Connect with us

RA'AYINMU

Game Da Sabon Tsarin Biyan Kudin Lantarki Na MAP

Published

on


Ba tare da wata matsala ba, sabuwar hanyar biyan kudin lantarki da aka gabatar na, ‘Meter Asset Probider, MAP, zai maye gurbin tsohuwar hanyar da ake bi ta, tsarin CAPMI, tun daga ranar 3 ga watan Afrilu. Hukumar kula da lantarki na Najeriya, NERC, a matsayin na mai kulawa, dole ne ya sanya shi zuwa da wannan sabon tsarin na, MAP, saboda rashin nasarar da wancan tsarin na, CAPMI wanda ya shekara shida ana amfani da shi wajen kiyaye lissafin kudin lantarkin da mabukata ke sha a Nijeriya.

Ta hanyar wannan sabon tsarin na MAP, dukkanin Kamfanonin raba hasken lantarkin, DisCos, dole ne su watsar da tsarin da ake amfani da shi a baya na, CAPMI kuma su karbi sabon tsarin na, MAP a cikin kwanaki 120, da kaddamar da shi, tun daga ranar 3 ga Afrilu. Yayin da tsohon tsarin na CAPMI ya kasa cin nasara wajen biyan bukatun masu amfani da hasken lantarkin, an zo da wannan sabon tsarin ne na MAP, domin kiyaye hakikanin abin da masu amfani da hasken lantarkin ke sha. Wanda ake sa ran samun nasararsa a cikin shekaru uku, wanda ake sa ran zai magance kudin lantarkin da kamfanonin raba lantarkin ke tsugawa.

Abin farin ciki ne cewa, kamfanin kasa mai kula da hasken lantarki ya ji cewa, ya zama dole a yi watsi da tsarin CAPMI wanda babu tabbacin gaskiya, wanda ya baiwa kamfanonin raba lantarkin, DisCos duk wasu uzurorin da suke buƙata wajen tsuga wa abokanan huldan su kudI ta hanyar lissafin ka, na kuɗadan da ya kamata su biya. Ayyukan rashin daidaituwa da suke tattare da tsohuwar hanyar biyan kudin lantarkin ta, CAPMI sun tilastawa mutane fiye da miliyan hudu yin gudun hijira daga cikin DisCos 11 na kasarnan zuwa matakan mitar dijital da aka shio da ita kafin shekarar 2012.

Kimanin kashi 50 ne na masu amfani da hasken lantarkin kamfanin lura da samar da hasken lantarkin, NERC, ya ce, ke amfani da mita, sauran rabin masu amfani da hasken lantarkin kuwa, sai abin da kamfanonin raba lantarkin, DisCos,  suka ga daman yanka masu amatsayin kudin wutar lantarkin da suka sha.misali, a Abuja da ma sauran wasu wuraren na cikin kasarnan, mazauna gidajen da ke da dakunan kwana biyu sukan biya kimanin Naira 4000 ne a duk wata ta hanyar amfani da mitocin dijital, sa’ilin da kwatankwacin su marasa Mitan ta dijital kamfanonin raba hasken lantarkin na DisCos, kan dora masu biyan kimanin Naira 22000 a kowane wata da sunan kudin wutan da suka sha.

Wannan shi ne irin matsananciyar cutan da ke cikin biyan kudin wutan ta hanyar kintace. A sa’ilin da kamfanonin na DisCos, ke nu na tsada a matsayin dalilin da ya sanya suka kasa sanyawa abokanan huldan na su mitocin, a wancan tsarin da ya gaza na CAPMI, wanda ya amince da masu amfani da wutan su sayi mitocin da kan su, wanda kuma za su biya su ne sannu a hankali a duk lokutan da suke sayen katin hasken lantarkin, tare da ruwa na kasha 12 a shekara, amma abin takaicin ga milyoyin masu amfani da hasken lantarkin shi ne, sun biya kudaden mitocin amma wata da watanni ba su same su ba. Ana nan kuma ana masu cajin ka ta hanyar tsuga masu kudi. abin farin cikin shi ne zuwan wannan sabon tsarin na MAP, duk zai magance hakan. Kowa zai sami mitan sa.

Hakanan kuma ita wannan sabuwar hanyar biyan kudin ta MAP, hakkin sanya mita ya tashi daga kan kamfanonin na DisCos, yanzun ya koma hannun wasu kamfanoni ne na daban, sune za su sanyawa masu amfani da hasken lantarkin mitocin sune kuma za su kula da gyaran su a duk lokacin da wata matsala ta taso. A wannan sabon tsarin na MAP, dukkanin mitocin da suka lalace, tilas ne a gyara ma mai amfani da ita ko kuma a sake ma shi wata sabuwa a cikin kasa da ranakun aiki biyu, sai dai in mai amfani da itan ne ya lalata ta da kanshi.

Idan kuwa har aka gaza gyara ma shi mitan ko kuma a sake ma shi wata sabuwa kar a cikin lokacin da aka kayyade, to zai biya kudin wutan ne a bisa abin da ya saba kashewa na kudin wutan a watanni uku baya. Hakanan idan mai amfani da mitan ta MAP, ya yi kaura daga inda yake ya koma wani wajen, tilas ne ya sanar domin a canza ma shi rajistan sa tare da kudaden da yake bi ko ake binsa a tsohon wajen da ya baro. A wannan tsarin na MAP, masu amfani da lantarkin da suka zabi su rika biyan gaba, tilas ne a sanya masu mitocin su a cikin kwanakin aiki 10 daga ranar da suka biya kudin.

Baya gas aukake wa kamfanonin na DisCos, wannan sabuwar hanyar za ta sa kamfanonin raba hasken lantarkin su kara mayar da himman su wajen sauke nauyin da yah au kansu. Wannan kuma sabuwar hanyar ta MAP, za sa kara samar da ayyukan yi, sannan kuma mutane da dama za su ji cewan da su ake yi a harkar samar da hasken lantarkin.

A namu ra’ayin, tare da mummunan yanayin da muka shiga a baya zamanin CAPMIN, kamata ya yi ma’aikatar Samar da hasken lantarkin da kuma hukumar samar da hasken lantarkin, NERC, su dukufa wajen tabbatar da ganin ba a bar wata kafa ba irin ta baya wacce kamfanonin na DisCos, za su bi wajen cutan al’umma.

 


Advertisement
Click to comment

labarai