Connect with us

RA'AYINMU

Muna Maraba Da Tsaftace Sashen Shari’a

Published

on


Bangaren Shari’a na daya daga cikin muhimman gabobi na matakin shugabancin al’umma a duk inda suke kuma a ko wane irin tsari suke bi. Saboda muhimmancin bangaren shari’a, shi ne aka damka wa wuka da nama na hukunta duk wani mahaluki da aka samu ya aikata laifi, ko da kuwa shugaba ne da kansa. Ke nan, muhimmancin bangaren ba zai misaltu ba.

Tun lokacin da Shugaba Buhari ya hau karagar mulki, ya sha nanata cewa babbar matsalarsa a yakin da yake so ya yi da cinhanci da rashawa ba ta wuce bangaren shari’a ba. Dalili, saboda shi kansa ya sha wuya a hannun bangaren shari’ar Nijeriya bisa yadda ya yi ta zuwa kotu sau shurin masaki kan magudin zabukan da ya shiga a baya kuma babu biyan bukata.

Shugaban kasan ya sha alwashin daidaita bangaren shari’ar Nijeriya, inda a matakin farko jami’an ‘yansandan ciki suka fafari gidajen wasu alkalai da aka zarga da cinhanci da rashawa. Koda yake, Majalisar Kula da Harkokin Sashen Shari’a ta Kasa ta nuna rashin dacewar hakan tare da bayyana cewa ita ce take da alhakin bin kadin duk wani abu da ya shafi sashen na shari’a. Shugaba Buhari sai ya mayar da lamarin binciken abubuwan kunyar da ake zargin alkalan da tafkawa kuma ta yi bincike ta mika masa, inda a karshen makon da ya gabata ya zartar da hukunci bisa shawarar majalisar.

Don haka, ritayar dole da aka yi wa Maishari’a Adeniyi Ademola da kuma korar Maishari’a O.O Tokode daga aikin alkalanci, wani kwakkwaran mataki ne da Shugaba Buhari ya dauka na cimma kyakkyawan kudirinsa na tsaftace sashen shari’ar kasar nan.

Ba shi ne shugaba na farko a kasar nan da ya yi yunkurin gyara bangaren na shari’a ba musamman kan abin da ya shafi yin shari’a ta gaskiya da adalci ga wadanda ake kamawa da hannu dumu-dumu wajen aikata miyagun laifuka. Amma kuma shi ne ya karya lagon barnar da galibin ‘yan kasa ke zargin ana tafkawa a sashen inda ya sa wadanda suka kawo iya-wuya kan lamarin suka yi ajiyar zuci.

Jaridarmu ta sha ba da rahotanni kan yadda ake haddasa tafiyar hawainiya wajen yanke hukuncin masu laifi a sakamakon nagoron da ake baiwa ma’aikatan shari’a da lauyoyi don su kawo tsaiko a kan shari’a, musamman kan abin da ya shafi yaki da cin hancin da ake yi a kasar.

Kafin wannan lokacin, Nijeriya ta yi fama da borin kunya kan yadda kiri-kiri gafiyoyin da suka amsa laifukansu na sata suke tsira daga shari’ar da ake musu kuma su cigaba da wadaka da abin da suka sata.  A lokuta daban-daban, an rika wasa da hankali a shari’o’i har a kai ga kwashe tsawon shekaru masu yawa ba tare da an yanke hukunci ba, domin kyale masu aikata miyagun laifuka su cigaba da rawar gaban-hantsi, inda hakan ya sa wasu suka rika kwadayin bin sawu domin sun ga abin da riba. Yanayin da Shugaba Buhari yake kokawa da shi da ke kawo masa tarnaki a yakin da yake yi da cin hanci da rashawa, ba karamin koma-baya yake haddasawa ba a kokarin rage ko kawar da kumbiya-kumbiya da magudin zabe. Abin da shugaban ya tasa a gaba shi ne gyara bangaren shari’a wanda ya lashi takobin dawo da shi kan turba mafi dacewa.

Tabbas mun gamsu da damuwar da shugaban kasan yake nunawa musamman kan ra’ayinsa na cewa sashen shari’a ya kamata ya shiga gaba wajen yaki da cin hanci da rashawa ta hanyar yanke hukunci na gaskiya da adalci. Domin samun nasarar wannan, ya zama wajibi jagororin bangaren su nuna cewa da gaske suke yi.

Har ila yau, mun amince da furucin da ya yi na cewa yana da matukar muhimmanci, bangaren shari’a a matsayinsa na babban ginshikin gyara al’umma ya rika tabbatar da cewa ana yanke hukunci a kan manyan laifuka cikin hanzari saboda kwallafa rai kan haka da jama’a ke yi. Kuma ga shi mutane da dama suna ganin a maimakon bangaren ya zama wurin kare hakkin talaka; sai ya zama wurin murkushe shi. Wadannan matsalolin ana fama da su ne duk da kasancewar ana aiki da Dokar Hukunta Masu Aikata Miyagun Laifuka ta 2015.

Domin tunkarar irin kallon da ake ma sa, sashen shari’ar ya fara daukar matakan tsaftace kansa. Inda ya yi wa wasu ma’aikatansa ritayar dole, wasu kuma ya kore su daga aiki. Aikin cire baragurbin sashen na cigaba da gudana kuma muna yaba wa shugabannin sashen saboda kwarin gwiwar da suka nuna na daukan kwararan matakin na gyara. A kan wannan ne ma muke jinjina wa Majalisar Kula da Harkokin Shari’a ta Kasa (NJC), saboda kyakkyawar shawarar da ta bayar ta hukunta Maishari’a Ademola da Maishari’a Tokode.

Daukar matakin ya tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro. Kasancewar akwai Alkalan da suke wasa da aikinsu tare da daukar kotu a matsayin mai shiga tsakani kawai, maimakon yanke hukunci bisa gaskiya da adalci. Sau tari, akan bar shari’a a hannun masu gabatar da kara da lauyoyi su rika fafatawa a tsakaninsu shi kuma Alkali ya zama dan kallo kurum. Hakan ya sa idan masu gabatar da kara da masu kare wanda ake kara suka hada baki a junansu, sai a raina wa kotu hankali. Masu gabatar da kara su gaza fito da shaidar aikata laifi baro-baro, lauyoyin da ke kare wanda ake kara kuma su yi ta mayar da hannun agogo baya.

Muna fata, daga wannan gyarar da ake yi, dukkan masu hannu a sha’anin shari’a na kasar nan za su hada karfi da karfe domin tabbatar da sashen na shari’a ya dawo kan turbar asali da aka san shi a kai na baiwa mai laifi lafinsa, mai gaskiya kuma a ba shi gaskiyarsa. Sannan ya kamata Kungiyar Lauyoyi ta Kasa (NBA) ta daidaita sahun ‘ya’yanta da suke karkacewa, wadanda suka kware tare da gogewa wajen mayar da fari ya zama baki, baki kuma ya zama fari saboda kudi.

Tabbas, idan aka samu sashen shari’a ya yi ado da gaskiya da rikon amana, sauran sassan gwamnati ma ba za a bar su a baya ba, kasancewar sashen a matsayin uwa-ma-ba-da-mama.

 


Advertisement
Click to comment

labarai