Connect with us

TATTAUNAWA

Usman Baba: Matashin Da Ya Kafa Makaranta Dan Bada Ilimin Boko Da Sana’a

Published

on


MALAM USMAN ADAMU BABA, matashi ne da ya kafa  makarantar Al-IMAN Academy International School da ke maitunbi, Minna. A hirarsa da wakilinmu MUHAMMAD AWWAL UMAR ya tabo dalilinsa na kafa makaranta mai zaman kanta na zamani inda ake bangaren boko da Islamiyya, ya kuma bayyana irin illar da barace-barace ya yi wa yankin Arewacin kasar nan. Ga dai hirar kamar haka.

Da farko mai karatu zai so sanin da wa muke tattaunawa.

Suna na Usman Adamu Baba, wanda ya kafa wannan makarantar ta Al-Iman Academy a nan unguwar maitunbi kimanin shekaru takwas ke nan.

Tunda farko mai ya dauki hankalin ka, ka kafa wannan makarantar.

Da farko dai ban yi karatun boko sosai ba, amma kasancewar na yi karatun addini kuma na ga yadda a Arewa mafi yawan Iyaye suna daukar tura yara makarantar allo dan yin bara kamar wani ginshiki ne na addini musulunci kuma duk da cewar ba haka abin yake ba. Sai na ga idan na kafa Islamiyya tsintsa kamar da sauran rina a kaba, na yi tunanin bincike kan tsarin karantarwa da gwamnati ta amince da shi sai na bude wannan makaranta mai kunshe da bangarori uku, bangaren boko da na addini da kuma sana’a.  Manufar duk yaron da ya kammala wannan makaranta zai samu ilimin boko da na addini kuma zai zama yana da sana’ar hannu wanda zai iya dogara da kafafunsa.

Idan ka dubi tsarin mu, daidai ya ke da na kowace makarantar gwamnati da masu zaman kansu, kokarin da muke yi a nan shi ne yadda zamu kaucewa halin ‘yan Arewa da shi na barace-barace, roko da yawon maula, muna kokarin  ganin  yara kanana masu tasowa a yankin nan na mu sun tsira da wannan.

Ba ka ganin wasu Iyayen zasu raina irin sana’o’in da ku ke koyarwa a nan?

Idan ka ce hakan, yanzu ka shiga rariya ba za ka iya kirga yaran da suka kammala karatun sakandare kuma suna zaune ba aikin yi ba, mu fa tsuntsu biyu muka jefa da dutse daya. Bayan mun hana rigimar yara a cikin unguwanni bayan sun dawo daga makaranta wanda rashin aikin na daga cikin abubuwan da ke jefa da daman matasa a harkar shaye-shaye, daba da fadace-fadace a cikin unguwanni, sai ya zama na muna tarniyatar da su akan sana’a.

Amma kamar wannan tsarin ai ba zai yi nasara ba tunda bisa al’ada ba mu saba da hakan ba, duba da yanayin da yankin na mu ya ke.

Haka ne, kuma wannan shi ya janyo ‘yan uwanmu mutanen kudu a kullun suke kallonmu kamar wadanda ba su san ciwon kansu ba, jahilci da rashin aiki ya samu gindin zama a tsakankanin mu wanda komai muna jiran gwamnati ne tayi mana. Da za ka kwatanta mu da kudu din sun yi mana zarra ai a bangaren ilimi ka gane, yadda iyaye marasa karfi kan jajirce dan ganin yara sun samu ilimin boko da na addinin da suka zabarwa kansu mu a nan abin ba haka yake ba sai kalilan, domin shi bokon ba a karfafa shi ba yadda ya kamata tunda ba a iya mayar da hankali kan daukar dawainiyar yaron yadda ya kamata balle na addini, sai ka ga shekarun da ya kamata a ce yaro ya himmantu wajen rike kanshi da taimakawa mahaifansa, sai ka tarar a lokacin ma  bai san ciwon kansa ba balle ma ya iya tunanin samarwa kansa yanayin da zai iya rike kanshi har ya taimakawa iyaye, domin bai samu wadataccen ilimi ba balle ya samarwa kansa abin a karshe sai ka tsince shi a shaye-shaye ko yawon bara kuma ma ya jefa kanshi muguyan hanya da ba za ta bulle ba.

Amma ai hakan bai isa ya zama hujja ba ko?

Saboda me, ka dubi yanayin da muke ciki yau, ilimi shi ke yin jagora ga rayuwar kowa, sana’a itace ke haskawa mutum hanya. Yanzu ka dauki yaro ka kai marantar allo da sunan ya yi bara dan samun abin da zai ci kuma ya taimakawa malaminsa, shin wannan hakkinsa ne ko na iyayen. Sannan ka duba irin yaran da ake kaiwa yawon bara shin wannan ya da ce, zamani yazo a duk inda ka ke za ka iya yin karatu domin ba inda ilimin nan bai je ba, saboda haka ka ga ke nan mu a bangaren mu mun samar da yanayin da zai iya kawo sauki wajen baiwa yara masu tasowa ilimin addini da na zamani kuma muka dada da sunan Ma’aiki wato sana’a.

Ganin cewar kai mai karamin karfi ne, wace hanya ka ke bi dan ganin samu nasarar wannan sauyin da ka ke kokarin haskawa a cikin al’umma.

Gaskiya ne, musamman idan ka dubi irin matsalolin da muke fuskanta, duk da haka ba mu karaya ba, domin wani lokaci har kaddarorin mu muke salwantarwa dan makarantar ta tsaya da kafafunta. Akwai kalubale kam, musamman na biyan kudin makaranta idan lokaci yayi wanda wannan al’ada ce ga duk masu tafiyar da karatu. Saboda haka mun jajirce mun tsaya tsayin daka dan ganin makarantar ta cigaba, idan ka kwatanta da shekarun baya kasan ana samun cigaba a hankali.

Sannan duba da halin da ake ciki yau a yankin nan na mu, sai muka tsara yara zasu zo makaranta daga karfe bakwai na safe zuwa biyar da rabi na yamma, idan sun karatun boko sun tashi sai su fara na addini domin duk littafan da ka san ana koyar da yara a makarantun Islamiyya muna koyar da su a nan, haka sana’a yanzu muna sana’o’in hannu mabanbanta kamar yadda na fada ma a baya a kallan guda takwas cikin ashirin da hudu da ma’aikatar ilimi ta amince a koyar da yara muna yin su a nan. Amma sau da dama mutane na ganin kamar ana tara abubuwa da yawa ga yara, mu kuma muna ganin yadda muke tafiyar alheri ne ga rayuwar yara kuma natsuwa ne a wajen iyaye.

Yanzu ka ga a wannan shekaran a bangaren tilawar Al-Kur’ani mai girma yara ashirin da biyar ne suka sauke Al-Kur’ani. Sannan ka sani wannan makarantar fa ba ta kwana ba ce amma dai muna iyakar kokarin mu.

Akwai wasu makarantu da suke samun tallafi daga waje, shin ko kuna daga cikinsu?

Maganar gaskiya tunda muka kafa wannan makaranta, ba mu taba samun tallafi a bangaren gwamnati ko wata hukuma ko kungiya ba, duk da cewar sana’o’in da muke koyar da yara sana’o’I da ke kayan aiki na sosan-sosai. Kuma ka ga yanzu haka muna da bukatar karin ajujuwa saboda yawan dalibai, amma dai dan abin da muke samu a matsayin kudin makaranta duk da cewar wani zagon ma abin kan rike sosai haka muke ta mulmulawa, da kan zamu samu tallafi lallai da abin ya bunkasa sosai.

Ganin kai matashi ne, wani kira za ka yiwa ‘yan uwan ka matasa musamman magidanta akan kula da hakkin ‘yayansu?

Da farko bari in fara da marasa iyalin, da su sani rayuwa fa ba ta cigaba idan babu ilimi, banga da shaye-shayen da suka samu kan su akai jahilci ya jefa da damansu wanda rashin aiki ya assasashi. Ya kamata matashi koda bai samu damar karatu ba, ya zama yana da tunanin kirkirowa kan shi yadda zai inganta rayuwarsa ta hanyar da ta da ce.

Magidanta kuwa su sani wani nauyi ne Allah Ya dora akansu na kula da tarbiyar iyalansu, ya zama dole a matsayin ka na uba ka baiwa danka ilimi, ka koyar da shi sana’a, domin in ya samu wannan harsashen ne zama tubalin ginin rayuwarsa. Akwai kididdiga da muka yi a baya kusan mafi yawan dalibai masu karancin karatu sai ka ga daga kudancin kasar nan suke, misali akwai wata yarinya da ta kammala jami’ar Uyo ‘yar shekara ashirin da daya kuma ita ce ta zama zakaran gwajin dafi a lokacin, bincike ya nuna mana ta shiga jami’a tana da shekara sha biyar, wanda a daidai lokacin idan ka kwatanta da mu nan sai ka ga mai wannan shekarun bai wuce aji uku na kwaleji wanda wannan kuskure ne a gare mu.

Abin da ni ke son in ce ya zama wajibi matashi ya tsaya da kafarsa sosai kafin yai aure dan samun damar kulawa da nauyin da ke wuyansa, domin da daman matasan mu sun dauka yin aure a haihu shi ke nan, wanda wannan kuskure ne babba, ya zama wajibi idan an yi auren nan a san dokokin da kunshe a ciki, idan an haihu a san hakkin da ya rataya akan iyaye

Akwai bukatar mu matasa mu kara zage dantse sosai ta hanyar aza tubalin ginin rayuwarmu yadda ya da ce, mu tabbatar ba wai tara iyalin ba, mu san hakkin da ke kan mu na iyalin kuma mu kiyaye shi.

 


Advertisement
Click to comment

labarai