Connect with us

ADABI

ADABI: Taba Ka Lashe Labarin ‘Mugun Jigo’ Na Khadija Abubakar

Published

on


Tare da Adamu Yusif Indabo

07038339244

[email protected]

Taba Ka Lashe wani fili ne da mu ka samar wa makaranta wannan shafi na ADABI A YAU, wanda zai rika zuwa lokaci-lokaci, don kawo mu ku gajeren kirkirarren labari ko kuma tsakure daga cikin littattafan fasihan marubutanmu, saboda fadarwa da kuma nishadantar da ku.

A yau filin namu zai fara ne da kawo mu ku labari mai taken Mugun Jigo; labarin da fasihiyar marubuciyar da ta ke tashe a duniyar rubutun yanar gizo, wato KHADIJA ABUBAKAR ALKALI, wacce aka fi sani da Khadija Candy ta rubuta.

Khadija Candy mamba ce ta kungiyar Nagarta Writers Association, sannan ita ce marubuciyar labaran Lamarin Duniya, Mairo, Babbar Jaka, Ban Zata Ba, Saifullah Ko Habibullah?, Khadijatu, Ta Ki Zaman Aure, Iyalin Mijina, Babban Goro da dai sauransu. Ga dai labarin na Mugun Jigo. A sha karatu lafiya:

 

  • Mugun Jigo

Tun tashi na ban taba ganin Umma cikin farinciki ba, a koda yaushe Baba na cikin musguna mata yake, bata ta6a yin wani abu ya yaba mata ba, Gashi duk wani hakk’i nata da Allah ya ďora masa ba yayi mata shi. Man shafawa sai dai ta shafa manja idan zatayi wanka sai dai ta siya omo tayi wanka dashi.

A gaban kowa zai iya rufeta da faďa ya ďinga faďa mata munanan kalamai wadda da a’ce ba mahaifina bane bai isa ya faďa mata haka na kyale shi ba.

Sam ba ya ganin tausayinta idan ta samu yan kuďin ta ya kar6e har wata rana ya kai ga tayi sa’insa dashi wadda sam ni ban jidaďi ba, ina ma a ce idan iyaye zasuyi faďan su zasuyi a idan mu ’ya’ya ba za mu gani ba.

Mahaifina wani irin kalar mutun ne wadda mu kanmu bama jindaďinsa har ta kai nima bana son ďaga ido na kalleshi, k’anne na da yake su kanana ne sai suka rik’a ganinshi wani azzalumin mutun.

Yau ma kamar kullum Mahaifiyar mu na kwance, tana murk’ususun ciyon zuciyar da yake damunta ko kuma nace hawan jini wadda kashi casa’in da tara zan iya cewa Baban mu ne ya saka mata shi.

Bai ta6a tausayin ciwon nata ba, ba ruwansa da siya mata magani, kullum cikin shan jik’e-jik’en ita ce ta ke, idan tayi masa maganar ya siya mata magani sai ya rufe ta da faďa wai da a’ce Namiji ta haifa ai shine zai nemo ya kawo mata, ya ďauki nauyinta da nashi. Ni har yanzu a abunda na kasa ganewa shine, shin ita haihuwa mace ce take ba kanta? ko kuma Allah ne yake bata? Mu shida Mahaifiyar mu ta haifa duka mata, Shin yin kanta ne ko na Allah? Mi muka aikata mu Y’ay’a mata da wasu mazan basa son a haife mu? Na daďe ina yima kai na waďannan tambayoyin amman har yanzu ban samu amsar su ba.

“Sannu Umma,” na ce da ita ina share hawayen da suka zu6o a fuskata na tausayin halin da take ciki, kai kawai ta ďaga min tana dantsar baki alamar tana jin ciwon sosai.

“Hafsatu…” Da wahalalliyar murya ta kira irin ta marasa lafiya. Da sauri na matso kusa da ita na amsa cike da ladabi, “Na’am Umma sannu”

Hannaye na ta kama ta rik’e da wani irin k’arfi tana faďin, “Hafsatu mutuwa zanyi Allah kai ne Allah”

Nan hankali na ya tashi, sai kukan da nake ya k’aru cikin rawar murya na ce, “Dan Allah Umma ki daina faďan haka cuta ba mutuwa bace in’sha Allahu za ki tashi.”

Kai ta girgiza min, tana unk’urin tashi zaune ta ce, “Allah yayi miki Albakar ya shirya min ku gaba ďaya ďan Allah ki rike Y’an’uwanki ku haďa kai”

Jingina ta nayi da jikina ina kuka da fadin, “Umma zaki tashi Dan Allah ki daina faďin haka.” Ganin shakk’uwa na kokarin rufeta yasa na kwantar da ita cike da tsoro ina fain “Bari na kira Baba.”

Rikke ni tayi a’lamar karna tashi, A nan na koma na zauna ina kuka. Bata daina shakk’uwar ba, sai ma k’aruwa take, numfashinta nayin sama kamar zai fita, ganin hakan yasa na tashi, Jiki na rawa na nufi gurin ruwan na ďe6o a kofi na nufo ta, kamin na karasa naji tana kalmar shahada. Daga inda nake na saki kofin na amsa da,

“Muhammadu rasullullahi sallalahu a’laihi wassalam.”

Daga nan ban sake sanin inda nake ba. Dana farka har an kawar da ita, Ina zaune cikin Y’an’uwa na sai faman kuka muke ni dasu, jama’a na bamu hak’uri, ashe kuka shine yake zuwa da kansa ba sai an kirashi ba, kuka na rik’a jin yana zo min ta ko’ina, har akayi amsar gaisuwar aka gama ban saka komai a baki na ba.

Ranar da Umma ta cika wata biyu da kwana tara da rasuwa Baba ya aike ni cikin dare siyen baturin rediyo, Babu shi a shagon dake kusa damu, Nasan idan ban siya ba wata fitinar ce dan rufe ni zaiyi da faďa, hakan yasa na nufi wani Shago dake k’arshen unguwar mu,

Cikin rashin sa’a shima ban tararda shi ba. Ina juyowa naji an kira ni,

“Hafsat.” Da tsoro na juyo ina kallon gurin da aka kira sunan nawa, daker na ina hango shi zaune saman tebur cikin duhu da alama shaye-shaye ya ke yi.

“Na’am Faruk folis.” Na kirashi da sunan da lowa a unguwar mu yake kiranshi, Dariya yayi ya taso rik’e da bindigarsa ya nufo ni, “Ashe kin gane ni.”

“Eh na gane ka.” Ina ba shi amsar na juya da sauri da nufin tafiya, sai kawai naji an rik’o Hijabi na, fisge hijabin nayi cike da matsifa na ce, “Sake ni karka sake rik’e min hijabi.”

Kamar mai jira sai kawai ya fisgoni ya haďeni da bingarsa yana fain, “Wa kike yima tsawa?”

Kallon bindigar nake ina fain, “Ba kai ba dan Allah yi hak’uri.”

A nan ya lura da tsoron bindigar nake, sai kawai yaja Hijabi na ya nufi wani lungu dani sai maimaita maganar yake, wai shi zanyi ma haka? Ni kuma Ina ba shi hak’uri. Sam bai saurare ni ba har sai da ya aikata mugun nufinsa na alfasha a kaina (Fyade).

A wahale na iso gida, Ina wani irin kuka ba sauti. Rufe ni Baba yayi da fada ba daďewar da nayi yake ma faďa ba rashin siyo batir din da banyi ba yake ma faďa. bai tambayeni miya tsayar da ni ba, bai aika wani ya nemo ni ba bai damu da duk abunda zai same ni ba shin wane irin Uba ne wannan?


Advertisement
Click to comment

labarai