Connect with us

KASUWANCI

Kwamitin Bibiyan Lamarin Tattalin Arziki Na CBN Ya Ci Gaba Da Aiki

Published

on


Tattalin arzikin Nijeriya zai fita daga cikin halin kuncin da ya shiga na watanni shida, saboda kiki-kaka din da aka yi tsakaninsu da majalisar zartaswa, saboda matakin da tsarin kwamitin kudade, na babban bankin kasa zai kammala.

Cikin watan Nuwamba ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika wa majalisar dattawa da sunayen mutane biyar, domin a amince dasu domin su maye guraben da ake dasu.

Biyu daga cikinsu za su kasance na akan mukaman mataimakan gwamna na babban bankin kasa, amma kuma sai hakan ya ki yiwu wa a dalilin takun sakar da ake yi lokacin tsakanin majalisar dattawa da ta zartaswa, har ma sai da aka yi watanni shida.

Daga cikin wannan lokacin ne masu sharhi suka kira da suna lokacin da aka shiga halin ni ‘yasu, da abin ya shafi gida da kuma waje, lokacin da masu zuba jari a kasuwar kudade ta Nijeriya suke bin abin da taka tsantsan.

Halin da ake ciki na tsarin yadda al’amura suke sai abin ya kasance ba yabo ba kuma fallasa, musamman ma basukan cikin gida, da kuma kudin ruwa.

Amma kuma makonni biyu da suka wuce su ‘yan majalisar sai suka mayar da wukarsu cikin kube, suka amince da sunayen mutanen da aka tura masu. Wannan kuma shi ya bada dama ta ci gaba da taron da ake yi na MPC, wanda sanarwar bayan taron ake sa ran ta daga baya.

Watannin ukun farko na shekarar 2018 wani lokaci ne namurmushi da kuma kuka, ga kasuwar hannun jari ta kasa, saboda duk abubuwa sai suka yi kamar komai ya tsaya ta wancan bangaren.

Shi irin halin da aka shiga kamar yadda masu hada hadar suka ce, ya kasance hakan ne, saboda zaman rashin tabbas da aka kasance na wani lokaci mai tsawo.

Lokacin aka yi hada- hadar kasuwannin sayar da hannun jari, a watanni uku da suka wuce, wanda shi ne kuma a lokacin ya sa, aka damu dangane, da taron tsare- tsare na manufofi, da kuma inda aka dosa, kasuwar jari wurin da mutane da yawa suka yi asarar bilyoyin Naira.

Bayan haka kuma jiya da ya kasance 3 da watan Afrilu ne, wanda kuma kwata ta biyu ce a cikin shekarar. An ci gaba da kasancewa cikin hali na gaba kßura baya sayaki, a kwata ta farko, lokacin da aka yi asarar mukudan kudade.

Wannan shi yasa farashin ya fadi da fiye da  kashi daya, wannan ya nuna ke nan an fadi 548.87, ko kuma fiye da kashi daya da rabi, zuwa 40,855.64 daga 41,504.51, lokacin da kuma harkar kasuwanci tayi kasa daga Naira Tiriliyan14.758 zuwa Naira bilyan234.

Ranar 20 ga watan Maris kuma sai harkar kasuwanci ta yi kasa daga Naira Bilyan 52  daga Tiriliyon 14.964, wanda aka samu ranar Litinin zuwa Naira tiriliyon14.912, wannan ya nuna ke nan an yi asarar Naira bilya 236 ko kuma kashi 1.53, daga Tiriliyon 15.666 zuwa Tiriliyan 15.430 ranar 6 ga watan Maris, aka yi asarar Naira bilyan 139 ko kuma kashi 0.9 ranar 12 ga watan Maris, daga Naira Tiriliyon 15.476 zuwa Tiriliyon 15.337.

Masu fashin baki sun danganta hakan  ne da al’amuran da suke faruwa dangane da, halin rashi tabbas akan al’amarin daya shafi tsaro, da masu zuba hannun jari, suke tunani yayin da kuma suke tunanin samun madafa, tsakanin lokacin da suka kasance babu wani taron MPC.

Shugaban  masu hulda da hannun sa jari a Bankin United Bank for Africa (UBA) Rasak Abiola ya bayyana cewar, kasuwar tana ciki saboda dawowar shi taron, wanda shine babban muhimmin abin da ake jiran sakamakon shi, wannan kuma ana sa ran matakan da aka dauka da kuma sanarwar da za a bada.

Maganar gaskiya babu maison al’amarin da ya shafi halin rashin tabbas, musammanma bangaren da ya shafi, kasuwar hada- hadar kudade,abin sai y kawo halin rashin tabbas, da kuma tsoro. Lokacinne ba wani mai zuba jari da ya kasance cikin farin ciki, a dalilin rashin taron, amma kuma tsarin al’amuranda suka shafi kudade, kamar yadda babban bankin kasa ya tanadar, abin ya yi matukar taimakawa, domin ci ga bada hada- hadar kudade kamar yadda aka saba.

Mai bada shawara akan tsarin hada – hadar kudade Dokta Uzochukwu Amakom ya bayyanawa jaridar Guardian, a dalilin rashin taron da ba a yi ba har na tsawon watanni shida, wannan ya nuna ke nan, maganar taronda ka e na shekara kan harkokin kudi, da suke nuna ga alkiblar da aka dosa, saboda cimma manufofi,da suka kasance sune ake dogaro dasu, wannan ya nuna ke nan, har yanzu baa san halin da ake ciki ba tukuna.

‘’Tunda yake MPC suna taro cikin wannan mako,da akwai bukatar ta fitar da,sanarwa mai karfi wadda, da kuma sake duba, dukkan abubuwan da aka san zasu taimakawa, tattalin arzikin kasa zuwa tafarki mai kyau’’.

Babban jami’i kuma mai kula da New Capital Limited Ouropo Dada, shi ma yayi bayani ne dangane da Amakon, inda yake cewa ita kasuwar ta gane, halin da ake ciki na rashin tabbas, a irin alkiblar da aka dosa, irin wannan ne kuma ke bada dama ta, a rika shaci fadi hakan, bayan da, ba a san inda ka dosar ba.

‘’Tsarin hada –hadar kudade yadda za a tafiyar da shi, wasu abubuwa ne akan yadda za atafiyar da harkokin kudade, idan kuma shi kwamitin ya kasa daukar wasu kwararan matakai, wannan wata manuniyace da ke nuna akwai babbar matsala dangane da tattalin arziki.

‘’Duk masu hada- hadar kudade yanzu abin da suke jira shi ne. me zai faru da bangare kudin ruwa, da yake matsin tattalin arziki yana kara ci gaba, saboda tsadar rayuwa ta far yin sauki, watakila MPR zasu dan yi kasa, idansu MPC sun yi taro. Amma kuma akwai rashin tabbas, da kuma sauran abubuwan da mutane ke shakkunsu.’’

Shugaban Chartered Institute of Stockbrokers (CIS) Oluwaseyi Abe ya nuna rashin jin dadinsa akan, daukar tsawon lokacin da ka yi, babu taro na MPC wato taron kwamitin tsarin harkokin kudade, hakan ya hana ke nan, sanarwarmatakan da ka dauka dangane da tsare tsaren manufoifin kudade, wanda wata manuniya ce da babban bankin kasa ke nuna hanyar data kamata  abi.

‘’Abin da wannan ke nunawa anan shi ne ba wasu tsare tsaren da ka dauka, wanda zai iya sa kasuwanni su ce wani abu, duk wani bayanin da zai biyo bayan taron MPC shi zai kara karfafa tattalin arziki.’’

Akwai abubuwan da suka rika faruwa wadanda kuma muka sani, amma kuma ba a bada sanarwa dangane dasu ba, musamman ma wadanda suka shafi kasuwannin kasa da kasa, yanzu suna yin al’amura da ka  ne basu da wata makamar da zasu iya dogara da ita.

 


Advertisement
Click to comment

labarai