Connect with us

TATTAUNAWA

Burina Gina Cigaban Al’ummar Dakata –Hon. Umar Otu

Published

on


Alhaji Umar Alhassan, shi ne zababben Kansilar Mazabar Dakata dake karamar hukumar Nassarawa ta Jihar Kano. A karkashin jam’iyya mai mulkin kasa wato (APC) a tattaunawar da yayi da Sani Tahir Kano.

Masu karatu za su so ka fara da gabatar musu da kanka…

To Alhamdulillah da farko sunana, Umar Alhassan wanda akafi sani da Umar Otu, an haifeni a Dakata a shekara ta alif (1972) nayi karatun firamare da sakandire duk a unguwar dakata daganan kuma sai na tafi Collejin Audu Bako makarantar gidan gona wato (Audu Bako College of Agricultural) inda nai aiki a kamfanin gaskiya tedtile na tsawon shekara tara (9)kuma duk da haka ina harkar siyasa yanzu kuma cikin yardar Allah na kasance nine kansila na mazabar dakata.

 

Ya a kai aka samu kai a harkar siyasa?

Na samu kaina a harkar siyasa ta hannun mai gida na Alhaji Nasiru Dan Nasi wanda a shekara ta 1999. A lokacin da aka fito da jamiyyar (PDP) shine ya jani wannan harka inda yasa kani a shugaban matasa bayan anyi zabe inda nayi shekara shida (6). Daga nan kuma nazo nayi kuma na dan huta saboda wasu al’amura a chanjin mulki daga nan kuma bayan an kirkiro jamiyyar (CPC) farko duk da haka na tayin siyasa har takai takawo a yanzu halin da akeciki. a shekarar (2011) inda na zama shugaban gashi anyi zabe anyi nasara kamar wanne aikace-aikace kake burinyi?

To! Dagaske muna da kudirorinka da burinka da muka saka a gaba wanda muke ganin cikin yardar Allah, akwai mataki guda uku (3) wadanda muke so mutaka ko mucinmma a wannna mazaba tamu mai albarka da farko a kwai harkar ilimi, da lafiya da kuma samarwa da mutane ayyuka wato.

Dogaro da kai wannan sune  babban burinmu koda yake zaniya fada cikin taimakon Allah da taimakon shugaban karamar hukumarmu wato Dr. Lamin Sani mu ba’abunda zamuce mai sai godiya domin ya bijiro mana da ayyuka cikin kankanin lokaci.

Wanda ina alfahari a mazabar Dakata na gyara rijiyar birtsatse guda uku, na gina rumfunan masallatai da kae sallah na nemawa yara wadanda suka fadi a jarabawar kwalafayin harmutum takwas (8) kudin register (NECO). Na samarwa mutane indijin foam wanda bansan iya karsuba. Yanzu kuma ina da sabo da samarwa ruwa hanya damina, sannan akwai dalibai mata guda biyu (2) masu sha’awar karatun lafiya.

 

Wanda yanzo na samar musu da forma da kuma da wainiyar karatu saboda iyayensu basu da karfen daukar nauyin karatunsu me katadarwa matasa don sune kashin bayan ko wace al’ummah?

Alhamdullah kamar yanda nafada a baya nayi musu alkawari zan samarwa matasa aikinyi kamar masuyin shaye-shaye muna nan muna duba irin tallafin da za’aiya mai girma gwannan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya kaddamar da wani shiri na gyara ya fara daga kanka nima in sha Allahu nima sha alkawarin gyara zai fara takaina a unguwar Dakata.

 

Ya kake kallon salon mulkin Gwamna Ganduje?

Alhamdulillah katafila sarkin aiki kenan idan zanfa da maka ayyukan mai girma gwamna suna da yaw aka duba yanda ya shinfida mana kwalta da sanya fitilar hanya a mazabata ta dakata.

 

Zuwa bela, mata anbasu jari sunanan suna juya jarinsu sai bun kasa yake bamai zaman banza a mazabar dakata. In kasake dubawa Kadimul Islam da gaske al’umma ne a gabanshi.

Daga karshe wane kira kake da shi ga sauran ‘yan siyasa?

Ina kira gaduk wani mutum dan siyasa ne koba dan siyasa bane don cigaban unguwar mu, akwai makaranta a mazabar dawakin dakata wacce wani aji yakone suna karatu babu silin akasa daliban suke karatu, a dawakin dai akwai asibitin sha katafi muna son gina dukunan haihuwa na zamani da sauransu.

 


Advertisement
Click to comment

labarai