Anguwar Zoman Gargajiyan

Babban Daraktan Cibiyar kula da lafiya ta kasa, National Primary Health Care Debelopment Agency (NPHCDA), Faisal Shuaib, cewa ya yi, gwamnati tana yaba aikin anguwar zoman na gargajiya, a inda suke bayar da gudummawar su a mataki na farko kan sha’anin haihuwan, amma a yanzun haka, gwamnati na bin wasu matakai domin gyarawa da saita aikin na su, a karkashin shirye-shiryen hukumar kula da lafiya ta anguwanni, (CHIPS), wanda kwanan nan gwamnati ta kaddamar da ita.

A cewar Mista Shuaib, cikin wata tattaunawa da ya yi da, ‘PREMIUM TIMES,’ daga cikin aikin na hukumar ta, CHIPS, shi ne gano ko su waye ainihin anguwar zoman na gargajiya domin a horar da su ta yadda za su iya karban haihuwan ba tare da haifar da wata matsala ba.

Ya ce, su wadannan CHIPs, din, sun bambanta da anguwar zoma na gargajiya,” wadanda ba su da ilimin komai.”

“A wasu lokutan, idan anguwar zoman na gargajiya suka karbi haihuwa, a kan sami matsala, wani lokacin ma har ta kai ga mutuwar uwar ko Jaririn. Ba don komai ba, sai don ba su da kwarewar da ta dace.

“Yanzun muna son mu sanya ido sosai wajen zaben wadanda za su iya aikin a cikin su.

“Su wadannan CHIPs din da aka kaddamar, suna tare da al’umma ne, an kuma zabo su ne tare da hadin kan Sarakunan gargajiya, Shugabannin Addini, Shugabannin al’umma, Matasa da kuma kungiyoyin da ke cikin al’umman.

“Da zaran wadannan shugabannin sun gano wadanda suka cancanta, sai mu ba su horo kan yadda za su gudanar da aikin na tsawon watanni uku zuwa shida. Ba a aji kadai ba, a aikace ma za mu gwada masu. Su wadannan din ne za mu dora ma alhakin wannan aikin a cikin a;l’ummu.

“Muna kokarin tattara su ne duka, muka sanya masu sunan, jami’an na CHIPs.

Wata ma’aikaciyar lafiya, Kua’alar Katty,  ta yi gargadin cewa, matan da kan je wajen anguwar zoman na gargajiya, suna fuskantar hadari ne babba na samun sabani a wajen haihuwan.

Ta ce, yawancin matsalar da a kan samu a irin wannan lokutan, su kan kai ne ga mutuwar Uwar da Jaririn.

“Anguwar zoman gargajiya,sukan yi amfani da kayan aikin da ba a kula da su da kyau ne ba, wanda hakan ke sanya haifar da wata cutan da za ta iya kaiwa ga hana samun wata haihuwan,” in ji ta.

Malama Katty, sai ta shawarci mata masu ciki musamman na karkara da su rika ziyartan cibiyoyin lafiya, domin hakan zai amfani Uwa da Jaririn da za a haifa.

 


Advertisement
Click to comment

labarai