Connect with us

KASUWANCI

Basukan Biliyan 650: Dillalan Man Fetur Za Su Matsa Wa Majalisa Don A Biya

Published

on


Dillan mai fetur na kasa sun karyata labarin cewa, sun fara sallamar ma’aikatansu saboda rashin biyan su bashin Naira Biliyan 650 da suke bin gwamnatin tarayya.

An kuma samu labarin cewa, dillalan man fetur sun amince da matsa wa majalisar tarayya lamba domin ta amince da a biya su kudaden, shugaba Muhammadu Buhari ne dai ya mika wa majalisar bukatar biyan su kudaden domin amincewarsu.

A farkon wannan shekarar ne dillalan man fetur a karkashin kungiyoyin “Depot and Petroleum Products Marketers Association of Nigeria” da kuma hadin gwuiwar “Major Oil Marketers Association of Nigeria” suka yi barazanar korar ma’aikatansu in har gwamnatin tarayya ta yi kunne uwar shegu da batun biyan su basusussukan da suke bi.

Sai dai a ranar 5 ga watan Maris dillan man fetur din suka janye wa’adin kwanaki 14 da suka ba gwamnatin tarayya a kan basususukan da suke bin gwamnatin tarayya na Naira Biliyan 650, bayan tattaunawa mai mahimmanci da amfani daya gudana tsakaninmu da hukumar NNPC da ma’aikatar kwadago da ofishin shugaban kasa da kuma kungiyar DAPPMAN/MOMAN.

Dillalan man ferur din sun nuna amincewar su a kan cewa, gwamnatin tarayya zata cika musu alkawari a tsakanin mako 2 bayan janye wa’adin kwanaki 14 da suka yi, hakan bai yiwu ba abin daya jawo raderadin cewar kanfanonin man sun fara sallamar ma’aikatansu.

Da aka nemi ji ta bakinsa a kan koran ma’aikatan da ake zargin kanfanonin mai na yi a kasaar nan, babban sakataren kungiyar DAPMMA, Olufemi Adewole, ya ce, ba shi da masaniya a kan wani ma’aikaci da aka kora sakamakon rashin biyan bashin da suke bin gwamnatin tarayya.

Ya ce, “Ba zan iya tsokaci a kana bin da bani da isassun hujja a kai, amma a iya sani na an janye wa’adin da aka ba gwamnatin tarayya ne sabo a sami isassashe lokaci da gwamnati zata shirya takardun daya kamata ta kuma aikawa majalisar tarayya har su kuma su tattauna tare da amince das hi ta inda gwamnatin tarayya zata samu ta biya dillalan kudadensu”

“A bin da na sani kenan a halin yanzu amma bani da labarin an kori wani daga bakin aiki saboda maganar bashin da muke bin gwamnatin tarayya, amma da muna sane da cewa, mutanenmu na tsananin bukatar kudade, shi ya sa muke kara matsa namba ga gwamnatin tarayya su gaggauta biyan dillalan man fetur din kudaden su”

Adewole ya kara da cewa, dillaan man fetur na jiran majalisar tarayya ta dawo daga hutun Easter, suna kuma fatan da zaran sun dawo zasu shi ga tattaunawa a kan yadda za a biya dillalan man fetrur din kudadensu.

Ya ce, “Muna da labarin shugaban kasa ya sanya hannu a kan takadar biyan kudaden a taron majalisar zartaswa na kasa an kuma riga an turawa majalisar tarayya domin amincewa”

“Bayanin da muka samu ya nuna an aika da takardar gab da zuwa hutun Easter, saboda haka basu samu gabatarb da wasikar a gaban majalisar ba, muna sa ran za a karanta wasikar ranar Laraba daga nan ne zamu fara bibiyan wasikar da nufin gani a biya mu kudaden mu”

Da aka tambaye shi ko suna da tabbacin majalisar kasa zata saurari takardar ranal laraba, sai Adewole ya ce, “Mu dai mun samu labarin bangaren zartasawa sun aika da takardar zuwa majalisar kasa, saboda haka da aaran sun dawo hutun Easter zamu bi sawun maganar, domin mu san matsayinbashin Biliyan 650 da dillalan man fetur ke bin gwamnatin tarayya”

Adewole ya ce, ko da gwamnatin tarayya ta biya su kudaden da suke bi, ba zasu ci gaba da shigo da man fetur ba a nan gaba.

Ya kara jaddada cewa, biyan bashin naira Biliyan 650 ba zai sa su ci gaba da shigo da man fetur ba, saboda har yanzu in har zasu shigo da man fetur sai kudinsa ya fi Naira 145 a kan kowanne lita.

A halin yanzu hukumar NNPC ce kadai ke shigo da man fetur a Nijeriya,a lokutta da yawa hukumar na korafin cewa, rashin sa hannu da wasu dillalan man fetur basa yin a shigo da man fetur din ya dora nauyi akan NNPC din abin da ke haifar da matsananciyar karancin man fetur a wasu lokuttan.

Adewole ya ce, “Lamarin shigo da fetur ba wai kawai mutum zai je matatan mai ya lodo mai kawai bane, In zaka shigo da man fetur sai ka je wajen abokan huldar ka kamar a kasar Amsterdam ko Europe ko kuma Rasha, bayan kun shirya sais u baka rana, kamar mako 2 kafin ya iso Nijeriya.

“Tun da farko sai ka biya su kudi kakadan, a halin yanzu bamu da kudaden, duk da mun janye wa’adin ba zamu iya shigo da man ba saboda bamu da kudi”

“In an biya mu kudaden kuma kudin fetur din ya dan fi Naira 145 bayan mun shigo da shi to zamu iya ci gaba da aiki shigo da fetur din, amma ko yau a ka biya mu kudaden amma kudin fetur din bai fi naira 145 ba to ba zamu yi aiki fito da man fetur din ba.


Advertisement
Click to comment

labarai