Connect with us

TATTAUNAWA

A Gaskiya Tun Ina Karami Ina Sha’awar Harkar Film —Isa Abubakar

Published

on


Daga Bashir Isah

Sunansa Isa Abubakar Karai, matashin dan-jarida, dan wasan kwaikwayo kuma mawaki. Nan da karshen wannan watan matashin ke sa ran gabatar wa al’umma da sabon kundin (album) wakokin bidiyo da ya shirya don nishadantarwa da fadakarwa. “DAN SAMARI” sunan album din nasa kenan.

Hakika matashin ya dauki lokacinsa tare da natsuwa wajen tsara wannan aikin nasa ba don komai ba sai don amfanin al’umma baki daya. Isa Abubakr Karai dan asalin karamar hukumar Keffi ne a Jihar Nasarawa.

Da yake amsa tambayar wakilinmu game da abin da ya kwadaita masa shiga harkar rawa da waka da wasan kwaikwayo, matashin ya bayyana cewa, “A gaskiya tun ina karami ina sha’awar harkar film, har na zo na ga harkar ma ba wai sha’awa ce kadai ba babbar sana’a ce wadda mutum zai iya  dogara da ita domin ya rike kansa har ya taimaki ‘yan’uwa da abokan arziki”.

Karai ya ci gaba da cewa, “Amma duka wannan sai ka hada da rawa da waka ta yadda za ka kara burge masoyanka, domin idan ka lura za ka ga mutane suna son kade-kade da raye-raye, wannan shi ne makasudin shiga wannan harkar”.

A cewar matashin, ya soma wannan harka ne tun a shekara ta 2007 lokacin a karkashin wata kungiya mai suna  Kofar Hausa Film Production Keffi da ke Jihar Nasarawa, lokacin ana koyar da rawa da waka da kuma wasan kwaikwayo. Ya ce a wannan lokacin ne ya soma, tare da zuwa bita rihazal sau biyu a duk mako, wato Asabar da Lahadi.

Haka nan, ya ce yana sa ran kaddamar da albon din “Dan Samari” ne ya zuwa karshen watan Afrilun da muke ciki da yardar Allah. Saboda a cewarsa, masoya sun mastu su ga an saki wannan kundi don su je su mallaka, amma komai sai a hankali.

Wanna cikin wannan wata na Aprilu da yardar Allah, domin masoya sun zaku suga an fitar dashi kuma komai sai a hankali,domin ba abu ne wanda zaka yi gaggawa ba.

Shin ko matashin ya taba fitar da wani albon dinsa kafin wannan lokaci? Tambayar da Karai ya amsa kenan da cewa, “A gaskiya wannan shi ne albon dina na waka na farko da zan fitar. Amma a dangaren film, na yi fina-finai da suka hada da; Gwarzon Shekara da Babban Kwala da kuma Rayuwar Dan Adam. Film din Rayuwar Dan Adam kusan shi ne film dina na farko da na fara da manyan jarumai irin su Sadik Sani Sadik da Tanimu Akawu da Rabi’u Rikadawa da dai sauransu”.

A karshe, Isa Karai ya ce, ya yanke shawarar sanya wa sabon albon din nasa suna “Dan Samari” ne duba da yadda masoya ke zaton shi wani dattijo ne idan suna jin muryarsa a rediyo kasancewarsa ma’aikacin gidan rediyo, amma kuma idan suka hadu sai su ga ashe matashi ne mai jini a jika. “Wannan shi ne ya karfafa mini gwiwa wajen shirya wannan albon din na kuma sanya masa taken “Dan Samari” domin an dan cashe da rawa sosai, abin dai sai wanda ya gani”, in ji Isa Abubakar Karai.


Advertisement
Click to comment

labarai