Connect with us

BIDIYO

SHARHIN FINAFINAI: Sharhin Fim Din ‘BURIN DUNIYA’

Published

on


Tare Da: Saddika Habib Abba 09097438402 [email protected]

 

Suna: Burin duniya

Tsara labari: Habun Hajiya

Furodusa: Yunusa Mu’azu

Bada umarni: Yusuf Khalid

Kamfani: A.B Zongree

Jarumai: Ali Nuhu, Hafsat Idris, Tijjani Faraga, Magaji Mijin Yawa, Farida Jalal, Hon Isa Umar, Bilkisu Abdullahi da Hauwa Farar lema.

Sharhi: Saddika Habib Abba

 

A farkon fim din an nuna Ahmad ( Ali Nuhu) tare matarsa Aisha(Hafsat Idris) suna zaune lafiya tare da yaransu guda biyu mace da namiji, an nuna Ahmad ma’aikaci ne a karkashin wani kamfani amma yana tafiyarda aikinsa cikin tsoran Allah shiyasa har a lokacin shi ba mai kudi ba ne ko da gida ko mota babu abinda ya mallaka duk kuwa da matarsa Aisha ita macece mai karyar arziki tana son ta ga tana fantamawa acikin dukiya don wasu lokutan ma Ahmad ya kan ranto bashi ya kawo mata ta biya bukatar ta a duk lokacin data nemi bukata ba shida kudi saboda tsananin son da ya ke yi mata amma duk da haka wannan duk bai gamsheta ba na samanta kawai take hangowa. Ahmad yana da maigida a wajen aiki wato shugaban kamfanin kuma ya aminta da shi sosai ana cikin haka sai wataran maigidansa ya umarceshi akan yaje airport ya dakko Maryam ‘yar yayansa wanda ya rasu ta dawo daga ingila Ahmad ya amsa ya tafi ya dakkota sun taho kan hanyarsu ta dawowa Ahmad yaji Maryam tana yi masa gadara da maganganu wanda basu gamsheshi ba kasancewar sa mutum tsayayye baya son raini hakan tasa  zuciya debe shi  ya sauke ta akan titi ya tafi ya barta ran ta ya baci sosai sai daga baya labari ya sha bam-bam ashe Maryam son Ahmad take yi kai tsaye ta nuna masa bukatarta akan zata aure shi kuma zata azurta shi da tarin dukiya amma fa fur Ahmad yaki amincewa sakamakon ko kadan bai ji yana sonta ba kuma yana tsananin son matarsa, Maryam tana ganin haka sai ta bullo ta hanyar matarsa Aisha saboda ta samu Ahmad ya aure ta Maryam ta alkawartawa Aisha zata ba ta gida da mota da kudi naira milyan arba’in da biyar Aisha tana jin haka ta rude tana ganin cewar burinta na zama mai kudi ya kusa cika nan da nan ta nunuwa Maryam cewar ta yarda zata saka Ahmad ya aure ta  amma sai dai kash Aisha fafur bata sami goyon bayan Ahmad ba ko a gidansu mahaifiyarta ma bataso saboda an nuna jajurtacciyar uwa ce, mahaifin Aisha ne mai irin halinta kawai ya amince, Aisha suka din ga dauki babu dadi da Ahmad ya kafe akan cewar shi bazai sai da farin cikinsa ba kuma ba shi da ikon rike mace biyu kuma shi ba zai karbi dukiyar  Maryam ba Aisha ta daga hankalinta ko abinci ta dai na ci har ta fara rashin lafiya sai da Ahmad ya ga tana kokarin mutuwa sannan ya amince ya auri Maryam ba da son ran sa ba.

Bayan auren Maryam da Ahmad Maryam ta cikawa Aisha duk alkawarin da ta yi mata Aisha ta fara fantamawa da dukiya tana harkokinta na kasuwanci ita kuwa Maryam ta zama bora a wajen Ahmad ko kulata ba ya yi kuma duk wata hanya tana bi domin ta faranta masa amma baya gani har sai da tura takai bango ya fuskanci irin wulakancin da Aisha ta keyi masa saboda ta yi kudi kwata-kwata bata da lokacinsa da na ‘ya’yansa kullum bata gidan sai can dare take dawowa idan ya yi magana ta fadamasa bakar magana mara dadi hatta ‘ya’yanta bata basu kulawa komai Maryam ce ta ke yi musu har sun shaku da ita a hankali a hankali. sakamakon kyautatawar da Maryam take yi wa Ahmad ta dauki kanta a me yin biyyayar aure bata kallon tarin dukiyarta domin hatta kamfanin da Ahmad yake aiki na ta ne wanda taci gado a wajen mahaifinta kasancewar tana kasar ingila shine ta barshi a gurin kanin mahaifinta yana cigaba da kula mata da shi shine maigidan Ahmad. amma duk haka bata jin kan ta akan ita wata ce Ahmad yana fuskantar haka sai ya fara sonta ya dai na kyamatar ta cikin lokaci karami ta kwace gidan ita kuwa Aisha tana can harkokin kasuwancinta sai da ta fuskanci Ahmad ya canja mata ya dai na  shiga harkarta komai sai Maryam sai kuma kishi ya motsa ma ta ta fara nadamar abinda ta aikata ta cewa Maryam zata dawo mata da dukiyarta ta bar mata mijinta Ahmad yace ai bata isa ba bakin alkalami ya bushe tunda har ta sai da farin cikinta Aisha ta tayar da rigima har Ahmad ya yi mata barazanar saki, duk da haka amma ta cigaba da nadamar abinda ta aikata.

 

  • Abubuwan Birgewa:

1- kowanne jarumi gurbin da aka sanya shi a fim din ya dace da gurin, kuma jaruman sun yi kokari.

2- Camera da daukar hoto ta fita yanda babu laifi a fim din.

3- Akwai darasi da sako mai karfi acikin labarin.

 

  • Kurakurai:

1- An nuna Ahmad ya ajiye Maryam akan hanya ya yi tafiyarsa yabarta amma sai ga shi an ga sun karasa kamfani sun shigo sun dawo a tare shin  koma wa ya yi ya dakko ta ba’a nunawa mai kallo ba ko kuwa mai ya fa ru?

2- Duk wanda ya dawo daga tafiya har tsahon shekaru a ingila a gida yakamata a gan shi ya sauka amma ba acikin kamfani ba amma sai mai kallo ya ga Maryam kai tsaye kamfani  ta wuce.

3- Shin maigidan Ahmad ba shida iyaline? kodayaushe a kamfani ake nuno shi duk da akwai wasu mas’aloli da ya kamata ace an gansa a gida suna tattaunawa da matarsa musamman akan maganar auren Maryam da Ahmad.

4-Akwai wurin da Aisha suke haduwa da kawarta a titi suna haduwa suna gaisawa kawar ta fara tambayarta a ina mijinta yake aiki? wannan tambayar sam bata kamata ba, domin ba muhallinta bane idan ma zata tambayeta sai a sanya wani abun wanda zai janyo sanadin tambayar amma ba’a tusa tambayar lallai lallai dole ba.

5-Akwai gurin da maigidan Ahmad ya umarce shi da ya je Airport ya dakko Maryam har ya cemasa zai bashi lambarta idan ya je sai ya buga mata amma har Ahmad ya tafi maikallo bai ga ya bashi lambar ba kuma aka ga ya tafi ya dakko ta shin Alhajin mantawa ya yi? kuma Ahmad ta yaya ya sameta a Airport din suka hadu tun da basu san  juna ba?

6-An ga Maryam ta bawa Aisha gida har iyayenta sun je sun gani kuma ga dukkan alamu ta koma gidan da zama ne amma daga bisani sai aka ga Aisha suna zaune a wani gidan daban tare da su Maryam har ma da mijinsu Ahmad shin ta yaya hakan ta kasance ko Aisha gidanta ta bari ta koma can?

 

  • Karkarewa:

Fim din akwai darasi, amma babu cikakiyar al’adar Bahaushe a ciki. Allahu a’alamu!


Advertisement
Click to comment

labarai