Connect with us

TATTAUNAWA

Obasanjo Ya Dade Yana Kulla Wa Arewa Makirci —Dakta Bature

Published

on


Shugaban kungiyar ‘yan kasuwa ta Nijeriya Dakta  Bature Abdul’aziz ya fasa kwai dangane da makircin da tsohon shugaban kasa Chief Olusegun Obasanjo ya dade yana kulla wa Arewa. Sannan ya ce zai yi wannan bayani ba don ya bata siyasar Obasanjo ba, kuma ba don ya bata masu binsa ba.Sai dai a  fahimtarsa, zai bayyana irin yadda yake a Nijeriya, da kuma yadda ya tafiyar rashin kirki.

Daga Sabo Ahmad, Abuja

 

Idan ba ka sani ba, ka san kadan daga abin da na sani, a Nijeriya, Obasanjo ya shiga mulki 1976, ya rike an yi alkawari za a ba da mulki 1979, to an ba da mulkin 1979, da aka ba da mulkin 1979 Shagari ya karba.

Tun da Shagari ya karba, Obasanjo yake yawo yana cin mutuncin Arewa, yana kuma zagin mutanen Arewa, yana kuma bata ci gaban Arewa, da kuma kowace irin kafa da ya san Arewa za ta yi mata amfani. Ya manta hawan mulkinsa na farko, ‘yan Arewa ne suka dora shi, amma ya zo daidai lokacin mulikin Shagarin nan, yana fada yana zagin su Sardauna kiri-kiri ba boye wa yake yi ba, kuma su Sir Abubakar Tafawa Balewa da sauran manyan mutanenmu da aka kashe a 1966, kuma abin mamaki sai yake yawo yana cewa duk wadannan mutanen namu da su muke takama da su har zuwa yau, kowanne dan siyasa a Arewa da su yake alfahari su Sir Ahmadu Bello, wai yana cewa Chukwuma Nzebu da aka kashe shi a yakin basasar Nijeriya, aka kashe Chukwuma Nzebu 1969, yana cewa kashe Chukwuma Nzebu wallahi babbar hasara ce, kuma shi a ganin sa, Chukwuma Nzebu, yana rantsuwa, cewa ya fi su Sir Abubakar Tafawa Balewa, to wannan kiyayya da me ta yi kama?

Wadanda suka kashe mutanen da miliyoyi suke amfana, wanda shi ma ja’za’in kisan da ya yi ya koma kansa, me Obasanjo ya gani yake wannan cin fuska namu? To a takaice dai ya ci gaba da irin wannan maganganun ne, ya ci gaba da maganganun da babu dadi. Allah da ikonsa, cikin alkwarin Allah Obasanjo kuma sai ya sake dawo wa ya jinginu da Shehu Musa ‘Yar Aduwa, wannan dalili sai Allah ya kaddarawa Shehu Musa ‘Yar Aduwa rasuwa, sai ya zama kuma Obasanjo shi ne shugaban Nijeriya, a wannan lokacin fa, shi ne shugaban Nijeriyar, amma a wannan lokacin fa amma sai ya juya ka’in da na’in ta ina zai cuci Arewa, ta ina zai dakushe Arewa.

A takaice,  yadda ya zo ya tarar da projects din nan da za a jawo ya zo Barno, wanda za a hade shi da teku, Obasanjo ne na farko ya fara dakile shi da ya dawo, kuma, Obasanjo ya afka kan cewar wato yana goyon bayan ko yana assasa wuta sai an yi Afuta Panel bayan ya dawo, tsammaninsa a Afuta Panel din nan za a binciko laifin su Sardauna ko za a binciko laifin tsofaffin ‘yan Arewa wadanda suka yi wancan lokaci a ci masu mutunci, wai a yi masu yadda aka yi a South Africa a yi masu haka. To ai tsarin South Africa daban, tsarin Biafara daban.

Sannan ya zo yana ta kawo abaibai, ya afka kan kadarorin Nijeriya, , wasu kadarorin ma manya a lokacinsa, wasu kadarorin ma tun daga Turawan mulkin mallaka suke, ya zo ya afka kansu ya dinga gwanjon su yana sayar da su, duk abin da ka sani mai daraja ya sayar da shi, a kan ko kasarsa can jihar yamma akwai irin wadannan abubuwa da aka mallaka daga Turawan mulkin mallaka bai sassai da nasu ba. Suka dinga saida su ko kashi 5 daga cikin dari na kudin abin ba a biya, har yanzu ana bin bashi suna nan an san su a Nijeriya, ya zo kuma bayan ya yi wannan, a Afuta Panel bai samu sa’ar da yake so ba, sai ya zo kuma a tunaninsa ya zai zama wuka da nama ko kuma ya zai zama boss oberall na siyasar Nijeriya ko ba ya ciki? Ya zo ya tayar da kokarin ganin cewar mutanen middle belt sai ya yi  kokarin an tada fitine-fitinen nan na fadace-fadace, a lokacinsa aka fara zafafan fadace-fadacen nan, kuma muna tunanin ‘yan wadannan jihohi guda uku ko guda hudu ya zamana cewar, wato a dabararsa, wadannan jihohi uku zuwa hudu wato ya karkata tasirin siyasar wadannan jihohi hudu ya koma kudancin kasa, wato yadda in zabe ya zo jihohin kudu suna da karfin jiha ishirin da daya ke nan, wato bai ci nasara ba, lokacin da Buhari ya zo, guguwar Buhari ta tafi da wannan shiri nasa, ta kakkarya shi.

Kullum su dinga nuna kansu su ba a Arewa suke ba, wannan wutar fitina shi ya fara rura ta, shi ya fara rura ta ta ci gaba har ya zuwa kafin saukarsa, ban da ‘yan Arewan ne ma suka dora shi hawa na biyu, amma tenuwarsa na biyun ma da zai koma sai da ya durkusa gwiwarsa bibbiyu a gaban dan Arewa a kan ya yi masa sutura ya yi masa rai, ya bar shi ya yi tenure ta biyu.

Atiku Abubakar ya bar shi ya yi tenure ta biyu, to a sannan ne fa ya samu damar irinsu Ajekutan nan, ya samu damar ya ya za a yi ya dakile Ajakuta, aikinta ya zama kwandam wato a wannan lokaci, shugaban Rasha, Bladimir Putin, sai da ya ce tun da Rasha ce ta fara gina ainahin wannan waje na Ajakuta,  in Nijeriya ta yarda a ba su dama ba sai an sake biyan wani kudi ba, su a wajen su za su mai da aikin ya koma kamar yadda aka yi nufi, ita kuwa wannan ma’aikata idan ba ku sani ba ‘yan Nijeriya da a ce ta ci gaba da aiki, amfanin da za ta yi mana a Nijeriya, to masu zaginmu ba mu da man fetut wata kila da sun samu saukin zagin namu domin wannan karfe na Ajakuta da ake debo shi daga kasar Allah subahanahu wa ta’ala yana iya yin kowane irin karfe ake amfani da shi a Nijeriya, shi ya sa yadda man fetur yake da kasuwa a kasuwar duniya shi ma haka yake da kasuwa wanda ‘yan Nijeriya ba za mu manta ba yadda rodi yake da kasuwa a kasuwar duniya ake yin sa a Jos da Oshogbo da Katsina.

Wadannan ma’aikatu sai da suka wadata Nijeriya har wajen Nijeriya da rodi, kuma rodin mu ainihin ya fi na Ukraine karfi da aminci amma wannan da yake ya san abu ne wanda za a yi shi a Arewa, shi ba don komai ba kada ya zama Arewa ta fito a duniya ma an san ta, ban da ma tattalin arziki da zai bada dama a gina,  ya dakile. Suka zo suka matsa ya dai za a yi su rusa Arewa, daga cikin irin wadannan mutane da muke zargi na tabbata pressure din da ake yi wa Arewa don ta samu wargajewa amma rashin zaman lafiya babu shakka shugaban kasa Buhari suka yi dogon bincike za a gano ko su waye, ko Farfesa waye kuma ko su waye ke cikin wannan za a gano ko su waye.

Muna rokon wannan gwamnati ta Buhari, yadda kafin tenuwar farko zuwa tenure ta biyu a karkade wannan ciwo da yake damun Nijeriya yadda wadanda ba su samu yadda suke so ba kullum suke kunna wutar fitina. Saboda haka bincike zai binciko su. Mai girma shugaban kasa, wadanda suke kunne-kunnen nan, wadanda suka yi  rub-da-ciki ne a dukiyar Nijeriya, kuma su suka debi dukiyar Nijeriya fiye da kowanne lokaci da aka debi dukiyar Nijeriya. Saboda haka ya kamata ayi maganinsu. Don kasa ta zauna lafiya, tattalin arzikinmu ya bunkasa.


Advertisement
Click to comment

labarai