Connect with us

ADABI

Zuwan Bahaushe Afirka Ta Yamma, Rayuwarsa Da Sana’o’insa (III)

Published

on


07030797630 imel: [email protected]

Har ya zuwa wannan wakati na karni na 15 babu wuri ko  kudi na ciniki a wannan zamani sai dai abin da su ka kira ‘ba-ni-in-baka’, wanda Turawa ke ce ma trading by bata. Ma’anar haka shi ne su manoman sai su ba makeran gero da dawa ko masara, da sauransu. Su kuma makeran sai su mayar masu da abubuwan da su ka kera. Mahalba kuma sai su ba makeran dan naman dabbobin da su ka halbo ko wasu abubuwan daban, su kuma su basu kayan halbin da su ka kera.

Ko wannensu a cikin ukun ya dogara akan kowanne kan zaman sana’ar sa. A daidai lokacin kuma wannan wuri ya kara bunkasa, domin ana ma tunanin unguwar Ambuttai aka fara kafawa a cikin birnin Katsina, to daganan sai kananan sansani na kewaye da ita su ka tsira. Mahalba na sare itacen su na mayar da su itacen bindigogi. Makera kuma, wadanda a sa’annan a ka fi kira da ‘yan tama su na saro itace su na konawa, su na kuma amfani da garwashin wajen gasa karafa. Cinikin tama fa ya gawurta.

Duk wani yunkuri na daidaita tarihin Katsina dole sai ya ci karo da ra’ayoyi mabanbanta, na daga bakunan wadanda aka samo labarun. Saidai wasu masana tarihi sun bayyana karara cewa Barth da Palmer ba su bi diddikin abinda aka bayyana masu ba, kuma shi kan shi Palmer, ya yada mafi yawancin wasu ra’ayoyi da suka ci karo da juna, ma’ana bai yarda da su ba. Bayan nan, tarihin Katsina ya zama maras yawa saboda masu bincike na farko-farko ba su yawaita binciken akan  dabi’o’i da ciniki da kasuwanci da zamantakewar jama’a da har su ka sanya daular ta ci gaba ba, sai dai sun rinjaye akan neman tarihn sarakuna kurum. An riga an tabbatar da hakan.

Wani binciken ya nuna cewa muhimmin tarihin da za a samu a Katsina ya fara daga mulkin sarki Korau, kuma ana tunanin a hakikance ana iya cewa ya yi mulki a tsakiyar Karni na 15. Abubuwan tarihin sarki Korau su ne wata wuka ko takobi mai suna ‘gajere’ wadda da ita ne Korau din ya yanka Sanau da kuma tukunyar karfe. Haka ma an ce Korau ya na da wani takobi mai suna ‘bebe’ wanda aka kwace daga hannun Sarkin Gobir Yakubu cikin 1795 lokacin yakin su da Katsinawa. Hatta gidan sarkin Katsina sunan da aka rada masa shi ne: ‘gidan Korau’. Sai kuma aka bullo da wata sara idan an nada Sarki a Katsinar, sai a ce ‘shiga gidan Korau’ Wani kirarin da ke yi wa kowanne sarki na Katsina tun daga wancan lokaci zuwa yau shi ne da ake cewa:

Korau Rakasa!

Korau dan Korau!

Korau jikan Korau!

Korau magajin Korau!

Rakasa magajin Rakasa!

Korau abu gungurun!

Korau mai tukunyar karfe!

Korau mayen Samri!

Yanka mashidi bakon Sanau!

 

A wasu littattafai an bayyana cewa Korau shi ya fara musuluntar da mutanen Katsina. A wasu kuma an bayyana cewa a lokacin mulkin sa ne aka fara bayyanar da musulunci.

A farkon Karni na 15 jama’a sun fara yaduwa gari ya kafu har ma ya fara bunkasa. Daga cikin wadannan wurare akwai Durbi-ta-kusheyi ita kanta, da ‘Yandaka da Birnin Samru da kuma Karofi.  Sauran wuraren da fatake ke tsayawa su yada zango da ‘yan mazaunun jama’a da ke gab da birnin Katsina kuma sai cikin lokaci kankani su ka hade da Katsinar. Akwai ma wasu wuraren da a yanzu babu su da ke daga gabashin Katsinar, kamar su Dutsin Bamle da birnin Mamman. Tun a daidai lokutan kuma aka fara nada masu unguwanni ko masu gari da ke kula da sha’anonin mulki. Akwai kuma masu kula da wuraren bauta, kamar inda ake bautar iskoki da sauran su, kamar su Badawa da Ambuttai.

Kafin zuwan zamanin sarki Korau akwai kuma masu kula da sha’anin karofi ko wuraren rini. Akwai kuma magajiyar bori ko mai shugabantar masu bori da masu shugabantar farauta da sarakunan kawunan makeru. To wadannan su ne ke kula da mulkin mutanen da ke wadannan wurare.

A wannan lokaci sana’ar Bahaushe ita ta dada sanyashi ya shahara matuka. Cikin wadannan sana’o’I akwai noma da kiwo da fatauci da kira da jima da saka da rini da dukanci da sassaka da wanzanci da fawa da dori, to sai kuma sana’o’in mata. Wasu sana’o’in mata sun hada da saka da kadi da yin kitso dad a sauransu.

 

Banda masarautar Katsina, masarautun da ke da karfi a wannan lokaci na yankin Bilad as Sudan sun hada da na Kano, Barno, Shongai da Kebbi. Anan, ci gaba na samuwa da sauri na sha’anin sarauta da tattalin arziki. Kai, daga karshen karni na 15 da farkon karni na 16 sarakunan su sun zama masu karfi da iko, su ne: sarkin Kano Muhammadu Rumfa (1463-1499) da Kanta na Kebbi (1513) da Mai Ali Ghazi na Borno (1470-1503) da kuma Askiya Muhammadu Toure na Shongai (1493-1528) Babban batun da ya fi daukar hankalin masu sarauta da talakawa a lokacin shi ne zancen addinin islama da kuma bautar iskoki da gumakka.

Ana cikin wannan yanayi sai ga wani babban malami da ake kyautata zaton ma waliyyi ne, ana ce da shi Sheikh Abu Abdallah Muhammad bin Abd al-Karim bin Muhammad al-Maghil wanda ya iso cikin birnin Katsina a shekara ta 1490 wanda kai tsaye da ya zo wa’azi ya yi ta yi, na zuwa ga addinin Allah (SWA) Wasikar da ya rubuta ma Sarkin Kano Muhammadu Rumfa (1463-1499) mai taken Taj al-din fima yajib ala-l muluk  ita ya aiko ma Sarkin Katsina, na ya na ba shi shawara ya sa ido sosai akan masu gudanar da mulkin sa ko masu gari, ya tabbatas da gaskiya ya kuma tabbatas komi an yi shi akan yanda addinin islama ya shimfida. A cikin takardar, ya ce a tilasta ma kowa ya rungumi addinin musulunci.  Ya kuma tsara ma gwamnatin sarki yanda za a amshi zakka da yanda za a bada ta ga mabukata. Shi kuma ya tsara masu yanda za su gudanar da mulki kamar yanda ya zo a Alkur’ani mai tsarki da Hadisin Manzon Allah (SAW)


Advertisement
Click to comment

labarai