Connect with us

MAKALAR YAU

Bakon Marubuci: Illolin Rashin Adalcin Da Ake Aikatawa

Published

on


Idris Aliyah Daudawa [email protected] 08065683849

Adalci wani abu ne dake bayyana da ayi ma kowa yadda ya dace, gwargwadon yadda ya dace a yi, ba tare da nuna wani bambanci ba na  domin wani daga can yake, ko don ba da nan yake ba, ko kuma don harshensu daya, domin ita  mace ce , sai a yi mata abin da ma ya wuce  a ba ta, shi kuma namiji ai ta yi ma shi na mujiya kawai. Ko mun fito daga gari daya ne, mazabar kansilanmu daya, Karamar Hukuma daya, jiha daya, ko kuma ai daga sashe kaza da kaza muke, bari na dan daga ma shi, addinmu daya, duk idan ana maganar adalci tsantsar shi, bai kamata  a kalli daya daga cikin wadannan abubuwan ba. Idan kuma aka ce sai an yi hakan to sam bai dace ba, ba kuma haka ya kamata a rika tafiyar da al’amura ba, saboda komai nada nasa tsarin da za a tafiyar da shi, ba hakanan ba, a yi ta yin abubuwa kara zube, idan za a yi ma wasu bangare a bude idanu domin a kalle su sosai, idan kuma za a yi ma wancan bangaren sai kawai a rufe idanu domin bama a son a san ko su wanene su.

Idan aka kalli gida a matsayin wurin da za a fara duba adalci yadda yake farawa, saboda can ne ake fara komai na rayuwa, can ne mai gida zai fara al’amarin yadda ake adalci, tun yana ango a matsayinsa miji, ita kuma matar tana amarya, haka abin zai fara har dai ta kai ga an fara samun karuwa ta haihuwa, tun ana uku sannu a hankali har watarana a kai ga kasancewa ‘ya’ya sun samu. Sai dai kuma maganar yadda za a tafiyar da shi gidan. Daga nan ne kuma sai a fara maganar yadda za a yi hidimar ‘ya’ya wadanda suke maza da mata ne, anan bai kamata shi maigida ya rika yin rashin adalci ba, a tsakanin ‘ya’yansa, musamman ma ko a cikin maza, ya nuna bambanci ke nan  wanda rashin adalci ne. Idan ya ci gaba da nuna wannan halayyar hakanan gidan kuwa zai kasance a samu rarrabuwar kai tsakanin ‘ya’yan na sa, wanda idan ba sa’a aka yi ba, gidan zai iya zama wani wuri ne na shuka kiyayya tsakanin ‘ya’yan na shi. Wannan ya nuna ke nan tamkar gida ya baci ke nan, idan Isa ya ce a ba shi wani abu sai a ce ma sa wani abu nan da nan za a yi ma shi, amma kuma idan Sallau ya nemi da a ba shi  wani abu ko kuma a yi ma sa yadda aka yi ma Isa, sai a fara fada ma shi maganganun da basu kamata a fada ma shi ba. To wannan tun a gida ma ke nan  an fara takin saka a dalilin yadda mahaifi yake yi, irin hakan sai su ‘ya’yannan su kai ga nasu ‘ya’yan har ma a kai ga yin jikoki, abin har ya kai ga yin gaba, wadda za ta dade ana yi. Sai maganar aure idan ba sa’a ka yi ba nan ma din a kan taba rashin adalcin wanda shi ma kan kasance, sanadiyar yarinya ta tafi uwa duniya karuwanci, dalili kuwa, wasu iyaye inda su kan yi nasu rashin adalcin shi ne, lokacin aure wasu sukan duba Naira ce ba maganar hali ba, koda kuwa, shi ya mai son yarinyar tasu da aure ne yake. Ba maganar nagari suke ba, su babbar nagarinsu ita ce Naira, farin cikinsu ke nan, koda kuwa ace shi yafi kowa munanan ayyukan ashsha, su ba wannan ya dame su  ba, da zarar dai za su yi ido hudu da Naira. Daga karshen idan ita yarinyar ba mai daukar irin halin bace, sai ta shiga uwa duniya, wanda kuma su iyayen  nata suna da kamisho, akan dukkan abubuwan data aikata, saboda ai basu zaba mata miji nagari ba, sun tafka mata rashin adalcin ne.

Idan aka kammala da gida sai kuma makaranta saboda nan ma wani wuri ne da wasu marasa tsoron Allah ke nuna rashin adalci, idan ka dauki Malaman makaranta, sune ke amfani da ita wannan kalma, saboda su yi yadda suka ga dama da dalibai, badan komai ba sai saboda sun san cewar su a matsayin wata matakala ce wadda daliban ke bi, su samu tudun dafawa. Don haka sai yadda suka ga dama za su yi, wasu daliban ba wai saboda ba su da kokari bane ake kada su jarabawa, ana yi masu rashin adalci ne musamman ma ganin cewar, su daliban da akan yi ma haka, ba su da wata hanya da za su yi maganin sa al’amarin, sai dai ko  su yi Allah ya isa, ko kuma suce ai ba komai. To irin wadannan daliban da ake danne ma hakki a dalilin rashin adalci, idan ba sa’a aka yi ba, ya kasance su tun suna ‘yan yara ba wai an yi masu kyakkyawar tarbiyya, a gaba irin sune ke haduwa  da wasu  da suka shiga cikin hali irin nasu, su hada kansu suma su kasance ma al’umma  alakakai a rayuwar su. Yarinya wata kuma idan ba sa’a aka yi ba, sai a nemi  bukatar sai an yi aikin banza da ita daga baya kuma a ba ta damar wucewa da karatu zangaya ta gaba, wadda kuma bata bada hadin kan hakan ba, sai ta kasance ta baya ga dangi a makaranta. Wani malamin shi al’amarin anshi ma yana da ban tsoro dalili kuwa a rashin adalcin da wasu kan tafka sai ya kasance, wadanda basu kamata su wuce zangaya ta gaba ba, sai watarana a ce ai sun wuce shekarar karatu ta gaba.

Shi al’amarin ai bai tsaya a makaranta ba da gida kadai , sune wuraren kadai da akan nuna shi rashin adalcin ba, saboda kuwa idan aka leka yadda ake  daukar ma’aikata, nan ma abin bai canza zane ba, saboda kwamacalar da akan yi, na rashin adalcin daukar ma’aikata. Wani abin haushi sai a buga sanarwa a jaridu ana bukatar daukar ma’aikata, wasu suna bata lokacinsu da kudinsu, saboda su samu halartar ita yin jarabawar ko kuma ganawa da masu neman aikin, bayan kuma su wadannan masu shirya ita jarabawar ko ganawa da masu neman a dauke su aiki, sun san iyakar mutanen da za a dauka, amma maimakon su yi ma wasu  adalci, sai sun sa , sun kashe kudadensu da dukiyoyinsu, amma sai duk kidan nasu ya kare a jinjina.

Ana dai bata ma wasu lokaci ne  kawai bayan an san ko mutum nawa ne za a dauka, ba kuma dole bane sai sun zo, sun rubuta jarabawa bas u wadanda za a daukar, irinsu ‘ya’yan Mowar an dade da basu offer din,(Takardar Shaidar Daukar Aiki) ko sun cancanta, ko kuma basu cancanta ba. ‘Yan Borar kuma sai su tafi da iyawarsu can , ba abin da ya damu kowa. Ta haka ake daukar wasu aiki saboda alfarmar data sa aka ki yi ma wasu adalci na  a, basu dama saboda suma sun iya , sai kuma an gwada akan san na kwarai. A basu aiki su kasa yin komai, har ma a kai ga gane shin me ke faruwa ne, dan haka sai su yi ta kwaba shirme a  wajen aikin, saboda daman an daukesu ne ba tare da sun yi jarabawar da kuma ganawa da wadanda za a dauka aikin ya kamata su yi.

Maganar Hukumar shirya jarabawar shiga jami’oi da kuma sauran manyan makarantu (JAMB) wannnan shekarar fiye da dalibai miliyan daya da rabi ne, suka dauki jarabawar, idan kuma ba sa’a, aka yi ba, zai yi wuya a dauki rabin miliyan da ba su damar zuwa jami’oi da sauran manyan makarantun ba, wannan ya nuna ke nan, sauran kamar ba a yi masu adalci ba ke nan, ga kuma yaudara saboda kuwa ai ita Hukumar ya dace ta san yawan daliban da za su samu damar shiga makarantun, don haka me kuma zai sa a sa wasu su bata kudadensu ta wajen sayen fom da kuma rubuta ita jarabawar da kuma lokaci , bayan kuma an san daga karshe ba daukarsu za a yi ba.

Tsakanin ita Hukumar zabe da kuma jam’iyyun siyasa sun san irin rashin adalcin da sukan yi wa al’umma, a dalilin rashin tsayar masu da wadanda suke son su zaba, maimakon haka ma, sai a basu wanda zai ta gasa masu Aya a kan Kunba , ba yadda zasu yi. Don haka ya dai kamata wai auren na gida yarinya ko bata ci abinci ba ta ga Mama da Baba, duk al’amuran da nayi bayani akansu, ana amfani da rashin adalci, wanda kuma daga karshen idan abin ya kai karshen mizanin shi, to abin fa ba wani kyau zai yi ba, a kula da yin adalci , a kuma guji yin zaluci. Saboda Allah Subhanahu wata’alah mahillancin mu ya yi koyi da ayi  adalci da kuma hani ga yin zalinci , saboda shi adali ne.

 


Advertisement
Click to comment

labarai